← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 62

Sashe 41

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Halifa kuwa dama ya na kai karshen maganar shi ya kashe waya,sai dai kuma kukan da ya ji Anty ta saka ya tsaya mishi a zuciya. Ya soma tuhumar kan shi, wai ma akan wane dalili ne ya yi irin wannan fushin haka? Saboda abin duniya kudi abin banza. Kayan lefen me? Ya dauki waya kamar ya kira Anty amma sai ya fasa,domin ya san halinta yana kiranta dan ya nuna mata ya yi kuskure zata hau dokin zuciya sai ya yi ta bata hakuri zai jira ta neme shi tukunna.

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*

*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w

Asiya Ta bude ido dakin kowa ya yi bacci Inna ma tana kan tabarmarta ta tada kai da da kullin kayan su wanda Inna ta hada da safe za su tafi Dawanau ganin likita. Asiya ta sauka a hankali ta fice daga dakin, Asibitin ya yi tsit wannan ke nuna dare ya yi nisa

Ina zata ga Halifa yanzu tana son ta samu tabbaci akan sakin da ya yi mata. Bata da kudin mota amma haka ta ci gaba da tafiya kanta ma gaba daya ya juye bata san ina take saka kafarta ba.

Kadan wani mai kekenapep ya bige ta, yace ke Malama ta shi a hanya mana? Tace dan Allah ina neman hanyar Gandune gandun sarki .Yace Kina kan hanya amma dai ba a kafa zaki ba ko? Tace to dan Allah ko zaka taimaka min wallahi daga Asibiti na ke. Yace can din gun wa zaki je? "Ta ce gidan mijina zani. Ya saki baki yana kallonta. Yarinya ce karama kuma gata wata iri amma kuma kamar mai ciki. Yace kinsan gidan kuma yana nan mijin na ki? Sai lokacin ta tuna in kuma yana can gidan su Anty fa? Amma saita ji zuciyarta ta yarda cewa zata same shi a sabon gidan.

Ta dube shi,in Allah ya yarda yana nan. Yace To hau muje amma ni da har na tashi daga aiki wai nawa ma zaki bada? Tace ko nawa ka ce zai baka muje kawai ta fada cike da kwarin gwiwa.

Sun fara tafiya sai yace "Wai to ki kira shi a waya mana. Tace wayata ta mutu ko kana da waya ka ara min ?' Yace kin rike number ne?' Tace Na rike.

Ya dakko wayar ya bata. Ta saka lambobin gabanta yana faduwa.

Tana kira ta fara ringing sai dai har ta katse ba a daga ba. Ta sake kira sai aka danna busy Tace Allah ka bashi ikon daga wa, wannan ce dama ta Allah ka ceci aure na. Me a daidaita ya ce ko baya daga wayar da bai sani ba? Asiya tace yana dagawa dan kasuwa ne fa.

Ta sake kira cikin sa a ya daga tare da sallama. Jin muryar shi sai tsoro ya kamata ta kasa magana. Yace "Hello ka na jina kuwa?" Cike da rawar murya Asiya tace Yaya ni ce Asiya kana ina ne gani nan zuwa. Ya maimaita sunan Asiya yanzu da tsohon daren nan daga ina ki ke tace daga Asibiti.
Nan take Halifa ya zabura ya mike dazu Baffa ke fada masa cewa Abban su Sulaiman ya fada masa bata da lafiya har ana maganar zuwa dawanau dan haka su aje maganar a gefe sai yarinyar ta samu sauki. Yanzu haka abinda ya hana shi bacci kenan yana tunanin wane irin ciwo ne sai anje dawanau? Zuciyar sa ta zuga shi akan kar yaje Asibitin domin yaji matukar bakin cikin sammacin da aka kawo mishi. Ya ce Asiya to kuna ina yanzu? Tace kana sabon gida ne can zamuje. Yace Ina can ke da waye? Tace Dan sahune yace bashi wayar." Ta mika mishi yana amsa Halifa ya ce kar ka tsaya ko ina ka wota nan Gandun Sarki ya yi masa kwatance.

Bakin layin ya fito ya tsaya. Sai ga su a dan sahu. Halifa ya tsaya cike da mamaki yana kallon yadda kiwon sa ya lalace, yarinyar ta rame ta yi baki ta koje,sai ciki kwi kamar an kifa kwarya. tana zare idanu. Ta nufo shi tana kuka ta shige jikin sa,ji ya yi gaba daya tana wani irin tsami. Ya dago fuskarta yace Asiya hakan da ki ka yi kuma adalci ne a gare ni? Bata yi magana ba,ya kalli dan sahu 'Nawa ne kudin ka?" Ya tambaya bayan ya rungumeta gefe daya yana laluba aljihunsa.Dan sahu yace kawai ka bada Megida aikin ma na tashi kawai dai taimakonta na yi can waje Tukuntawa na ganta.

Duk da Halifa bai zaci zai samu kudi ba domin jallabiya ce a jikin sa,sai ya ci sa'ar samun wasu sabbin yan dari biyu irin wadan da yakan je da su sallar Asubahi dan rabawa sadaka. Bai tsaya kirga su ba ya ce to Oga gashi ka yi hakuri da wannan na gode. Dan sahu ya amsa yana fadin "Nima na gode megida."
Har ciki Asiya ta yi karkadaf da Halifa kamar tana tsoron kar ya kwace mata.
Sai da suka shiga lafo ya sake tsorata da hasken fitila ya bayyana ta sosai, idanu sun yi jajir ya zaunar da ita kan kujera ya dakko ruwa mai sanyi daga firji ya bude ya bata. Ta amsa ta kama sha har sai da ya tsorata wata zuciyar tana fada masa ko dai tabuwar hankalin da gaske ne Baffa ya ce za su je Dawanau,ya yi sauri ya amshe ruwa har tana kware wa,cikin tari tace "Yaya zan kara.' Ya bata tare da fadin To kisha a hankali.
Ta shanye ruwan tas,sannan ya zuba mata madara mai sanyi cikin kofi ta shanye sannan yace in kara miki? Ta gyada kai. alamun e,ya kuma zuba mata ta kafa kai karshe dai sai data shanye madarar da ya ke sawo wa su kwana biyu suna sha. Yace tashi kije kiyi wanka. Ta shiga bandaki yaje ya tsaya ya hada mata ruwan zafi a bahon wanka yace ta wanke jikinta sosai dan tana tsami sai ta kuma hada wani ruwan ta kara wanke wa. Ita dai kai kawai take dagawa, domin mugun ciwon kan da ke damunta yasa tana jin kan kamar ba a jikinta ba.

Ya dawo yana dubawa ko zai ga kayan da zata iya sawa,amma babu kayanta a gidan sai wadanda ba a dinka ba duk dinkakkun ya kai mata.karshe ya dakko jallabiyar sa ya tafi bandakin dan yaji shiru.
Turus ya tsaya bacci take a ruwan ta cuda jikin bata dauraye ba.A tsorace ya karasa ya girgiza ta ta bude ido luuu ta kuma lumshe su.Ya koma ya cire ya dawo daga shi sai gajeren wando,ya zage ya wanke ta tas ya dauraye ya nado abar sa a tawul.

Ya kwantar da ita ya ja bargo ya rufe ta.Ya dan rage karfin Ac, ya zauna bakin gadon yana kallonta, fargaba ya cika zuciyar shi,ya rasa wa zai kira ya ce gata nan ta zo. Daga baya kuma sai ya yanke shawarar yin shiru da bakin shi haka zai taimaka ya san wasu abubuwan dake bibiyarta.

Sai dai akwai bukatar likita.Nan take ya kira likitan da suke zuwa gurin sa ya fada masa yana da mara lafiya da yake son likitan ya taimaka ya zo ya duba masa. Likitan yace Har ya kwanta amma yana jin nauyin irin alkhairin da Halifa ya ke masa dan haka yace To ya kwatanta masa gidan zai zo.
Kusan mintuna Talatin sai ga likitan ya zo Halifa ya zura mata jallabiyar sa sannan ya shigo da likitan Gwajin farko na hawan jini ya ga ya haura dari biyu,ya tsorata sosai ya ce wannan zai iya taba mata kwakwalwa tun yaushe take fama da ciwo? Halifa yace wallahi bai sani ba jiya ta zo daga gidan su. Likitan yace To zai mata allurar bacci tare da wasu allurai ya barta ta yi baccinta sosai ko ta kai rana bata farka ba kar ya tashe ta,sai ta tashi dan kashin kanta sai su zo Asibitin. Halifa yace Ranka ya dade ka yi hakuri ko nawa ne zan biya ka dinga zuwa kana dubata a gida. "Ba damuwa in ta farka sai ka sanar dani. Likitan ya fada da sauri.Halifa ya raka shi mota tare da fadin Yallabai katuro min da account. Dr yace Ina godiya Alhaji. Dr Yana jin dadin yadda Halifa yake girmamashi. Duk da ya kula haka dabi ar shi take yana da girmama kowa.

Ya koma Shima ya kwanta ya zuba mata ido yana kallon ta bai yi wani bacciba sosai kadan kadan ya farka..

Ya dawo masallaci yana zaune a falo ya daga waya ya kira Baffa yana tambayar shi ko ya labarin jikin Asiya din yana son sanin inda magana ta kwana dan zai yi tafiya ne zuwa Dubai. Baffa yace bai sake tuntubar su ba,amma ya dan yi hakuri zuwa ta warware. Sannan yace ya daure yaje ya dubo ta. Halifa yace sai in ya dawo domin nan da awa daya jirgin su zai ta shi. Halifa ya yi haka ne dan kar ko cigiya ta biyo ta gurin Baffa ya kawo shi a ransa. Dan shine kadai ba zai iya yi wa karya ba.Ya kira Bros ya fada masa cewar ya tafi Dubai.
Chapter 41 · 0% Book details