Sashe 32
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya bashi sako cewa Asiya ta kunna wayar ta, kuma ya fada mata ya yi tafiya.
Bilkisu ta yi farin ciki da ganin Videon su Halifa kuma tana cikin wadanda suka kara yada abin da yin sharhi sannan tana ganin wannan. wata dama ce da zata samu shiga dan tasan kowane namiji dole ya saki wannan matar. Ita kuma lokacin ta zai fara. Saidai duk kira da sakon jaje da ta ke yi Halifa bai daga ba kuma bai nuna mata cewar ya ga sakonta ba. Dan haka ta soma fadada tunanin ta dan samu dama ta biyu.
A kauye Asiya ta kasa ci bare sha ga laulayi ga damuwa haka Baba Tabawa ta yi ta kokari gurin tausarta da kuma sama mata yan jike jike na gargajiya. Ta san zata iya jin saukin jikinta amma bazata iya jin saukin mugun raunin dake zuciyarta na soyayyar Halifa ba.. Sai a yanzu ta sake tabbatar da tana yi masa wani mugun so kuma makaho domin ta daina hango laifin sa a duk wadannan matsalolin ta fara dora alhakin a kanta, me yasa bata rufe dakinta taba har sai an kwankwasa kafin a shiga? Me yasa da Halifa yace karta tafi ta ki sauraron shi.
Gaskiya ita kam in har taji sauki zata koma gurin mijin ta wanda take bacci a kafadarsa wanda yake fada mata dadadan kalamai a kowane lokaci wanda ya maida ita macen da zata iya gogayya da kowace mace.
Halifa tun da ya sauka a ma sauki ya kasa aiwatar da komai har kusan kwana uku sannan ya fita kasuwa dan duba kayan da zai siya, ko yawan magana baya so abinci kuwa sai mara nauyi, bai sami nutsuwa ba sai da ya dira a Madina Ya yi ta gwada lambar Asiya har yau dai babu labari.
Anty ta kira Hajiya Talatu domin tattauna batun su Halifa, duk da tana ganin ta gama da Talatu amma tana zaton zata yi mata wani amfani. Cike da mamaki Talatu ta daga a tsorace ta amsa dan yanzu tana dan shakkar Anty. Kamar babu abinda ya faru Anty ta soma fadin "Sahiba kin dai yarda ni, tun daga biki na rasa me na miki tunda ni na damu da ke sai nace bari ni in kira. Talatu tace" Sahiba haka ma zaki fada ni da kika yi barazanar halaka ni. Anty ta saka dariya cike da makirci tace Ai ranar na tabbatar cewa ke matsoraciya ce wasa fa na miki haba Sahiba karfin jarumtarki na jarraba, in na barki kuma in kama wa? Talatu tace Humm ina jin ki, fadi abinda kike son fadi nasan amfani na ne ya tashi da kin gama sai ki yasar da ni.
Anty tace To kin yi min mummunan zato da ba haka bane. Yanzu dai ina son ki saurareni ina ganin lokacin auren Ma u da Halifa ne ya yi nasan dai shine matsalar ki, Anty ta ci gaba da fadin nasan kinga abinda yake yawo a Tiktok na Halifa.? "Mun gani inji Talatu sai dai ko kaffara bazan yi ba Idan na rantse da cewa sharrin ki ne. Anty tace " Banyi mamaki ba dan kin gane, domin a sharri ke uwata ce yanzu dai ina son ki bani haske game da yadda zan fidda yarinyar nan daga Rayuwar Halifa, Na fahimci asirin baya cin su makircin yafi aiki, dubi wannan fa cikin yan mintuna na yi tunanin sharrin nan kafin awa shida har Duniya ta dauka. Talatu ta katse Anty da fadin "Yanzu dai menene muradin ki? Tace Shawara nake son muyi dake game da yadda za a barar da cikin tunda na yi kokarin kar a same shi, amma sai da ya samu, Na sake yin abinda za a zubdashi har wa yau suka rayu to yanzu tunda na yi nasarar rabata da gidan sai dai hankali na ya tashi da naji Halifa yana fadin matar shi ce kuma dansa ne.
Hajiya Talatu tace "Kuma muka ji ance ya sake ta ya kuma koreta da muka kalla a Tiktok da Ma u ta kamo gurin? " Anty tace Yan karawa miya gishiri ne mu ai mune muka sa a Tiktok din ba wani ba, sauran mutane suka ci gaba da ingiza mai kantu ruwa kuma sai hakan ya kara armasa abin da zama ya gagare shi yanzu haka zancan da nake miki yana can chaina sai kura ta lafa zai dawo.
Hajiya Talatu tace har na hango abinda zai faru tunda baya nan amma ni menene ladana idan na tsara miki yadda komai zai kasance?" Anty tace A daura mishi aure da Ma'u shine kawai, sai mu hada kai da ita mu sa mu biyan bukatar mu.
Hajiya Talatu ta saki dariya tare da fadin na yarda da wannan Dan haka yanzu zan shirya in bar Zariya in nufo Kano kinsan ance shirin zaune ya fi na tsaye zamu tsara yadda za a sace ta a zubar da cikin Ko mu sake danna mata wani sharrin da zai kaita gidan Yari. Anty tace ina fatan ki Iso lafiya Sahiba ta. Hajiya Talatu ta saki dariya bayan ta kashe wayar tace lokaci ya yi da zan rama wukancin da aka yi min......
*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*
*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[8/13, 17:12] Ummi Tandama😇: Anty ta kalli Hajiya talatu cike da mamaki tace Wallahi Sahiba nasan kin iya shirya tuggu amma ban yi tsammanin har haka ba, yanzun nan sai da kika lissafa min kala daidai har a shirin wanda duk wanda na dauka a ciki sai na yi nasara. Cikin alfahari Hajiya Talatu tace "Ai Sahiba in kika ga na bar mutum ni na so, mutum nawa ke gidan yari wanda na yi silar zuwan su.? Kinsan Allah abinda kika min kwanaki wallahi wani abu na duba daban kawai na kyale ki, mutuncin da kika min a farkon haduwar mu bana manta alkairi ko yaya yake,amma wallahi da badan haka ba, da sai na shirya miki abinda dangin ki ma sai sun tsane ki.
Anty ta yi yar dariyar yake tace Sahiba kenan ai nima kawai dan na duba din ne amma wallahi danabi ta Malamin nan tuni zai batar da ke. Talatu ta saki dariya, tace "Ke matsalar ki tana da yawa wallahi. da kina duba mutunci bazaki sako dan kanin ki a gaba haka ba, duk abinda yake miki bakya gani kawai dai ki yarda ke muguwa ce ko ta ina." Anty tace naji yanzu dai mu koma kan maganar mu dan Allah na baki wuka da nama. Hajiya Talatu ta ja tsaki tare da fadin." Wai ba iya cikin kike son a zubar ba? " Anty ta amshe da faɗin Sai sakinta da nake son Halifa ya yi, wallahi da Adamu ne da tuni na sa shi ya sake ta, amma Halifa yana da taurin kai da muguwar zuciya, abinda ke bani haushi ya kasa kwada zuciyar akan yarinyar nan Sam. yanzu ma fa saboda damuwar ta ya bar gari ko kasar ma zan ce so nake kafin ya dawo na kammala ko mai sai kawai ya yi sabon Aure. Hajiya Talatu tace "Da Ma u na ba, "karamin alhaki ne wannan case din kawai zuwa zamuyi gidan nasu mu dauke ta zuwa Asibiti a kwakule abin banza a watsar mu maida ta mu dire. "
Anty ta ce to wane Asibitin zamu kaita kinsan dai babu wani Asibitin da za su yarda su cire mana ciki haka siddan ko? Hajiya Talatu ta yi wa Anty wani irin kallon raini Sannan ta ja tsaki, tace." Karki fada min cewa baki da daurin gindi a garin nan? Kina nufin baki da likitoci kamar uku da zaki iya kira su miki abinda kike so nan take? Baki da Yan sanda kamar biyar da zaki kira su a take ayi miki yadda kike so? Baki da lauyoyi da alkalai a hannun ki? Ke har faraskiton kotu da gandiroba San ina da su sunfi guda nawa. Ke yan daba ma ina da su saboda tsaro. Kuma duk wadannan Umarni kawai zan basu. Ta sake jan tsaki gaskiya naji kunyar hada hanya dake ashe ke gaba daya ma gwara kifin rijiya dake. "
Anty cike da muzanta tace Nifa bana rigima da kowa harda zan damu saina hada wannan gayyar ina zube musu kudi na. ke kuwa ai yar harkallace ko yaushe kin ari kudin wane kin cinye na wance. Hajiya Talatu tace" To yanzu wannan da zakiyi ya ci uwar harkalla, tunda kisan kai ki ke son a yi kuma Kaninki da ya yarda dake, ni kuma kinga ko wanda muke Uba daya bazan iya cuta ba bare cikin Ummana. Ta sauke numfashi. Kinga da kina da likita minti biyar ya yi yawa za a watsar da shi yabi sokawe. " Anty tace Menene abin yi dai yanzu? Hajiya Talatu tace yanzu muje yan magani mu sayi na zubda ciki muje gidan mu dauke ta mu kaita wani guri mu bata, ko kuma mu bata ma a gidan na su, in kuma zamu ja abin ya yi tsawo ka wai sai mu saka wani ya bata. Saboda karma a gane mu ne, amma fa zamu zama cikin zullumin na rashin tabbas. "