← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 62

Sashe 55

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta saka face marks amma bata kira shiba lokacin da ta samu me dan sahu. Taje Asibitin ta kira Nurse aka yi musu allurar ta tambayi. Nurse ko sunyi waya Nurse ta ce mata a a bai kira ba, har ta tambayi Asiya ko lafiya ta ganta duk a Hargitse Asiya tace ba komai bari ta tafi. Zuciyarta tace kawai ta wuce gurin Inna dan haka ta samu dan sahu dan ya kaita Fage, sai dai suna kaiwa kwari tace da me Adaidaita dan Allah ka kai ni Hotel. Ya juyo ya dube ta da sauri,"Hotel kuma baiwar Allah?" Tace wata kawata zan duba. Yace To wane Hotel din aciki? Asiya ta dan yi shiru ta manta ashe fa Hotel din da yawa. Can tace wanda haka maza ke zuwa da mata ni na manta sunan shi, kai baka san wani Hotel haka ba wanda maza ke kai mata ka kaini in duba ta sai ka maida ni Gandun sarki zan biya ka. Dan sahu ya yi yar dariya wannan kuwa tasan adadin Hotel din garin nan? Sannan ya juya kan Adaidaita ya nufi hanyar Nasarawa yace zan kai ki dai inda mutane suka fi dabdala Tahir ko kuma Ni'i ma sai ki duba.Tace To gaban ta ya kara tsanan ta faduwa, Daidai rawul din gidan Gwamna kawai ta hangi motar Halifa ta daya hannun suna fitowa daga titin da za su hau, da sauri tace wa mai keken Juya ka bi waccan bakar motar ga su can. Ya yi ganganci ya yanke ya fasa shaga titin ya sha rawul suka bisu. Duk da danja ta tsaida su bayan wucewar motar su Halifa shima mai dan sahu ya bisu bai tsaya ba,. Yace mata wannan ai kasuwar Farmcenter ya nufa, tace muje dai. Kafin su same su har sun bar gurin sun dai samu motar, a gurin paking na kasuwar.
Asiya ta kalli lokaci a wayarta, karfe uku tun safe. Ta dubi me a daidaitar tace hanyar Hotel din ne suka fito ko? Yace e nan ne. Tace shike nan kaini Gandun Sarki.

*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[12/11/2025, 08:53] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt

*Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302*

Bintu tana girki a kicin ta ji an banko kofar falo ta fito Hafsi ce ta shigo. Bintu tace Au ke ce ? Hafsi ta amsa cike da rashin kunya wallahi fa sai kin bar gidan nan tunda ba gidanku bane. Bintu tace ki fada wa wanda ya kawo mu mana sai ya zo ya fitar da mu. Ta dungure kan Ahmad tana fadin kai dena kallo na mummunan banza. Bintu tace Ko zaki mutu ki dawo dai kanin ki ne shi ba yadda zaki yi. Fitar min daga nan. "Bazan fita ba. 'Bintu tace OK jira,ta dauki waya karki fita dama ai ba wannan ne zuwanki na farko ko na biyu kina min rashin kunya ba, bari in sanar da Ubanki sai ya taka miki birki.

Har lokacin da Dady ya daga yana jiyo muryar Hafsi tana zazzagawa Bintu rashin kunya. Ta ce Abban Ahmad Yarinyar nan ba yaune na farko ta zo ta ci mutunci na ba, ta dinga dukan yaran nan, in ba dama gara ka sama min wani gurin. Dady yace "Kiyi hakuri Bintu karki da mu kar ki kulata uwarta ke turo ta, zan yi maganin abin idan na dawo. Tace To.a Hands free ne Hafsi ta ji komai.
Dan haka ta saki dariya,wai Abban Ahmad duk mu ba Abban mu bane to sai kun jira daga ke harsu akwai wasu a gaban ku. Ta yi ball da wani filet na tangaran dake kusa da ita ta wuce.

Tana fita Bintu ta maida kofa ta rufe ta lallashi yaranta.

Da dare Dady ya samu Hafsi a dakin Anty dama tun da taji dawowarshi ta shige dakin. Yace ke dama wato zuwa ki ke kina cimin zarafin mata kina dukar min yara ko? To wallahi na gargade ki duk san da kika kara taba min su sai na rama masu, sannan kuma zuwa ranar asabar in saurayin ki bai fito ba ranar Lahadi zan saka ranar auran ki da duk wanda na ga zai rike ki,wanda in iyashege ki ke ji ya fiki, ya fice abinsa.
Anty ta kalleta, Wai bana ce ki daina shiga harkar matar nan ba ne? Kinsan dai Dady tunda ya furta maganar aure kuma ya samu goyon bayan su Halifa ki bishi a hankali. Ni yanzu kinga ina kula shi ne? Hafsi tace Wallahi Anty kamar in kashe matar nan da yaranta na ke ji na tsane su,tsana me tsanani. Ke kuma sai ki zuba musu ido su zauna lafiya a gidan nan? Anty tace 'To fada min yadda zan yi tunda kin ce i na saka musu ido,, fada min. Kina kallon yadda na koma abin Duniya ya ishe ni, ba wanda na isa in fadawa ya ji, shi kanshi Dadynku da yake matukar shakkata yanzu tsoron shi nake yi, tun da abinda na yi ya karye. Hafsi tace to ki sake yi mana Anty ki dawo da izzarki kin fi kwarjini dubi yadda kika koma yanzu ko su Nihal ba tsoron ki suke ji ba. wallahi. Anty ta ja tsaki tare da faɗin Ana baki kina kin karɓa. Ni dai yanzu kinji abinda ya fada ki turo min Hafizun inyi magana da shi wannan kwane kwane da yake yi fa ya isa haka. Hafsi ta dan yi shiru can tace "Anty wai kawun sa dake Abuja ne ya tafi Ummara sai ya dawo tukunna. Anty tace ai ki fada masa kawai ya zo ina son ganin sa. Kema na ga nema ki ke ki sa min ciwon zuciya bayan na hawan jini da suka sa min. Hafsi ta fita tana kunkunai.

Bros ya shigo dakin da sallama ta daga kai ta kalle shi tun ranar da aka yi wannan hatsaniyar rabon shi da gidan. Fuskarshi babu walwala ya gaida Anty ta amsa ita ma fuskar ta a dake, tana ganin bai kyauta mata ba,tunda ya zabi Babanshi. Ta Katse shiru da faɗin "Ai na zaci baza ka kuma zuwa inda nake ba tunda na fadawa ubanka magana bayan ni baku kalli girma zunubin da ya aikata min ba. Bros yace Anty ni ba wannan ya kawo ni ba, na zo ne in fada miki in su Nihal sun taso daga makaranta zan zo da dare zan tafi dasu su koma gida. Ta kankance ido tana kallon shi, me kake nufi gurin wannan shashashar matar ta ka zaka kai su? To ban yarda ba, in har ina raye baza a kai su ba makira ce ba yarinyar arziƙi bace. Bros yace ita ma kuma makira ce, to aike kika zaba min ita saboda kin yarda da ingancinta. Kuma dai zuwa yanzu banace ga laifinta ba. Anty tace "Kara da kiyashi ne daukar marasani na yi. Ya gyara zama, gurin uwarsu ma zan kai su, akwai abinda ban fada miki ba, Ya kalli Anty wadda ta zaro ido tana kallon shi so yake ya maida matar shi ke nan, aiko ba zai yiwu ba. Kinsan na maida mamansu. Ya katse mata tunani." Ka maida wa ka ce?" Wannan mai kashin tsiyar ka maida wadda ka shiga matsala saboda farar kafarta, ai kuwa zaka kuma sakinta domin ba zai yiwu ba. In ko ba haka ba,gara in tsine maka gaba daya.

Bros yace "Anty na maida matata tun a satin da kika sa na sake ta, mun zauna a Hotel kafin na kama haya, yanzu haka ta haihu muna da yaro wanda na yi wa Dady takwara da shi, har ma ya fara tafiya, dan haka babu wata farar kafa da mata ta take da shi, domin duk abinda na samu yanzu ina tare da ita na samu dan haka sai dai ki tsine min din in kina son hakan amma babu hujja, babu kwakwkwaran dalili sannan ina me neman gafarar ki idan abinda na aikata ya bata miki to ki yafe min, zan dawo anjima in dauke su su koma gurin maman su.

Saboda tsanani mamaki Anty bata iya furta ko kalma daya ba, har Bros ya fice,ta yi mutuwar zaune. Wane irin wasan kwaikwayo ne ake yinsa a gidanta haka?

Da farko mijinta ya zo da mace da yara biyu ya yi aure a boye, yanzu kuma Babban danta ya zo wai ya maida matar da ta tsana, kuma har sun haihu, bayan ta bibiya an fada mata cewa matar nan ta yi aure a wani gari. Wai tana ina duk haka ta faru, bacci ko me?
Zufa ta soma karyo mata me yasa abubuwa yanzu suke ta zuwa mata bai bai? Me ta yi ba daidai ba a rayuwar ta. Kuka ta ke son yi amma ta kasa. Tabbas inta mike zata faɗi a zaunen ma jiri take gani dan haka ta jingina bayanta da bango. Ta lumshe ido da kyar ta samu wasu hawaye suka soma ziraro mata ta gefen ido.

*** *** ***

Asiya ta shiga gida cike da bakin ciki, ga dai gida har gida haka kuma ga ababen more rayuwa amma babu farin ciki a cikin shi bare kwanciyar hankali. Asiya ta darsa haka a cikin zuciyar ta lokacin da take bin ko ina na gidan da kallo. Ta zauna a kujera ta sauke danta wanda ke ta kuka saboda allurar da aka yi masa dama an fada mata zai ta rigima. Wai haka rayuwar take ne babu wani sauki a cikinta? Asiya ta tambayi kanta a fili. Ta sa yaron a kafada tana jijjiga shi, tana kai komo a tsakiyar falo gashi tun abin kari bata ci ba komai,yau ko gado bata gyara ba bare kuma gidan, kuma bata jin zata iya yin wani abu. Motar baƙin gilashi gareta hakan ya hana ta ga ko wacece a ciki, bata da tabbacin cewa Fati ce shine ya hana ta dauki mataki akan ta. Cikin yanayin ta yini ba ci ba sha salla kawai ta ke yi sai jijjiga ɗanta da yake ta kuka, sai kuwa kukan ita ma da take sha.
Chapter 55 · 0% Book details