Sashe 48
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Koda Halifa ya shigo gida Asiya bata gane kansa ba,yana cikin bacin rai sosai, suna falo da Hajjo ya wuce daki, ta aje dan ta bishi da sauri ya jingina da sif ya dafe fuskar shi da tafin hannun sa. Taje ta shige jikin sa ta rungume tana fadin Allahumma ajirni fiimusibati. Yaya me ya faru,dan Allah kar ka daga hankalin ka, zo mu zauna ka fada min ko da banyi maka maganin abin ba za muyi shawara kaji Yayana. Kamar rakumi ya bita domin ta yi maganar cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Suka zauna bakin gado, Ya kalleta Asiya duk abinan da ke faruwa ya tabbata Anty ce ke hada shi, me na yi mata haka da take shirya min makirci kala kala, in kece matsalar ta ta fito fili tace min bata sonki, shike nan ni ina son ki sai kawai in muku tsakani ta yadda ko ganin ki bazata yi ba,ba sai ta yi ta wannan wasan kwaikwayon ba,harda yunkurin kashe ki, wai ma me kika yi mata?Hawaye suka soma zubo masa. Asiya ta saka hannu tana share masa hawaye, Haba Yayana bana son kana hawaye zuciyata zafi take yi, karka damu jarrabawa ce komai zai warware kamar ba a yi ba.
Zata gane kuskuren ta kuma ni na yafe mata saboda kai. Yace "Ni bazan yafe ba, zan bi miki dukan wani hakki na ki har sai ta yarda ta cutar da ke. Asiya ta tashi ta je ta bude karamin firjin da ke dakin ta ta dakko ruwa ta tsiyaya a kofi ta bashi ka sha. Ya karba ya shanye sannan ya bata labarin dukkan abinda ya faru. Asiya ta cika da mamaki amma sai ta boye mamakinta da damuwar dan kada ya kara shiga damuwa. Ta samu ta kwantar masa da hankali.
Ya fada mata abinda lauya yace.
Tace kar kayi shara'a da ita,ta ci albarkacin zumunci
da kuma 'ya'yanta, ka samu Bros ka fada masa dan kaji ta bakin sa, sannan ka tara duk wata hujjar ka sanan ka tara manyanku dan su san me yafaru, sannan saboda mu warware matsalar mu da Inna ita ma ta zo gurin.
Halifa yace kema kin kawo shawara amma zan duba. Asiya tace saboda ni damuwata yanzu bai wuce Inna ta gano gaskiya ba, sai nafi sakata in walwala.
Halifa yace kar ki damu fa, in yi miki ta wani mawaki da yace ko mutuwa baza ta rabamu ba,in tazo tare zata dauke mu. Asiya ta saka dariya.
Dama kana jin waka? Yace fisha ba.
Sulaiman ya samu Inna da hantsi ta idar da sallar walaha tana zaune tana Jan carbi, bayan sun gaisa yace, Inna dan Allah ki daure ki sanar dani wani abu daya, kila ta haka zamu samu bakin zaren warware matsalar Asiya. Inna Tace "An samu labarin Asiya din ne? A a ba a samu ba, bincike ne dai duk akan abinda ya shafi sakin ta,muna sa ran gano bakin zaren.
Inna tace wannan yaron dan gidan Fatsuma mai dashi ne ya kawo takardar yace wai Inji Halifa.Kuma da na bi bayan shi na na leka na hange shi, yana tafiya, Sulaiman yace Dan gidan Malam Danyaro kenan? Shi kuwa inji Inna Sulaiman yace to ba komai zan samu yaron inji wanda ya bashi sakon takardar saboda gaskiya Inna ba Halifa ba ne. Inna ta ce ni dai Allah ya bayyana min yata,yan zu nasan cikinta ya isa haihuwa, matsawar tana raye, ko akan bola ko wasu su taimaka mata,Allah yasa ta fada hannu na gari, kullum addu'a ta kenan. Hawaye suka zubo mata.
Sulaiman ya bata baki tare da kwantar mata da hankali. Kafin ya fita a gidan.
Anty ta fito zata fita sai ta ga a nata fenti a gefe da Halifa ya tashi, ta tsaya ta cika da mamaki ashe har anzo lokacin da za a dinga yin
abu ba shawarar ta kuma babu sanin ta,to Halifa ne ko kuwa Dady ne wanda aka ba wa gidan?
Ta isa gurin masu aiki,tace kai waye ya saka ku wannan aiki? Babban su yace "Sannu da fitowa Hajiya, Alhaji ne me gidan." Tace Tofa! Lallai kuwa mai gidan. Ta wuce tana danna waya. Ta kira shi ya daga, ko sallama babu tace Wai me kake nufi ne?Dan Halifa ya baka gidan shike nan sai ka dinga yin wasu abubuwa gaba gadi ban isa ka fada min ba ko?
Ya yi yar dariya "Habiba kikan so saka kanki a matsala meye abin daga hankali gyara ne na saka a yi mutane ne za su dawo ciki da zama." Mutane kuma! Ta katse shi wadanne mutane ina fatan dai ba dangin ka zaka rakito min ba? Dan wallahi sai in karbe gidan inga ta fadi. Dady yace kinga ba zancan waya bane inna dawo ma yi.
Anty tana mamakin yadda Dady ke yi mata musu dole sai ta sake bazama akan shi gaba daya asiran da ta yi sun karye a lokaci guda haka.
Dady ya shigo gida cike da kwarin gwaiwar sa, ya samu kuwa shi Anty ke jira har daki ta bishi babu ko sallama bare gaisuwa ta saka shi gaba sai ya fada mata su waye zai saka a gurin. Yace Bintu ce zata dawo gidan nan, tace wace ce Bintu din nan da kake ta magana? Yace Matar Abokina da ya mutu ya bar amanar su a hannu na, kin tsane su saboda su ba masu shi bane ba zaki iya hulda da su ba baki taba zuwa gurin su ba tun mijinta yana raye, da ya mutu da kyar ki ka je gaisuwa, ai bazaki san su ba.
Anty tace OK to menene matsala ta da su? Bayan haka kuma me yasa za su dawo nan bata da dangi ne?" Dady yace tsawon shekarun nan bakwai ni ke biyan haya yanzu kuwa tunda Allah ya sa ina da gida su zo su ci arziki kamar yadda nima arziki ya sa aka bani. Dan haka bai zama dole sai na fada miki ko inyi shawara da ke ba, gargadin da zan yi miki ba ruwanki da Bintu kar ki sake ki ce zaki takura mata domin komai zai iya faruwa.
Anty ta sake fusata, kana nufin zaka kore ni ka zauna da ita,kokuma zaka sake ni ka aureta? Ya ja tsaki ya shige bandaki ya barta tana fadin.
Da kuwa ka ji haushi wallahi , wannan kucakar matar wallahi ko a yar wanke wanke ni bata min ba bare kuma kishiya,ai kana aurarta ni kuma zan san ta kwatanci domin ba hauka ake yi ba. Wani takaici ya kara turnike Anty da ta danganta ta da kishiya, tace kai wallahi ma baka isa ta tare a gidan nan ba, tunda ba gidan ubanta bane. Daga bandaki Dady cikin takaici yace ke ai gidan naki Uban ne.
Anty ta shiga salati tana ihu tana fadin yau ni ka zaga saboda wata shegiya har zaka zagi ubana, kai kan ka yau sai ka bar gidan nan ba ma wai ka shigo min da wata ba. Ke naki uban hoto ne ko kalanda ce da baza a zage shi ba, Ina zaton uba baifi uba ba. Ta fito a dakin ta tsaya tsakiyar falo ta na fadin Hafsa zo ku ji min Babanku wai yau ni yake zagi. Hafsy Ta fito da sauran yara, suka yi cirko cirko.
Zagi kuma Anty kamar Yaya? Anty ta fashe da kuka tana fadin zagi dai da ki ka sani wai Ubana, akan wata banzar mata da ya ke ikirarin zai taimaka mata ta dawo gidan nan da zama. Kuma dai na yi rantsuwa saidai ya zaba ko dai ni ko ita.
Hafsi tace Anty dan Allah ki daina cewa ko ke ko ita, akwai wadda ta isa ta shigo gidan nan ba ke kika kawo ta ba, kije kawai ki kwanta shima Dady ya fada ne kawai dan ya daga miki hankali a banz...... Saukar wani wawa mari Hafsi ta ji a kuncinta. Kafin ta fahimci ko waye ya sake sauke mata a daya gefen. Dady yace "Yanzun rashin kunyar ki har ta kai ki kutso kai cikin magana ta da mahaifiyar ki kuma har kina nema ki zage ni?"
Dukan su suka cika da mamaki suka juya suna kallon Dady kamar wani TV. Hafsi ta fashe da kuka tana kallon Anty dan neman ta yi wani abu. Dady ya sake nufarta yana fadin bari in zane miki jikin ki in ya so sai kiyi kukan mai dalili. Ta fada dakin su ta kullo kofa tana ta rusa kuka. Anty tace Lallai abin naka da gaske ka ke yi to kuwa ba zai yiwu ba ko asiri aka yi maka sai na karya shi.
Ta nufi wayarta ta dauka ta shiga neman number Adamu Ya daga yana gidan amarya lokacin ya shiga wanka. Amarya ta daga wayar Anty cike da bacin rai tace Ina mai wayar bashi maza . Amarya tace ya shiga wanka.
To yana fitowa ki ce ina neman sa maza yanzu yanzu a gida Amarya tace haba Anty yanzu fa ya dawo kwana biyu ba ya gari, gaskiya sai da safe zai zo koma meye abarwa safiya. Anty ta kara zuwa iya wuya, tace "Ke zan dura miki ashar ina wasa da ke ne dan uwarki,Ina kiran dana ki na fada min cewa sai gobe zai amsa kiran!!" Sa ar uwarki ce ni?" Katse wayar ta yi sannan ta goge kiran ta kuma kulle layin Anty data Hafsi ko sun kira zasuji yana amfani da wayar. Dan haka babu abinda ya fahimta da ya fito, sai ma ciwon cikin da ta hau murkusu, tun yana mata sannu abin babu sauki har dai ya ce ta tashi suje Asibiti. Ta yi ne shima dan su fice ta san Anty zata iya zuwa gidan.
Ta kira Halifa ya dauka, tana kuka take fada masa cewa Dady ya na wulakan ta ta akan wannan gidan daya bashi dan haka ita tana neman su yanzu. Halifa wanda ke cike da jin haushin ta yace gaskiya ba zai iya zuwa yanzu ba sai da safe, tace Halifa ni ke kiran ka kana fada min sai da safe? Yace "To Anty kin san uzrina ne? Jiki ba kwari tace a a, yace" To a barwa safiyar.