← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 62

Sashe 49

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anty ta furta cewa lallai ta kare min, me ya rage min na kima yanzu, ta fashe da kukan gaske ba kamar na dazu na wasan kwaikwayo ba.

Washe gari tun safe masu kawo kayan Bintu suka shigo da sabon gado wanda Dady ne ya siya da kujeru sai sauran tarkacen ta na akin da kayan sawa. Yan gidan su sun zo da yake yan gwale ne, suna taya ta gyaran gurin Dady ma yana tsaye a gurin yana sabe da Ahmad a kafadarsa.

Halifa ne ya shigo gidan bayan ya yi fakin din motarsa, suka gaisa da Dady ya tambaye shi ko anyi baki ne a gidan ya ga yaro. Dady yace Bintu ce ta dawo gidan, dama ina son magana da ku na kira Adamu ma yana hanyar zuwa. "Wacece Bintu?" Halifa ya tambaya. Matar marigayi abokina wadda ka ke ba su zakka. Oho to madallah. To bari in shiga ciki, Dady ya ce to.
Jim kadan sai ga Bros shima ya shigo. Ya tambayi Dady su waye ke tarewa a gidan? Yace muje ciki akan magnar ne na kira ku..

Anty tana ganin Halifa ta dora sabon kuka, shi kuwa Baice kala ba haushin Anty ma yake ji in ya tuna abubuwan da ta yi masa.a haka tana ta rattafawa Halifa zance har su Bros suka shigo lokacin tana fadin wai ya kama Hafsa yana ta duka. Halifa yace "Dady baya duka gaskiya abinda ya saka Dady ya daki Hafsi to ba karami bane."

Dady ya cafke maganar da fadin Wai Yarinyar nan ta bude baki tana neman zagina a gabanta gata nan. "Zagi!!!" Halifa da Bros suka hada baki. Gata nan Ai a gabanta aka yi. Dady ya fada yana nuna Anty. Bros yace "Dady ai da ka yi ma shegiya dukan da zata suma, kyashi Dady ta fito da miji ko kuma a samo ko waye a dangi a tura masa ta karata mara hankalin banza kawai. Dady yace Nima na yi tunanin haka amma bari mu gama da abinda ya tara mu.

Anty ta kalli Bros Dan uban ka kai har kana da bakin magana, jiya in kira ka har sau nawa matarka ta daga tace bazaka zo ba dare ya yi ta kashe min waya ?Bros yace wace matar a ciki? Har nawa ne matan naka? Anty ta katse shi. Gabanshi ya fadi ya yi katobara,sai ya wayance da fadin To abin ne da mamaki Anty kin ce mata tace bazan zo, ba, to tama isa ta daga min waya ne,ki dai duba kinyi kuskuren kira ne amma jiya da dare ina gida. Anty tace 'E ai bansan lambar ka ba kuma kowa ya sani wallahi babu wanda zai yi wa Hafsa auren dole wallahi garama ku sake shawara,sannan dole Dady ya janye batun dawo da wacan matar nan gidan dan kuwa sai dai ya zaba ko zamanta ko nawa,dan kuwa bana son ganinta a gidan nan.

Dady ya kalli Halifa da Adamu yace ku bani hankalin ku kuma ina son ku fahimce ni sosai game da Zaman matar can a gidan nan.Acan inda take ni ke biyan haya kuma ni ke ci dasu,nan kuwa in tadawo na huta. Anty tace shi bata yarda ba. Bros yace To ke Anty menene matsalar ki da haka kowa da gefen ta? Tace haka kawai,nan gaba kuma sai yace zai aureta, ni ba damuna zai yi ba dan ya aureta amma abin kunya ne ace na hada miji da ita. Halifa ya ja tsaki yace duk kishi ne banda abin Anty tunda shine da gidan sa kuma kema karkashin sa ki ke ya yi yadda yake so da gidan sa.

Anty tace "Haka ka fada to ni na hakura da gidan nasa ya bani takarda ta zan kama haya. Dady yace To bari kiji cikakkiyar Magana sai dai karki zauna amma Bintu mata ta ce,na aure ta shekaru hudu da suka wuce muna da yara biyu Ahmad da Nasir yanzu kuma tana da wani cikin...

*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

[11/25, 17:05] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt

*Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302*

Tamkar mafarki Anty ta ji kalaman Dady wan da ke magana babu alamun wasa bare tsoro kokuma shakka .

Ba iya Anty ba Bros da Halifa sun girgiza da jin wadannan kalamai na Dady, dakin ya yi shiru kowa da abinda yake tunani, Lallai wata damuwar tafi karfin kuka, domin Anty da a banza ne da yanzu ta fadi tana farfarin mutuwa,amma yanzu gata zaune ta zubawa Dady ido wanda ke sauraro ko wani zai furta wata magana amma duk anyi shiru.

Ya yi gyaran murya babu mai abin fadi, in babu to kuna iya tafiya dama na sanar da ku ne dan naji Habiba tana ikrarin yi mata wani abu, karta sake ta soma,ku ne dai yanzu wadanda dole ku fada mata gaskiya. Cikin wata irin murya wadda da kyar Anty ta tattara yawun bakinta ta soma magana, "Yanzu kana ganin ka yi daidai kenan wannan cin amanar da ka yi min? Halifa ku du ba fa, kuji zancen nan shekaru hudu baya ya yi aure ban sani ba, ku baku sani ba,yanzu kana bashi gida har ya kawo matar,kuka ya kufcewa Anty Halifa in har ni yar uwar ka ce kuma na isa da kai ina son ka janye wannan kyautar Gidan da ka bashi." Ta ci gaba da rusa kuka.
Dady yace ki godewa Allah da ya tsaya a kishiya kawai, in dan ta halinki ne ba sai mutum ya kama bin matan banza a waje ba, me kika sani na kula da miji? Abinci saidai ki aiko yara su kawo min, shinfidata zaki iya tuna rabonki da kakkabe min bare ki kwanta akai? In na matsu da bukata ta sai dai na zo dakin ki inkin gama wulakantani da min ba a da gori da kira na jarababbe sannan in naci sa a ki bani hakina shima kina yi kina ke inyi sauri kina jan tsaki. A haka na rayu da ke, yanzu kuwa in azuminan ya zo shekara guda kenan rabon da ki bani abinda ya shafi hakki na kwanciya.

Ya kalli Bros wanda ya sunkuyar da kai,zantukan sun yi wa kunnuwanshi nauyi, Dady ya ci gaba da fadin dukkan ku ba yara bane yanzu, kowannen ku ya san yanayin da nake magana a kai, idan na yi aure dan in tsare mutuncina da na iyalina akwai laifi a ciki? Suka girgiza kai alamun babu. Anty ta katse shi da fadin Wallahi gara ace ga ka can an kama ka da wata akan wannan ranar ta yau ni a guri na. Bros Yace "Au'zubillahi minna shshaidani rajim,Allah ya tsare mu da mugunji da mugun gani, Anty infa rai ya baci hankali baya bata,ko mu da muke matasa bama fatan a samu haka a garemu bare mahaifinmu Dady Allah ya kara rufun asiri,in hali ya samu ka kara mata biyu Allah ne ya yarje maka, zan tafi dan bazan jure jin wadannan zantukan ba. Bai jira amsa ba ya wuce cike da bacin rai.

Halifa ya dago ya kalli Dady zuciyar shi tana fada mishi cewa kenan wata rana Asiya zata iya yi mishi fatan ya yi zina idan har Anty a matsayin uwa kuma kaka tana kauracewa mijinta tare kuma da mishi wannan fatan kila duk haka mata suke domin dai ba a haka suka yi aure ba. Halifa ya sauke ajiyar zuciya,Yace "Dady lokacin da zaka auri Anty amma tilasta mata aka yi ko? Cikin sanyin murya ya yi maganar.

Dady yace inji wa? Tana sona ina sonta aka yi mana aure, mun dai samu yar tangarda kafin bikin da yake muna tare da ita tun tana primary lokacin mahaifinsu yana raye, bayan rasuwar shi lokacin ina dako a singa ni na ci gaba da daukar nauyin karatun ta da kananan bukatu har zuwa lokacin da mahaifiyar ku ta auri mahaifin ka. Ganin sun koma gidan masu hali tunda shi mai kudi ne. Sai ta tsiro min da matsaloli da bukatun da suka fi karfina,nace na hakura shine mahaifiyar ku tace bata isa ba, kawai ma ayi auren mahaifinka shine ya yi mata komai kuma da zai yi auren yayansa ya hada da namu bai fi sati daya ko biyu da auren ba mahaifin ka ya rasu lokacin da cikin ka.

A haihuwarka Allah ya yi wa mahaifiyar ka rasuwa lokacin ni na bata shawara aka ta amso ka mu rike ka.Da kyar baffan ka ya yarda domin yace bamu taba haihuwa ba baza mu iya kula da yaro ba. Ni na dage muka amso ka, haka duk yadda za ayi ta samu ruwa nono na yi amma abin ya faskara sai dai madara na dinga saye duk sati wannan abokin nawa mijin Bintu ya sai madara ba sau daya ba
Na kawo an baka. Ai gata zaune tace karya ne in ta isa.
Lokacin da ta samu cikin Adamu renon ka gurina ya dawo, da kyar nake fita a gidan nan in kana kuka sai ka bini. Lokacin da ta haifi nata dan haka ta juya maka baya Lokacin na mata uzri dama ba kowace uwa bace zata fifita dan wani akan nata. Amma sai ta zo ta soma nuna kishi akan ka wai nafi kula da kai na fi sonka. Anty ta Katse shi "Au har sharri zaka hada min da shi?" Dady yace Ki rantse baki taba yin yaji kince in zauna gani ga Halifa ba, ai Babarku tana raye bata mutu ba. Sai da kika yi yaji akan na saka Halifa makarantar kudi wadda kike korafin nawa nake samu da zan saka shi, in bari danki ya isa makaranta shi a saka shi naki. Duk kayan wasan da nake kawo wa Halifa ba boye wa danki ki ka yi ba?

Keke nan da na sai wa Halifa kwacewa ki ka yi,duk sharri ne na yi miki? Halifa ya tuna maganar Keke lokacin da tace wai tana tsoro kar yaje mota ta takashi amma tabbas daga baya Bros yana hawa keken. Ya tuna wannan lokacin yana da wayo.
Chapter 49 · 0% Book details