Sashe 56
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
A haka goma ta wuce sha daya ta kawo jiki na dare. Ta ji shigowar motar sa, tana ta shawara akan abinda zata yi masa ko zata ji sanyi Tana ga kamar ta tunkare shi da zancan. Zantukan marubuciyar suka fado mata, anya zata bi wadannan shawarin sun mata tsauri addu'a dai zata ta shi ta yi dan ta san bazata iya bacci ba ma, amma ta kauda kai kar ta nuna ko alamar ta na zargin sa abu ne mawuyaci.
Bata san ya shigo ba, tana kai kawo a falon ɗa na kuka. Sai Murya shi taji yana tambayar me ya same shi? Tare da kai hannu zai dauke shi, ta ja da baya cikin sauri kamar wadda taga abin tsoro fuskatar ta ta yi suntum da kuka, yace "Ya Subahanallah, Kema taya shi kukan kika yi? Ta kau da kai,kowa da nashi dalilin kuka. Yace To kawo shi sai ki fadamin naki ga mai share miki hawaye Allah ya dawo da shi lafiya.faɗa min dalilin domin shi na san nashi, munyi waya da Nurse ta fada min cewa zai yi kuka kuma kar ayi masa wankan yamma, saboda allurar nan,
na yi ta kiran ki in fada miki baki daga ba. Ta kalli wayar dake gefe sanna tace banga kiran ba. Yace ki dai duba kafin ki musa, kawo shi. Ta sake kallon shi cikin ido, ka yi wanka tukunna. Ya matso ya karbe shi ba tare da jira ta miko shi ba. 'Ki huta kema ai kin sha aikin jijjiga ga shi da alamu yau gidan bai samu gyara ba,komai yana nan yadda na barshi.
Dole fa sai an sama miki mai aiki gaskiya zata taimaka miki mussaman irin wannan lokacin kina fama da yaro, ko ba yaro gidan nan Baby ya yi miki girma da aikin gyaranshi kullum. To ka dawo da su Fatin mana tunda dama na ga bakaji dadin tafiyar su ba. Ta fada cikin gatse. Sai lokacin ya fuskanci abinda take nufi. Allah ya baki hakuri, ni shawara nake badawa Gida dai na ki ne Baby ki yi yadda ki ke so dashi su Fati tunda kika sallme su na kara magana? Kuɗin su ma sai daga baya na ba su.. Su Fati kuma ai sun zama tarihi a gidan nan.
Ya nufi daki, turus yayi yana kallon ko ina ba a gyara ba. Ya fito ya same ta zaune ta dora sabon kuka,ya tsaya cike da mamaki da fargaba yana cewa wai me aka yi ne,ki fada min mana?
Ta yi masa banza ga yaro na kuka, ya koma ciki ya kira Nurse ya tambaye ta ko akwai wani abu da aka gani na rashin lafiya game da yaron tace babu, ya fada mata yaron ya yini kuka jikinshi ya dauki zafi. Tace "An kuwa bashi maganin da aka bata na zazzabi? Yace bari ya tambaya, ya fada mata yanzu ya dawo ya samu Uwar da dan suna ta kuka. Tace akan samu haka a haihuwar fari, sukan taya yaran kuka in sun rasa yadda za su rerrashe su. A bashi magani. Ya dawo ya same ta ya zauna kusa da ita, kiyi shiru shike nan ina maganin na shi kin kuwa bashi? Kai ta girgiza alamun a a. Ya bashi maganin ya yi ta jijjiga ta zuba tagumi tana kallon su, gaskiya Halifa namiji ne da kowace mace zata so shi. Ta darsa hakan a ranta. har ya yi bacci. Ya je ya shimfide shi ya yi masa addu'a ya dawo ya zauna ya rungumo ta, Babyna sannu da kokari kiyi hakuri haka iyayen mu suka yi ta fama har muka zama mutane, kwana kadan kema zaki saba da komai, ai kina kokari Allah ya saka miki da Aljana. Asiya ta sauke ajiyar zuciya. To yanzu me ya kamata ta ce masa? Ta dube shi. Kana son ka kara aure ne? Ta jeho masa tambayar. Ya kalle ta. "Me kuma ya kawo wannan tunanin Baby?" Kawai amsa zaka bani. Ta katse shi. "A a " Ya amsa a takaice. Wata ce muka hadu a Asibiti na ganta a tashin hankali sai na tambaye ta ko lafiya, shine ta ke fada min ta ga mijinta a Hotel da wata. Ya dubi Asiya da sauri, "To ita me taje yi Hotel ita ma gurin wani taje kenan? " Asiya Tace ita ta ce min zargi ta yi sai ta ke bibiyar shi.
Halifa yace Ta kuwa sa kanta a wahala, Ai be kamata ta yi haka ba ita ma Addu'a zata yi masa kawai. Asiya ta zuba mishi ido, ya kalle ta, ko a kwai wanda ke shiryawa banda Allah? Tace Babu amma shi ba zai ji kunyar Allah ba, sai yaje yana bin mata kuma bata kasa biya mishi bukatar shi ba. Ya dan yi tsam, kamar tana jefa mishi magnar ne. Amma sai yace Allah ya kyauta ta shi ki gyara mana gurin kwanciya. Ya wuce ciki. Yana bandaki ta shigo. Ta zuba ma wayar shi ido. Ta dauka tana juya ta dan bata san Sabuwar lambar sirrin sa ba.
Sako ya shigo ta sama a whatsapp hotuna ne suka shigo amma ta kasa shiga domin shima whatsapp din a kulle yake. Bata ji fitowar shiba sai dai taji yace Me ki ke nema kuma a wayata? Ta dan firgita ta mika mishi tana fadin sako naji ya shigo kuma sai na yi mamakin ka saka sabon Security a wayar.
Ya fizgi wayar, saboda irin ku ne ake saka Security a waya, na taba daukar wayar ki na duba? Me ki ke son ki gani? Ko nima bincike ne zaki fara min. Lallai zamu samu matsala in har zaki taba min waya.Ya bata rai sosai kar ki sake ko da wasa ki sake daukar min waya da sunan bincike baki da wannan hurumin na faɗa miki, na kula kwanakin nan fitina kawai ki ke so bana son in nuna miki rashin hakuri na, kar kuma ki bari ki kai ni bango.
Ya yi tsammanin ta bashi hakuri,kawai sai yaga ta bata rai ta shiga gyaran gado. Tsaki ya ja ya dauki filo ya fice.
Asiya ta yi shiru tana mamaki, a yi maka laifi kuma a fika fada, daga ganin yadda ya haukace an taba masa waya wallahi bashi da gaskiya ko kadan.Ta fada a fili.
*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[12/17/2025, 19:26] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt
*Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302*
Da safe Halifa bai bi ta kan Asiya ba, ya shiga ya yi wanka ya shirya hatta ɗan sa bai kula ba, ya fice abinsa. Hakan ya daga mata hankali kodai sai ta fito masa a mutum ne ta nuna masa tasan me yake aikatawa a fili sannan zai haɗa hankalin sa, kila jikin sa zai yi sanyi ya shiga faɗin ta yi hakuri. Laifin nan ya bayyana karara koda yake wani nuna mata yaji haushin abinda Anty ta fada duk munafirci ne.