Sashe 24
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Asiya wadda suke ta lallashinta akan ta tsaya za ayi mata magani sai kuka take ta na fadin Lahaula wa la kuwwata illa billah!!. La ila hailla anta subahanaka inni kuntu minazzalumin!!!
Malam ya mike da nufin zuba mata ruwan da kayan jikinta tunda taki yarda ta cire kayan gashi tana ta kiran Allah. Yana daukar kwaryar sai kamar an ta kade shi can gefe. Ruwan maganin ya zube kwaryar ta tarwatse.
Ya zaro ido ya kalli gurin sannan ya kalli Hajiya, wannan yarinyar tana da gaddama gashi ta korar mana Aljanin da zai yi mata wankan. Anty tace tace Na shiga uku da matsiya ciyar nan, yanzu ba wani abu da za ayi Kenan? Bai tanka ba ya nufi hanyar fita a falon Anty ta bi bayan shi tana fadin Allah ya huci zuciyar ka. Ta bude masa kofa daidai lokacin da Sadiya take sake bugawa. Anty ta dube ta tana tambayar lafiya? Sadiya tana kokarin danna kai cikin falon tana cewa ina Asiya ga wayar ta Halifa yana ta kira.
Anty ta amshi wayar ta ce kije zata zo. Ta ci gaba da bin Malam tana magana kasa kasa. Bai tanka ta ba sai da ya shiga mota ya zauna sannan ya dube ta, baki shirya ba kika kirani, tun a wancan lokacin na sanar dake ki jata a jiki amma kin ƙi, kin gama tsorata ta yaushe zata yarda. Yanzu kam bansan abin yi ba. Ya rufe gilashin motar suka fice. Sadiya ta koma da sauri ta shiga falon Anty ta samu Asiya tana ta shirbar kuka. Ta kamota cike da fargaba tana tambayar "Me suka miki?" Asiya ta mike suka fito Anty ta kalle su ta ja tsaki tace "Ke menene na rungume ta,? wani abun ne ya faru sarakan zuzuta magana. Magani za a bata kuma ta barar, shine harda wani kiran Halifa a waya to me zaku fada masa?
Ta mika musu wayar, ga wayar sai ku sanar dashi abinda kuke son ya sani. Ta wuce kamar ba wata matsala.
Sadiya ta amsa suna isa daki Halifa yana kira. Asiya. Ta daga yace Baby Wai me yake faruwa ne? Ta sai saita muryar ta ce ba Anty ta fada maka ba? Ta fadi hakan ne domin bata san me Anty tace masa ba. Yace "Ta fada min amma me yasa zakiyi haka? Ko ba kya son maganin tunda ta nuna kulawa ta karbo miki ai sai ki amsa ko da bazaki sha ba akalla dai zataji dadi. Asiya ta sauke ajiyar zuciya tace zan kiyaye gaba ka bata hakuri ban yi dan taji haushi ba, data bar gurin ne mai maganin yaga bata nan sai yace wai in cire kayan jikina ya yi min wankan magani zai cire min dattin jikina. Ita kuma Anty ta ki tsayawa in mata bayani..... What!! Ya katse ta kamar yaya ki cire ya miki wanka? Anty kuma ta kawo shi gidan? Ni tace min ruwa tofi ne ta sa aka amso miki saboda kariya shine kika zubar a gaban ta kuma kina ta kuka wai zata yi tsafi dake. Haka ne? Asiya ta danyi dim Anty bata jin tsoron Allah bare ranar mutuwarta. Amma nasan ya zan mata. Yace ki bani amsa mana. " Tace haka ne amma ni nayi kuka ne kuma na zubar da maganin ne da nazo fita. Dan yace in cire kayana ya min wanka. Anty ina son in fada mata bata saurari magana ta ba, shine yace mata wai nace za suyi tsafi da ni.
Sannan kuma dan Allah ka fada wa Anty lafiya ta kalau masu maganin nan yan iskane, inhar ba za a barni da maganar magani ba ni zan bi Maman Annur mu koma gida ni Ina jin tsoro. Ta fashe da kuka. Halifa ya yi shiru ya rasa wane tunani ma zai yi.
Amma shi kanshi yasan gaskiyar magana bai kamata Anty ta matsawa yarinyar nan tace wai lallai tana da aljanu sai ta nema mata magani ba, Sannan baya son ya yi abinda Asiya zata raina Anty yana ganin mafi dacewa kawai ya tare a gidan shi abin ya isa haka.
Cikin sarkewar murya yace Baby ki yi hakuri idan Na dawo zan yi abinda ya dace.
. Da gaske Asiya har ya dawo a tsorace take, dan haka yace ta shirya sukai maman Annur gida. Sai da yayi musu tsaraba sa anan ya kai su. Inna tana ta godiya da addu"a maman Annur tace da Asiya ta kula da kanta sosai. Asiya tace to Amma dan Allah karta fadawa Inna.
Sai da suka biya ta wani gurin shakatawa Halifa ya yi musu oder kayan kwalam suka ci suna hira. A ranar ne ya furta cewa Asiya da zu da kika ce zaki koma gida ko wallahi sai naji kamar kin ce Duniya zata tashi, kamar yadda Na sha alwashi zan yi maganin matsalolin ita Anty bata san halin wasu masu magani ba, sam babu Allah a ransu. Hukuncin da na yanke shine kawai zamu koma gidana shike nan komai ya zo karshe. Asiya tace duk yadda ka ce amma ni dai bana son harkar masu maganin nan ne. Yace zamu biya kiga gidan an gama komai gefe na har na saka kaya. Asiya cike da nurna tace suje ta gani.
Gidan ya matukar birge Asiya ya zaga da ita ko ina_ta gani, tace Yaya ni ce a wannan gidan zan zauna kamar gidan Shugaban Kasa? Ya sa dariya suka shiga sasan shi ya kunna wuta haske ya game ko ina. Halifa ya daga ta sama yana juyi a kan kafet din dake tsakiyar falon. Ina son ki Asiya sosai in kika barni wallahi rayuwata zata tsaya cak. Ya zauna tana kan cinyarsa. Tace nima ba zan iya barin ka ba Yayana kai ne Duniyata Aljanna ta. Ni dama tun a ranar farko Na fara son ka.
Zo muje ki ga dakin baccin mu a nan zamu samu babynmu yau din nan ba sai gobe ba. Tace a nan zamu kwana? Yace sosai gidan mu ne gobe zamu je can mu kwaso iya kayan sawa, kafin sati daya zan saka komai na gida. Shike nan mun tare.
Wata irin rayuwa suka yi a daren wadda baza ta kankaru a zuciyar su ba. Sun kwana cike da nishadi da so da kauna. Da safe suka yi wanka sannan suka maida kayan jikin su suka nufi gida.
Anty ta kwana cike da zullumin inda Halifa ya tafi kuma shida matarsa, abu mafi tsoro ya kashe wayoyinsa duk inda tasan zata iya samun labarin sa ta buga amma shiru. Daga karshe ta kira wani malamin ta domin ya yi mata bincike. Jim kaɗan ya kira ya sanar da ita cewa yana raye amma fa yana mugun hannu dan haka ta aiko da dubu dari domin ayi mata wani aiki da zai bayyana da gaggawa asubahin fari. Duk da zuciyar ta tayi farin ciki dajin haka, sai dai dolenta ta danne domin da sauran lokacin, yanzu da Halifa ya mutu ba tare da ya mallaka mata kaf dukiyar shi ba ai aikin banza Kenan. Dan haka ta tura kudin kuma tashiga kiran yan uwa tana sanar da su harma wadanda suke Uba daya. Kafin waye war gari hankula sun tashi domin fa babu wanda ya samu Halifa a waya. Ana idar da sallar asubahi dangin suka soma tururuwa dan zuwa jin ko a samu wani karin bayani game da batan Halifa da matar shi.
Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*
*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[7/7, 22:15] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w
Baffa ya yi sallama da Dady, ya fito, bayan sun gaisa Baffa cike da damuwa, yace wai sai na samu labari wadannan mutanan sun sace Halifa to ta yaya abin ya faru? Dady cike da jimami yace "To ni dai na dawo Antyn ta su take sanar da ni cewa an kama Halifa abinda har yanzu na kasa fahimta shine kiran ta suka yi ko waye sanar da ita oho. Sai kuka ta kwana yi. Baffa yace har wayar matar tasa ba a samu ba kenan? Dady yace " Ita ai ba wanda ya san lambarta ma bare a kira. Baffa ya nisa sannan yace " To Iyayenta sun samu labari kuwa? " Dady yace Gaskiya da kyar ne, domin ba wanda ya tuna da su ma, amma bansani ba. Baffa yace" To ni abin ne na rasa gane kansa, ance ba su kira waya ba, ta yaya aka san cewa an sace shi? Jikina yana bani yaron nan ba haka bane. " Dady yace Allah ya sa, domin ina cike da dimuwa.
A cikin gida kuwa Yayun Halifa wadanda suka kasance kannan Anty Uwa daya Uba daya duk sun hallara a gidan suna ta koke koke a batan Kaninsu da matar sa. Maman Ummita kuwa tana zargin ko dai Anty ce ta salwantar da shi, domin ita ta jima da fita daga halin Anty ta fada wa sauran sunce ba haka ba, sunsan dai Anty ta kanainaye Halifa ko su zai wa alheri dole sai ta sani in ta ga dama ta hana shi, ko kuma ta amsa ta rage ko ta rike ma in taga dama amma basa zaton zata iya salwantar da Halifa akan dukiyarsa, dan haka ita a gurinta Duk inda Halifa yake dole Anty ta sani.