Sashe 46
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kafin kwana hudu Asiya ta yi shar da ita, ta gyagije, abinda ke ta damunta ba taron suna. Halifa yace kar ki damu zamu yi sunan mu kuma idan Allah ya yarda muka warware komai sai mu yi wa jama a na su.
Ana gobe suna Halifa ya kawo wa Asiya kaya akwati uku da ya sa aka dinka mata, sarka takalma mayafai harda kayan ciki dangin pant.
Ya kawo raguna guda biyu da asuba aka rada sunan a masallacin unguwar su.
Sai lokacin makota suka san da mace a gidan har ta haihu, da suka koma gida suka sanar da matan su, kuma sun zo suna, Hajjo da jikarta Fati sune suka yi girki, tunda ba mai yawa bane. Gidan dai gaba daya ko mutum goma ba a kai ba. Halifa ya kira mai hoto inda ya dauke su kala kala shida Asiya da Jariri mai sunan Ubanshi da kakan shi. Hajjo ce ta samo wata 'yarta suka yi aikin raguna. Asiya ta basu da yawa ta ɗibi na cin su sauran ta ce
su sa a cikin mai. Hajjo tana zato aiki ya kawo su Asiya Kano dan haka ba su da kowa.
Tun ranar farko da Fati jikar Hajjo ta dora ido akan Halifa sai ta kasa sukuni bata taba ganin namijin da ya kwanta mata kamar Halifa ba,gashi matashi mai aji ga kudi ga kyan siffa,tana ta mamaki yadda akayi ya auri Asiya wata
lange lange da ita kamar kara, duk da daular da ke
gidan amma gata nan ita ba wata kyakykyawa ba. Ta sha alwashin sai wannan gidan ya zama na ta. Haka take sakawa kullum in tana zagaya gidan ko tana aiki a kicin.
Asiy tana zaune a falo a na ta gwagwagwa da shan nono har yanzu baya iya kamawa saboda irin mara kunyan nono nan gare ta wanda ke tsaye car dole sai dai ayi sama da dan ita kuma hannuwanta gajiya suke sai Hajjo ta tallafe sannan in ya samu ya kama yana fara tsotso gaba daya sai zafi ya isheta. Halifa ya fito yana rike da kugu yana murmushi yana kallon ta, birge shi hakan ke yi, ta dube shi cike da shagwaba ta ce Yaya kawai a dakko mishi wannan abin tsotson ko a hada mishi madara, zafi nake ji. Yace Baby kin fiye raki kema haka kika yi wa Inna. Hajjo ta yi yar dariya tare da fadin a haka zata saba Maman nata ne ba masu sakkowa ba shiyasa dole sai a hankali. Halifa ya matso ya sa yatsa ya lakuci kumatun yaron tare da fadin Babana ayi wa Momy a hankali ka ji ko? Suka sa dariya. Fati dake can gefe tana goge goge ta shagala da kallon Halifa a jikin shi ya ji kamar ana kallon shi ta gefe TV ya kalli gurin ta yi saurin dauke kai tana kara kakkabe gurin. Ya lura da irin kallon da yarinyar take mishi ba tun yau ba.
Yace Baby ni zan fita tace Kadan jira mana Yaya mu raka ka? Yace na yafe baki ne da ni yau yan Niger za su dauki kaya. Su sun fi son su ganni. Asiya tace To Yaya sai mun yi waya Allah ya bada sa a da rabo mai amfani.Yace Ameen ya wuce.
Ji ya yi an ce Sannu Alhaji ya waiwaya ya kalli gurin yarinyar nan ce, tace ina kwana "Lafiya" ya amsa yana mai ci gaba da tafiya.Sai da ya shiga mota sannan ya kallo gurin har yanzu yarinyar tana tsaye a gurin tana kallon motar. Ya dan taba baki ya fice.
Sulaiman ya hadu da Tela bayan ya kwatanta masa inda yake ya bashi dinkuna Tela yace "Ina gwajin kayanta?" Kash Inji Sulaiman bari zan turo maka, na shafa a,yace "To ba matsala. Tela yace bari a kawo maka lemo ka sha tafiya gashi duk da bamu da nisa da titi sai gashi ka wahala." Sulaiman yace ruwa zaka bani, Nifa zuwa na daya nan Unguwar lokacin da wani abokina Mansur kayi nayi.Tela yace Kayi nayi dai wanda na sani dan gidan Dala?Sulaiman yace shi mana wani baki haka. Tela yace shine kuwa ai yana gidan yari ka san kwanaki an kama shi da wata matar aure,shine ina ga dalilin zuwanshi,ance yana gauron dutse.Sulaiman yace Allah ya kyauta Shi kuwa Mansur me ya kai shi irin wannan danye aikin. "Son zuciya mana,da Sana arka da komai kasan pop yake yi ya iya aiki kuma yana samu. Sulaiman yace azal din kenan. Tela ya kawo wa Sulaiman ruwa suka yi sallama bayan ya sha.
*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[11/6, 08:25] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt
Halifa ya yi murna da Sulaiman ya sanar mishi amma duk da haka sai yace ina son ka samo min cikakken sunan da zan same shi idan naje gidan yari. Sulaiman ya sake kiran Tela ya tura masa gwajin dinki da kuma kudin da suka daidaita,sannan yace masa ko yasan cikaken sunan Mansur dan zai kai masa ziyara can gidan yari din. Tela Yace Ai gaskiya kayi nayi kamar sunan mahaifinsa Garba Dala,kasan tsohon dan canji ne.
Sulaiman yace To hakan ma ya yi Insha Allahu zaije.Ya sanar da Halifa, komai.
Fati ta kalli Kakarta suna cikin Keke napep tace, Ni kuwa Hajjo kin kula yarinyar nan da muke yi wa aiki kamar wata wawuya ko? Hajjo tace kamar Yaya me ki ka ga ta yi? Fati ta ce, kawai dai haka nake ganin Hajjo tace ina kula da yadda ki ke kallon mai gidan nan wallahi ba ruwana kar ki ja abinda za a kore mu. Fati ta ce ai ni da zan samu lambar sa..... bari dai zan dauki wayar ta in dauki lambarsa.Hajjo ki yi tunani ace jikar ki ce a cikin wannan gidan da sai dai in ware miki wannan falon da su ke cewa na baki in samo miki masu aiki,ki saka goma ki tsoma biyar.
Hajjo ta saki dariya ki ce sabuwar Duniya,da dai cewa yai yana sonki shine sai in murtsike ido na in goya miki baya, amma yanzu ki ce zaki sa kanki in yaki fa? Fati tace ai nayi mafarki munyi aure da shi.
Hajjo tace "Tabdi to wallahi ki bi a hankali na fada miki.
Asiya ta sha wanka tana sanye cikin dogowar rigar atamfa ta yi kyau sosai tana dauke da ɗanta a kafaɗa. Ta fito Halifa yana zaune yana kallon TV Ta zauna tana fadin har Fati ta zo kenan naji kamshi ya cika gidan. Yau ba tare suke da Hajjo ba ga maigidanta yana jiran wanka Halifa Yace "Ke kam yanzu ai kin iya wankan ko?Tace tun yaushe na sati daya tayi min. Ya kai hannu ya sagalo wuyanta, kyakykyawata wallahi na takura fa, wai dole sai kinyi wata arba'in ne? Dama ance mai mace daya aminin gwawro,tace Kamar yaya? Yayi dariya Yace To nima dai yanzu ai daidai muke da wanda ba shi da ita. Fin sati biyu saidai a bani shayi da lemon tsami. In ta lashe yawu,kin ga da ku biyu ne shike nan.... Asiya ta yi saurin saka hannu ta dafe bakin Halifa cike da shagaba ta ce, Ka ce Allah katuba, dan gaskiya bana son zancan nan ko da wasa, kana son in mutune? To na ji matsalarka zanji da ita insha Allahu. Amma ka yi min alkawarin cewa ka daina tunanin cuso wata tsakaninmu. Ina fa da kishi Yaya akan ka ba zan iya yin kisa ba,amma ni za ka ga na yi fut na mutu.
Kafin ya yi magana sallamar Fati ce dauke da tiren kayan karin kumallo,ta gaishe su sannan ta nufi Dinning ta shirya ta kuma zuwa ta kwaso sauran. Sannan ta dan matso gurin su kamshin humrar da ta shafa ta bude su,tace Anty an gama shirya karin kumallo. Asiya tace Fati wannan turaren na ki yana da kamshi kina sai da humra ne? Tace "A a daga gida na zo da shi." Amma kin iya hadawa ko?" Fati tace " Ban iya ba wallahi." Asiya tace Kina Maidugurin? Fati a ranta tace ai bazan hada miki bane, a fili tace "Kinsan ba kowa ya iya ba. " Asiya tace OK Baba Hajjo fa bata iso ba ne? Fati ta kalli Halifa wanda ke danna waya kamar baya jin su,ta ce "Zata dauraye kayanta ne,shi yasa, amma yanzu zata karaso. Bari in gyara dakin ku kafin ku gama." Asiya tace to. Tana wuce wa Halifa yace gaskiya turaren da kamshi ki tambayi Hajjo din ko za a samu masu saidawa. Asiya ta kafa mai ido tana kallon shi ta kasa magana. Har sai da yace, Aƙwai kuskure a magana ta? Cike da gatse ta ce babu. Tashi muje ka karya. Fati ta na gyaran daki tana ayyana yadda nan da lokaci kalilan zata mallaki wannan kyakykyawan daki da kuma mai dakin. Ta dauki jallabiyar Halifa da ke kan gado ta rungume tana fadin I love you so much. Idan taga abin Asiya sai ta yi tsaki kafin ta gyara. Tana ganin ta fi Asiya wayewa kuma ta girme mata bata zaton zata sha wata wahala gurin karbe mata miji,gashi ita ba ta da kowa bare wata ta bata shawara,ta fada kan gadon tana manne da rigar Halifa a kirji tana ta sumbatar ta.