← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 62

Sashe 62

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baban Nihal ne yake fitowa daga cikin gidan ya nufo su cike da fara a Yaba Halifa hannu suka tafa, ya na fadin “Afwan Halifa na ga ka fusata shekaran jiya . Halifa yace dole in fusata ace auren Hafsi sai Ana jibi zanji dan ina fushi da Anty ko menene ai ba a ki sanar min ba. Bros yace. Kasan bikin ne babu shiri kuma ba tabbaci akan za a yi shiga rigingimu, kasan yaron nan ne da ke zuwa gunta tuntuni Dady yace ya fito tunda bata da aiki sai daga wa matarsa da yayanta hankali, yaron yaki zuwa shi kuma Dady ya sakamata ranar aure, aka ce yaron ya zo yaki zuwa. Nan munzo da Maman Nihal kasan na kawo ta gurin Anty dan na gaji da boyeta . shine fa na amshi lambar yaron gurin Hafsi nace ya zo ya ki, na sa aka dakko min shi mukaje Hisba. A can aka nemo iyaye shi suka zo wani abin takaici ashe ko sana a bashi da ita. Da kyar suka hado dubu Hamsin shine kudin aure da sadaki.

Ba lefe bare wani abu na al ada. Gurin zama kuwa gidan iyayensa za su zauna. Asiya da ke gefe wadda ta tabbatar Bros bai kula da ita ba sai da ta ji karshen zancen sannan tace “Ina yini.” Ya kalleta sosai Halifa dama an ganta ne?
Halifa ya amshi Yaron ya mika masa ga Babana. Ya fada yana fara ‘a. Bros ya amshe shi baki bude wai tama haihu duk bamu sani ba haba Halifa ashe dai ni zaka iya boye min wani abu.

Halifa yace Wai da gaske kake yi ban fada maka ba? Ni fa na dauka na fada maka ka tuna Bros ya ja tsaki a ina ka fada min ɗin kawai dai baka kyauta min ba, dan bana boye maka komai ka sani. Ayimin afwa. Dama ba ɓata ta yi ba tana gurina a sabon gida. Bros ya ja tsaki shine dan rashin kirki muka yi ta nemanta har da kai ana saka addu o i, akwai guraren da nasa ayi min sauka Allah ya bayyana ta kusan guri uku batare da ka sani ba.
Halifa cikin dariya yace Gata ai yau Allah ya bayyan ta har da ɗanta.

Bros ya yi dariya yace Allah ya yafe maka.
Suka dunguma cikin gidan falon cike taf da dangi nan suka yo kan Halifa da murna, sai kuma suka lura cewa da Asiya suke tare, dan haka suka cika da mamaki da kuma tambayoyi akan yau she aka ganta. Sai kuma Bros ya ce ai ga dan Halifa nan fa sabon farin ciki ya tashi maman Nihal da bata taba ganin Asiya ba sai ranar taji kawai Asiya ta kwanta mata a rai. Ita kuma Asiya sai raba ido take ko zata hango Anty gaba ɗaya a tsorace ta ke tana yake tana kallon ta ina Anty zata fito.

Hayaniyar ta yi yawa Anty ta tashi daga kwance zata fito. Baba tace Likita ya haramta miki fita cikin hayaniyar nan dan haka ki kwanta.

Anty tace yanzu Zan dawo Ina ga kamar wasu bakin aka yi.

Hajiya Talatu ta shigo suka ci karo tace ga Halifa nan da matarsa kawata har da dan su saurayi da shi.

A tsakiyar kai Anty ta ji maganar dan haka ta fita da sauri dan tabbatar da abinda ta gani. Ta daga yatsanta dan manuni tana nuna Asiya abinda kawai ta iya furtawa kenan? Ta zube a kasa tana wani irirn abu kamar farfadiya. Asiya ta makale a bayan Halifa tana faɗin mu tafi gida. Bai ce mata Kala ba kuma bai je gurin Anty ba wadda dangi suka zagaye ta suna kuka. Bros ya dauki Anty cak sai mota. Suka wuce Asibiti Asiya sai kuka take.

Ta ji tausayin Anty ganin yadda ta rame ta kare duk tsufa ya bayyana a gare ta.

Halifa ya dakawa Asiya tsawa ki rufe min baki dan Allah kina ta kukan nan tun a gidan kin fi kowa tausayi ne ko me? Asiya tace Nice sila data ganni ne ta fadi da lafiyarta kalau. Yace Ke kika ture ta ko kinje kusa da ita. Alhakin kine ya ka mata da kunya. In ta ci Sa a bata mutu ba ta nemi gafarar ki.

Asiya tace Ni fa tuntuni na yafe wa Anty komai ya wuce a gurina. Muje Asibitin. Baza a ba Halifa ya furta a fusace. Tsoro ya darsu a zuciyar Asiya ta yi shiru.

Bayan sun isa gida Halifa ya kasa zaune da tsaye. Can Asiya ta jiyo shi yana tambayar Bros cewa wane Asibitin su ke? Ya dauki mota ya fita.

Ance hannun ka baya rube wa ka yanke ka yar.Domin sai ga Halifa ya tasa Anty yana kuka likita ya tabbatar masu rabin jikinta ya shanye Tana kallonshi tana hawaye wanda bai san ko na menene ba, sai dai yafi kama da hawayen nadama in ya yi la akari da yadda kwayar idon ta take nuna rauni.

Halifa ya shiga dakin Asiya tana zaune ta rasa wane irin tunani ma zata yi game da yadda rayuwarta ke tafiya a harɗe.

Ya zauna kusa da ita, Asiya ta dube shi cike da sa ran zai hantare ta kamar yadda ya saba. Tace ya mai jikin kuwa. Yace ta nakasa Asiya Anty ta koma abin tausayi Ina son in Allah yasa ta fara magana zan kai ki ki yafe mata. Cike da tausayi Asiya tace Insha Allah dama na yafe mata.
Ya kama hannun Asiya Ina son ki yi min wani alkawari mana dan Allah karki kara zargina nima kuma na daina boye miki koma menene tunda abinda ya kawo duk wannan matsalolin kenan har ga Allah na yi haka ne dan bana son ki shiga damuwa Asiya ina son ki fa irin wanda bakya tsammani sannan na tabbatar kina sona .
Kirike a ranki ko wata na aura sai dai don jin dadi da nishadi ko kinyi sakaci da wani gurbi in kawo wata ta cike amma ba dan so ba,shi so guda daya ne tak kuma ke nake yi wa.

Asiya tace Insha Allah tana rungume Halifa ya matse ta gam kamar ya maidata cikin sa dan kauna. Tace ka Sa a ranka in har ni ce zan baka matsala to ka yi bankwana da matala kishinka ne da son ka suka min yawa. Yaya ina alfahari da wani abu wanda ke da wahalar samu a zamanin nan. Kai ka fara sanina a ‘ya mace, ni na fara saninka a ɗa namiji Katuna yadda muka yi ta fama a daren farkon mu? Har yanzu kalamai da sambatun ka suna nan a zuciyata. In furta maka su? Ya dora tafin hannunshi kan lebunan ta.Nima ban manta da sunayen wadanda kika yi ta kira su kawo miki dauki ba. Suka sa dariya tare da rungume juna.

Hafsi ce ke jinyar Anty lokacin da Asiya suka shiga dakin sun dawo daga gashin ƙashi kenan. Dakin cike Bros da matan shi, ga Dady da matar sa Bintu. Gaban Asiya sai faduwa yake kar ganinta ya sake rikita Anty.
Idanu Anty ta zuba kan Asiya tana ta kallonta ba tsammani sai aka ji Anty ta yi wani gwaranci wanda da bata taba magana ba. Gaba daya aka maida hankali gurinta Hafsi tana cewa me kike so Anty?
Ta maimaita sau uku kafin aka gano tana fadin Asiya ki yafe min.

Yadda Anty ke hawayen shine ke bayyana tsantsar nadamar ta Asiya ta kama hannun ta tana fadin Anty nayafe miki komai cikin kuka Asiya sarkin tausayi. Anty tace a bata takarda da biro dan tana son yin magana amma ba a gane me take faɗa sai da kyar.
Da hagu ta rubuta shima da kyar. “Na cutar da Asiya da yawa ni na mata sharrin kwarto. Ni na bata guba ni na yaɗa ta a Duniya.
Halifa ne ya fara Karantawa ya jefar da takadar dar ya kama hannun Anty yace duk ta yafe miki Anty Allah ya baki lafiya.

A mota za su gida Asiya tace shi kuma wannan yaron ko yana Ina yanzu oho. Halifa yace ban jima da sa wa a sake shiba kurkuku muka aje shi tuntuni ai ni na san komai. Asiya tace rayuwar nan abin tsoro ce dubi yadda Anty ta dawo abin tausayi .Halifa yace Hafsi ma rayuwa ta nuna ta tun yanzu aure mara daraja yanzu ma wane aure tunda dole ta yi jinyar Anty. Asiya tace dan Allah ku samo mai jinya ita kuma sai ta tare a gidan ta .

Bayan sallamo Anty aka yi tarewar Hafsi sai dai fa kowa yaƙe ya ke abin gwanin tausayawa Hafsi zama da iyayen miji gida daya daki ciki daya sai maida Kaya aka yi gida.

Saukin ta ma Halifa yace Bros ya samu inda zai saka mijin nata a kwari ya koyi kasuwa to in har ya riƙe amana akwai yiwuwar su duba lamarinsa.

Asiya suna kwance da Halifa da rana tace Yaya ka ya kice wannan soyayyar ta rana tsaka zuwa yanzu dai duk na biyaka bashin da na ci maka ga azumi yana zuwa saura baifi sati daya ba.

Ya ƙara matse ta ai karki damu ibada zamuyi sosai da azumi kamar ba gobe. Ya daga filon da ya tada kai,kin gani dakko passport Kaf azumin mu a Umara zamu yi shi.

Farin ciki Asiya ta dira kasa tana ta rawa ta manta ma tinɓir take Halifa sai dariya yake tana sake birge shi.Ya sauka ya kama ta ya rungume kin sake mai dani ruwa wannan rawar ta birkitani Baby. Asiya tace dole in nuna godiyata a gareka amma Ina zan bar yaro na? Yace dashi zamu tafi.

Bayan fitar Halifa Asiya ta dinga kiran dangi tana sanar da su. Ta fita tsakar gida tana ƙarewa gidan kallo tana godewa Allah da kyautar miji kamar Halifa da ya bata. Zuwa yanzu ta iya da fushin sa kuma tana kauce wa duk abinda zai janyo hakan.

Alhamdulilah ƙarshen littafin HASASHE kenan Allah yasa muyi amfani da darasin dake cikin labarin.
Chapter 62 · 0% Book details