Sashe 20
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata safiyar Juma a taje gaida Anty da safe suna tare da Hafsi, ta gaida Anty wadda ta ke amsawa da kyar kullum cikin lissafin yadda zata bullowa wannan shegiyar yarinyar take, ta dubi Hafsi tace ina kwana? Hafsi tace "Ni bangan shi ba, kwana nan. " Asiya ta kama hanyar fita Hafsi ta ce "Dubi yarinyar nan tafa murmure Anty wai ace ubanka ya mutu amma ka manta ka zo ka yi ta shagalin ka da namiji.
Anty ta saki dariya Asiya ta fice da sauri dan bata son jin abinda Anty zata fada. Ta samu Halifa ya fito wanka ta hada masa shayi da wainar kwai da dankali. Yana karyawa suna hira, ya gama ya mike yana mika tare da fadin zan tafi kasuwa gashi bayana na ciwo zo kimin tausa. Suka shiga daki kasuwa dai ranar sai da ya yi azahar ya ci abincin rana.
Lamarin da ya sa Anty shige da fice, da dogon nazari, yadda ta san Halifa ina ka fito kasuwa ina zaka kasuwa ko ciwo Halifa ya ke yi sai ya fita kasuwa amma wai ace shine saboda wannan mokadaddiyar yarinyar wai Halifa har azahar yana gida me gareta ne da zata bashi har ya zauce irirn haka. dole taje ta yi masa magana tun goma na safe ta ke aike ana duba mata motar sa har aka yi salla bai fita ba.
Ta iso kofar dakin daidai lokacin da Asiya ta rako shi zai tafi tana fadin Dan Allah Yaya idanun ka amana ne karsu kalli kowa sai kwastoma.
Yace "Kar ki damu kanwata ai nima yanzu idanun na sun rikide sun zama irin naki, ba sa ganin Kowace mace a matsayin mace face ke,sauran mata yanzu duk Kallon maza nake musu." Yakai karshen maganar tare da kamo hancin ta cike da wasa.
Turus suka yi ganin Anty. Ta kalli Halifa cikin fuskar tausayi tare da fadin Jikin ne Halifa?" Yace jiki kuma Anty kamar yaya? Ta kalli gurin motarsa, gani nayi nafita motarka tana nan baka dauka ba har na dawo baka fita ba wanda hakan ba al adarka bace baka wasa da nema." Ya dan sosa kai, Wallahi Anty ga wadda ta cikani da hira nan. Ya nuna Asiya cike da wasa.
Asiya tace au Yaya haka ma zakace, cike da shagwaba ta kalli Anty tana fadin Wallahi Anty ba ruwa na nikam shine nan yaki tafiya.... Ke dalla yi ma mutane shiru inda zama yake a gidan ya samu abinda zai kawo ki gidan? Halifa ya kalli Asiya da sauri saboda hantarar da Anty ta yi mata. Ji ya yi har cikin zuciyar sa baiji dadi ba.
Asiya ta sunkuyar da kai ta ki dagowa Halifa ya tausasa murya yace Baby ki koma ciki kinji za mu yi waya. Ta dago kai ta dube shi cike da fuskar tausayi ta daga masa hannu tana masa bye bye ta Juya ciki da dan gudu. Ya bita da kallo ta kullo kofar.
Ya kalli Anty yace Wannan fa bai dace ba Anty, dan Allah ki kama girman ki banji dadin abinda ki ka mata ba. Anty tace "Ba shakka lallai Halifa ni kake jawa gargadi akan matar ka, har zamu fara da haka? To ina mai baka shawara ka kama kanka kaima.
Ya wuce rai bace baice komai ba. Tunda ya fita a motar ya kira Asiya ta daga tare da fadin" Baby ki yi hakuri kinji ni?" Asiya cike da shagwaba tace haba yayana ai ni ba haushi naji ba, Anty ai Anty mu ce, tana da dama ta yi mana fada in munyi ba daidai ba taya zanji haushi kai ne kace wai in koma ban raka ka mota ba, kuma baka min wannan sumbatar da kake min ba kuma bakace in kula da kaina ba kamar yadda ka ke yi.
Ya yi yar dariya "Shike nan ayi hakuri zan biya bashi gobe Allah ya yi miki albarka."Ameen na gode mijina Allah ya tsare gaban ka da bayan ka, ya kai ka lafiya ya kawo rabo mai amfani." Ameen masoyiyata ina kaunarki. Tace me zan dafa maka anjima? Komai me dadi, in babu wani abu na girki da ki ke bukata kimin waya zan aiko. Asiya ta ce to. Bayan sun yi sallama Asiya ta yi shiru tana tunani ba shakka zata sha wahala da Anty amma ta san yadda zata bi da lamarin insha Allah.
Anty ta kara tunzura sosai karfa yarinyar nan tace zata shigar mata hanci da kudundune. Ta koma tana fadawa Hafsi abinda ya faru. Hafsi tace " Anty gara ki dauki matakin ɗan hakin daka raina shine yake tsole maka ido. Anty ta yi kwafa, tace ina takaicin sakacin da nayi ne har ta samu dama ta shigo cikin gidan nan. Hafsi Tace" Anty ai baki makara ba,,ki ka kori mai 'ya' ya ma bare wannan tsuntsuwar karamar alhaki. " Anty tace To Hafsi in kin haifu cikina ko ke din nan zaki fidda ta gidan nan. Hafsi ta sa dariya tana fadin " Sai dai in baki bani Umarni ba ta jima ta yi sati daya in na dinga tashin balli a gidan nan... "
Anty ta sa dariya ke abinda ba kamar yadda ki ke tsammani bane. Halifa zai iya raga min amma ke ubanki zai ci ba ruwa na. Hafsi ta saka dariya tace "Anty in har dai kin bani dama to ki zuba min ido ki bani sati daya, kowa dai da irin baiwar sa da kuma tasa Basirar ke tsohon lissafi ki ke yi, ni kuwa yar zamani ce.
Anty cike da mamaki tace ba shakka dama ance magaji mafiyi. To na baki dama sai dai ina son ki rinƙa sanar dani duk abinda zaki yi. "Ba matsala." Hafsi ta fada cike da yakini.
Asiya ta gama aiki tana zaune tana tunanin yadda zata bullowa Halifa ya yarda ya kai ta gida, tun jiya take latsa shi amma yaki zancan. Ko abinci take ci sai ta tuna Umman su da Sadiya da yaranta da kuma Abba, ta yanke shawara in har yaki kaita zata sa ya kira mata Yaya Sulaiman ya je ya kai ma su Inna waya mu gaisa.
Sallamar Hafsi ta katse mata tunani ta amsa kamar abin kirki ta shiga ta zauna Asiya tace za a kawo miki abinci? Hafsi ta ce tab "Gaskiya ni ba kowane kwado nake ci ba, da ƙazanta shi kanshi Uncle na yi mamaki yadda yake da kyankyami amma har kike yin jagwalgwalo yake iya sawa a cikinsa mai daraja!.
Asiya ta yi murmushi tare da fadin Kina da gaskiya sai dai kuma shi Uncle din naki kullum cikin yabon wannan jagwalgwalo da ƙazantar ya ke, ga shi yana santi, ta kai hannu ta dakko wayar tare da fadin kiga, kalli tukwaicin da ya bani. Hafsi ta kalli IPhone 13, ta zaro ido wayar da take ta naci Anty ta sa Halifa ya bata shine ya ba wannan wadda bata san darajar wayar ba. Asiya ta ce ya kikaji a ranki? Kin taya ni murna? Hafsi ta mike tsaye ta nuna Asiya da yatsa, tana fadin "Yana da kyau ki shiga hankalin ki, domin ni ba sa ar ki bace, kuma duk bala'inki wallahi sai ki fita a gidan nan banza yar matsiyata"
. Asiya ta yi yar dariya tace to zamu gani, gaskiya domin mutuwa ce kadai zata iya rabani da mijina, ina miki addu a Allah ya baki mijin irin nawa. Ta kaici ya kama Hafsi ta rasa me zata ce ta zuba ma Asiya ido tana huci . Asiya tace to ya kika ji a ranki, ba dadi ko? To ki kiyaye da cin zarafin mutane. Hafsi tace zaki yi da kinsani ta fice tana huci.
Halifa ya yarda zasuje gidan su Asiya tare sannan da dare murna gurin Asiya zata ga Inna.
Sun fito suka shiga dan yiwa Anty Sallama ya ga Hafsi tana ta cika tana batsewa, cike da raha ya ce Dota lafiya kuwa? Ta turo baki tace lafiya lau Uncle dama so nake ka dawo in kawo maka karar matar ka. Anty Asiya. Anty tace Kash Amma dai tun da kuka yi abinnan dazu nace kiyi hakuri ko? Shi aure ai lokaci ne da shi. " Cike da mamaki Halifa yace me ya faru? Anty tace waya sanar musu ni ko sauraron ta banyi ba, banda abinta ma da me zai sa tace wai zata je ta koya mata girki? Hafsi tace Uncle Dan Allah laifi ne idan naje sasanka na taya matar ka aiki? Ya girgiza kai alamun a a. Taci gaba shine ina zuwa wai ta ce wai in tafi bata so kuma in je inyi aure nima wai na tsaya yawo banza banda ko saurayi Wai me bakin jini.
Halifa ya kalli Asiya wadda mamaki ya hana ta yin magana sai Kallon Hafsi ta ke ta yi cikin daga murya yace menene gaskiyar lamarin??
*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*
*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[6/24, 08:20] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w/9223372036854675807
*🔉 NASIHOHIN MALAMAN SUNNAH🔉*
Manzon Allah (saw) yace duk wanda wani bala'i ko damuwa na daga al'amuran duniya ke damunsa, idan ya yi ɗaya daga cikin waɗannan addu'o'in Allah zai yaye masa damuwarsa:-
1️⃣ LA'ILA HA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZZA'LIMIN.
2️⃣LA'ILAH ILLALAHU AZEEMUL HALIM,LA'ILAHA ILLAHU RABUL ARSHIL AZEEM, LA'ILAHA ILLAHU RABBUS SAMAWATI WARABUL ARDI WARABUL ARSHIL KAREEM.
Asiya tace a ranta wai haka abin ya zama kenan, dan haka sai ta yanke shawarar zuwa musu ta yadda basa zato. "Ina sauraron ki, Asiya cike da kwanciyar hankali tace duk yau yaya banga Hafsi ba sai yanzu. Gaskiya ba dani bane. Halifa ya kalli Hafsi" Kinji me take fada? Hafsi tace ki fadi tsakanin ki da Allah."