← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 62

Sashe 12

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki ta ja ta zauna a falon tana fadin kai ka yi kaɗan ka bi mutane wato sai dai kai a bika ko? To kowa ya rike maganar sa. Ta kalli yan matan tace ku yi hakuri, zan zo gidan. Wata ce take son mallake shi.

Muryar Hafsi Halifa ya jiyo a cikin kicin sai ya nufi can ya tsare ta da ido, me kuka je yi gidan su Asiya? Hafsi tace Uncle ni kawai rakiya na yi sai dai ka tambayi Anty. Yace "Karya kike yi, to da kuka je gidan me kuka ce?" Hafsi ta fito daga cikin kicin din, dan ta fara tsoron abinda zai biyo baya, zai iya yi mata duka, tace Uncle Anty ce tayi magana da su fa. Halifa ya yi tsaki ya fita.

*** *** ***

Ƙarfe goma kamar yadda masu gyaran jiki suka bukata Halifa ya kira Asiya yace ta shirya yana hanya. Yau Asiya nutsuwa ta yi domin tun amsa gaisuwarta Halifa bai sake magana ba, wannan ya sa ta shiga taitayin ta, tare da kame kanta. Har suka isa shagon yace in sun gama ta kira shi zai wuce kasuwa ne, ta yi masa addu'ar Allah ya bada sa a. ko da ya tafi bata bar mamaki ba tsoronta kardai wani laifin ta yi masa, ko kuma yanayi ne da ke sa mutum kan canza oho.

Yana tsaka da kasuwa kamar daga sama sai ganin Bilkisu ya yi a gaban shagon sa, duk da facemaks ɗin da ta saka hakan ba zai hana ya gane ta ba. Daya daga cikin yaran shi yace, me take son siya? Tace gurin Megidansu ta zo. Yace Bari a sanar dashi.

Halifa yace ta shigo ta zuna a kujera suka kawo mata lemo. Yana ta rubutun sa a wata takarda sai da yagama sannan ya kalleta. Lafiya na gan ki a kasuwa? Ta cire fasemarks din da ke fuskarta,ƙwalla na taruwa a idon ta ta ce. "Kaima ka san abinda zai kawo ni gurinka. Yanzu duk yadda muke baza ka yi min uzrin karamin kuskure ba? Afwa a soyayya wajibi ne Na maka Alkawarin har abada bazan sake ba, Wallahi Halifa ina son ka sosai bana bacci bana iya cin komai, zan iya mutuwa fa."ta ida maganar hawaye na ida saukowa kumatun ta.

Ya kalli yaran shagon sa dake ta Kallon kallo, domin kowa najin abinda take fadi. Ya yi kasa da murya domin zuciyar shi tana rawa, haryanzu yana son ta in har ya barta ta ci gaba da zantuka nan ba shakka zata iya shan kansa. Yace kije gida za muyi magana. Tace " Kai min rantsuwa akan cewar zaka zo, in har ka rantse na yarda ya yi shiru. Yana son ya Lallaba ta kawai ta tafi." In baza ka zoba kawai ka sanar dani gaskiya." Baka saba yin karya ba kar ka fara domin ka faranta min. Ta sake daure shi,. Kije zan zo amma gaskiya ba yau ba, amma tabbas zan zo. Ta mike tare da faɗin "Ina jira dan Allah. "

Zuciya Halifa ta fara rawa game da Bilkisu dan yana son ta, harya fara ganin kamar bai kyauta mata ba. Dole ya duba ya gani menene ya kamata ya yi.
Sam ya manta da batun Asiya tana gurin gyaran jiki yace in an gama ta kira shi zai zo da kansa ya maida ta gida,, kiran mai gyaran jikin ta sanar dashi sun gama tun dazu ya sa ya tuna. Ya tashi ya sallami yaran shagon sa ya nufi titin gidan zoo. Sai dai ya na zuwa gadar dangi sai ya samu kanshi da tunanin ya fara zuwa cikin gari akwai bukatar ya yi magana da Bilkisu. Ta yi mamaki sosai lokacin da ta fito tabbas kuwa shine.

Ta zauna a kujerar gefe bayan ta bude motar. Suka kalli juna tausayin ta ne ya cika zuciyar shi. Yace Bilkisu gaskiya har yanzu ina son ki, ina kaunarki matuka, amma kaddara ta sa zan auri Asiya, babu yadda za ayi in kaucewa Auren ta. Ina son ki dan bani lokaci kema zamuyi aure. Ta yi Dim domin taso ace ya hakura da batun wata sun shirya kan su. Ta soma hawaye cikin shashshekar kuka, tace "Bakomai na hakura zan jiraka, kuma ko ta Hudu ce in har zan same ka zan jira dan in ceci kaina daga mutuwa, nasan in har na rasa ka mutuwa zanyi." Yace baza ki rasani ba. Sun jima suna tattaunawa game da son da suke yi wa junan su daga bisani suka yi sallama bayan mai shagon ta sake kiran sa cewa sun kusa rufe shagon su.

Haka ya taho yana dan jin haushin Asiya.
Kallo daya ya yi mata tare da amsa sannu da zuwan da ta yi masa. Yace ta taso, bai kula wasan da mai shagon take tsokanar sa da shii ba tana cewa ya kaga amaryar fatan mu zamu yi mata kwalliyar ranar biki, ya dan yi yake tare da fadin " Insha Allah.
Asiya ta yi tsam da ranta sannan ta kame kanta ganin yadda Halifa ya zo mata ayau. Sai da suka hau titi sannan ta dan saci kallon shi tace" Shi bawa yana barwa Allah lamarin shi a duk yadda ya tsinci kansa. Kuma nuna bacin rai a yayi da aka samu kai a cikin wata jarrabawa tamkar kin karbar ƙaddara ce. "Wani Abu ne kika ga ya faru?" Ya jeho mata tambaya cikin kamewa.. Ta girgiza kai ba da kai nake yi ba ina kokarin haddace karatun mu na jiya ne na islamiyya. Ya kalleta ita ma ta dake kamar gaske. "Ina wayata?" Ya tambaya ta dakko cikin sauri tace gata nan. An cika ta da chaji a shagon matar nan. Ya kallo Wayar sannan ya maida kai titi tare da fadin " Zaki iya gane gurin nan gobe kar ki jirani zan baki kudin mota ki zo ki koma." Tace sosai kuwa ina fage ina gidan zoo da kafa ma zan iya zuwa sai in bullo ta gadar Nasawa. Gidan Murtala ina tsallakawa sai layin gidan IG in fito layin gidan Bashir Tofa.

" Ya aka yi kika san duk wadannan guraren? " Ya katseta da sauri. Tace na yi tallar Kankana da abarba a lokacin kakar su, yanzu ma ba dan zuwan ka ba da lokacin su na yi zanje Na'Ibawa yan lemo insaro in hau Dansahu zuwa titin gidan zoo daga nan in jera a tire ina tafe ina siyarwa har fage kafin naje ya kare. Kaga kuwa dole insan hanya. Bai kara magna ba har suka tsaya abin ya dame ta ta kalle shi. Tace To bansani ba nice ko a kasuwa ne wani ya sosa maka zuciya, amma dai ina mai baka hakuri Allah ya huci zuciyar ka a madadin koma wa nene . Bata jira amsa ba ta bude mota tafice ta nufi gida.

Ya kira Sulaiman a waya yace yazo mota za suyi magana. Ya dubi Sulaiman ya ce ina jin wani bacin rai game da Auren Asiya kamar in fasa, gaba daya da yamman nan haushinta nake ji. Sulaiman ya rasa abin cewa dan takaici dan haka ya zuba masa ido yana ta kallo da sauraron abinda yake fada. Sai daya gama Sulaiman ya bude mota zai fita. Halifa ya rike masa gefen riga tare da fadin ka ce wani abu mana.
Sulaiman yace babu abinda zance ka yi duk yadda ka ke so. Ya fizge rigarshi ya wuce.
Lamura sun cude, an taso Halifa gaba Hajiya Talatu na yi ga Anty, gidan su Bilkisu suma basu, zauna ba. Duk da Halifa mutum ne jarumi yana tsaye kan ibada, ga sadaka ance tsafi gaskiyar me shi, dan haka sai da abin ya taba shi har ya rasa gane abinda ya kamata ya yi.

Lamarin ya Shafi Asiya sosai har zuwa Ana gobe daurin aure bata samu ganin shi ba tun ranar da ya sauke ta. Dan haka bata koma takan mai gyaran jiki ba ga kuma jikin Baban su ya yi zafi. Ya sa aka kira mishi Baban su Sulaiman. Ya bar masa wasiyya cewar Koda Allah bai nufa ya ga gobe ba, yana rokon shi da su tabbatar an daura Auren Asiya, kuma yana son dan Allah ya sanar da Halifa cewa ya rike amanar Asiya kar ya barta ta yi kukan maraici.

Ana gobe daurin auren aka wayi gari da mutuwar mahaifin su Asiya, Babansu sulaiman shine ya kira Baffan Halifa ya sanar da su mutuwar mahaifin su Asiya kuma ya fada musu za a daura aure bayan an dawo daga Jana iza sakamakon ya bar wasiyya.
Halifa ya girgiza da jin labarin mutuwar kuma ya tausaya wa Asiya Dan haka shima ya nufo gidan mutuwar. Daren jiya ya gama yanke shawara da zuciyar shi cewa zai sa a daga bikin, sannan ya fara Auren Bilkisu, harma ya sanar da Anty hakan tana ta farin ciki tsarinta ya tafi yadda take so kuma aikin malaman ta ya yi ba shakka. To zata koma kan Bilkisu dan ta tsaya kar abin ya yiwu. Ita ce zata kawo wadda zai aura kamar yadda ta ke so.

Bilkisu ta yi farin ciki komai yana tafiya yadda malamin ya tsara mata, gashi dai Halifan nata ya dawo gadan-gadan.

Asiya suna ta kuka lokacin da za a dauki mahaaifinsu, ji take komai na duniya ya ishe ta, ina ma ace itace ta tafi ta bar su. Ji take bazata iya sake dariya ba har abada, Baban su ya tafi da dukkan farin cikinta.

Lokacin da aka dawo daga kai shi makabarta gidan cike da dangi da makota, sai kuma taji wai za a daura mata aure. Sabon kuka ta soma domin kanshi Auren ya fita a ranta, musamman yanda shi wanda zai aureta ya ja kafa cikin yan kwanakin nan har zuwa yau batasan ya lamarin ke tafiya ba.
Chapter 12 · 0% Book details