← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 62

Sashe 5

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kafin Anty ta karaso tuni Hajiya Talatu ta yi wa kanta masauki a dakin Anty Har ta cire kayan jikin ta ta dauki zanin wankan Anty ta daura, zata fada bandaki ta ji sallamar Anty, da yake munafukan juna ne nan suka hau ihun murna kowace tana fadin sahiba ta ga sahiba.

Idan matan nan biyu suka hadu ko shedan nasan gefe yake komawa ya yi kallo, domin dukkan su sunfishi hau. Nan suka zube a kan gado suna hirar yau she gamo tare da nuna kewar juna, Anty ta yi ta nuna jin dadin wannan zuwa da Sahibar ta ta yi. Tace ai kin fi min yan uwana su hudun duk mata ne amma ko kai lefen Halifa ba su zo ba, ke ko ganin kayan ba su zo ba.
Hajiya Talatu tace,, "Watsar da su ai gani, sai ranar biki su zo su ishemu da kararrafi." Sai kuma suka bige da labarin dangin su kowa yana aibata na shi suna zagin su.
Halifa ya shirya tsaf cikin shadda mai ruwan siminti ya kalli madubi ya so ya saka hula amma kanshi ya yi masa nauyi tun da ya sako kafarshi gidan, ga wani bacin rai da ya ke ji kamar ya hau kowa da zagi. Cikin zuciyar shi yake nanata La ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalumin. Ya sani duk bacin ran da Bilkisu ta haifar mishi ne, amma ko ajiyan baiji irin wannan yanayin tabbas ba. Ya fesa turare ko ma me yake ji dole ne yanzu ya tafi gurin yarinyar nan dan suga juna, domin yanzu in aka sata cikin wasu matan kamar ta ba lallai ya gane ta ba.
Ya fito yana rufe daki kamar daga Sama ya ji sallama a bayan sa, muryar mace ce dan haka bai amsa ba kuma bai jiyo ba saida ya gama kulle dakin, yana jiyo wa ga mamakin sa sai ya ga ta feso mishi wani gari kamar hoda, da sauri ya rufe fuskar shi tare da fadin a'uzu bikalimatillahi tammat min sharri ma kalaka. Ma u ta kyalkyale da dariya "Ango nice fa Asma u, ka tsorata ne hodar angwanci ce fa na fesa maka irinta al adar garinmu."
Ya bude fuska ya kalle ta rai bace. Ya daga murya "Ke wacece da zaki zo kina min irin wannan wasan ni sa an ki ne? Tace "Yi hakuri ta juya da gudu ya bita cikin gidan inda ya samu Hajiya Talatu da Anty a falo. Ko sallama bai yi ba ya dubi Anty Wace irin mara tarbiyyar yarinya ce ta shigo gidannan ta zo tana watsamin wata hoda wai wasa, da wa nake wasa a gidan nan har ita tasamu irin wannan damar!!
Anty ta mike, cike da fargaba da kuma zargin Hajiya Talatu. Tace Halifa nutsu ka fada min me ya faru? Hajiya Talatu ta yi caraf yanzu haka Ma u ce, Sarkin tsokana al adar mutan garinmu ta yi maka, ka yi hakuri. Halifa ya kalli Hajiya Talatu dan Allah ki gaya mata ita mace ce ya kamata ta kama kanta, amma ni in har ta sake yimin irin wannan haukan to zan mata jahilci. Ya juya ya fice ya koma ya bude dakinsa dan gyara jikin sa.
Anty ta kalli Hajiya Talatu ta ce Sahiba da wace fuskar kuka zo gidan nan? Talatu ta yi yar dariya "Wai har kin saka wani tunani daga dan wannan wasan Sahiba? To zuciya daya muka zo kuma lafiya zamu rabu." Anty ta soma kwalawa Ma u kira ta zo da sauri tana dariya kamar wata sakarya tun kafin Anty ta tambaye ta har ta soma zuba, Anty na ba Uncle Halifa tsoro ashe haka yake da fusata? Tsawar da ya yi min har yanzu hanjin cikina bai kwance wani kulli da ya yi min ta nan gefen ba. "Da Allah yi wa mutane shiru! Anty ta daka mata tsawa. Indai ma wani tunani ki ke akan Halifa to ki sani ba irin mace da yake so bace ke.!" Hajiya Talatu ta danne fushi da ke son ta so mata. Anty ta sake fadin "Ina mai gargaɗin ki da babbar murya daki bar bala i ya yi bacci, ki bar hanyar dakin shi har kubar gidan nan ke rashin kamun kan naki ko a ina sai kin nuna shi?!"
Ma u ta zo wuya ta kalli Mahaifiyar ta sai ta girgiza mata kai, sannan ta yi mata alama da ido wai ta bada hakuri. Dan haka cikin sauri tace Kiyi hakuri Anty bansan zaiji haushi ba. Ta kalli Hajiya Talatu Mama ki bata hakuri. Hajiya Talatu tace, " Ba zan bata ba, ai dama zane ki tayi ko shi Halifa ya daura miki mari kinga Ma u bana son dibar albarka ai da nasan haka zakiyi bazan taba zuwa dake ba sakara da Allah wuce mana a nan."

Anty ta cika da mamaki domin wannan ne karo na farko da Sahiba ta yarda yarta ta yi ba daidai ba. Dan haka ta saka a ranta cewa da walaki goro a miya domin banza bata kai zomo kasuwa. Dan haka dole ta baza idanu ko ta ina dan kula da abinda Sahiba da yarta za su aikata mata a gida. Kalaman Hajiya Kaka suka dawo mata inda take cewa ga wata masifa nan zata sauka a gidan ki, gobara daga daji maganin ta sai Allah.

Hajiya Talatu ta mike ta bi bayan yarta, bari in je inci kaniyar ta. Ta katse wa Anty tunani.
Anty ta taba baki in ma lallashinta zaki je ku dai kuka sani.

Hajiya Talatu ta samu Ma u tana kai da kawo a cikin dakin Hafsi inda nan ta kwana. Ma u ta tari numfashin uwar da cewa amma Mama kina jin irin bakaken maganganun da matar nan ta yi min kuma wai ke ma ki ka biye mata. Hajiya Talatu ta yi kasa da murya tace "Dadina dake gaggawa, Ma u shifa yaki da ki ke ji da gani dan zamba ne. Kar wannan abin ya daga miki hankali nan gaba kadan komai zai dawo hannunki sannu a hankali sai kin rama duk wani wulakanci da kowa ya yi miki. Yanzu fada min kina ganin ya shaki wannan hodar? "
Ma u tace duk da dai ya sa hannu ya tare fuskar sa amma har atishawa naga ya yi, wannan ke nuna ya shaka. Hajiya Talatu tace angama sai mu jira sakamako nan da gobe.

Asiya tana yanka awara ta kalii Sadiya tace, Maman Annur kinji wai anjima abokin Yaya Sulaiman zai zo da bayan Isha i. Sadiya ta sa dariya tace "Mijin ki zaki ce." Inna tace to ai da baki yi awarar ba me ya sa baki fada ba?
Asiya tace to zamu fasa yin abinda zamu samu abinci? Ni ina ganin ko Abba zai iya zama ya siyar min idan ya zo. Inna tace shike nan in kin shigo sallar Ishai sai ki jira shi a gida kar ya same ki gurin suyar. " Asiya ta ce to. Sadiya tace" Inna a ciro mata dan turare a kayan lefen nata ko? " Inna tace e mana har da Hoda da janbaki. Murmushi Asiya ta yi a zuciyar ta tana kara sallamawa ga lamarin Allah. Wai ita ce yau zata yi aure wadda ko saurayin bata da shi, wadda yan matan layi suke mata Kallon kazama, gashi ita ba wata kyakyawa ba sirantaka kuwa wasu har ce mata suke sullen kara. Masu tura kurar ruwa sunfi nuna suna sonta wasu ma da lalata. Sai gashi jiya zuwa yau Allah ya kawo wani sauyi nan take.
Tana ta sauri ta kwashe awarar da ke cikin mai ta. tashi ta shiga gida domin ga shi can ana ta salla a massalaci. Tana cike da tunanin yau yanmata layin su sun bata mamaki sai zuwa suke suna tambayarta Wai lefenta aka kawo yau she ne bikin? Har da masu cewa ta kawo masu ankon in an fitar. Hakan ya sa taji ashe ita ma takai.
"Nawa awara?" Aka katse mata tunani da tambaya. Uku Hamsss ta kasa karasawa lokacin da ta dago ido ta kalli mai tambayar ba zata tantance saurayin nata ba, amma wannan taga ya mata kwarjini ya kuma cika gurin. Ya tsuguna ya dauki guda daya, tare da fadin." Akwai alakoro kasuwa?" Ta sunne kanta a cinya sannan ta tashi da gudu ta nufi cikin gida.
Sadiya ta taimaka mata ta gyara duk da wata zuciyar tana tambayar ta cewar tana da tabbacin shine? Ta fesheta da turaruka ta yi gayunta cikin atamfarta raifes ta sallah ce. Sadiya tace to kije zan zubawa Abba awarar ya kawo masa. Inna tace ga hamsin yazo ya amso fiya wata me sanyi gida Maman Huda.
Chapter 5 · 0% Book details