← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 62

Sashe 42

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inna ta samu bacci domin yau babu koke koken Asiya da alama itama ta samu bacci.Wani ikon Allah bata kula babu Asiya a gadon ba har sai da ta idar da salla ta soma hada kaya dan da wuri zasu tafi Dawanau din dan ganin likita. Taje tashin Asiya ta yi salla sai ta ga gadon babu kowa,ta daga abin rufar da sauri ta yi bandaki kafin minti goma labarin bacewar Asiya ya baza Asibitin. Aka ce taje gida ta gani ko can taje,sai kuma ga Sadiya da kokon su na kari,tace Asiya bataje ba.

Inna ta soma kuka Sadiya kuka. Likita yace shi dai tsoron shi kar ciwon ya yi karfin da zuciyarta zata dinga bata umarni mara kyau kuma ta na bi.hakan babban hadari ne in ba a kula ba sai taje ta fada wuta ko ruwa wanda zai halaka ta.

Haka suka bazama neman ta ga shi su ba waya ba bare duk inda suke zaton cewa tana can su kira su ji .
Nan fa Unguwar ta dauka Asiya ta bata a Asibiti wasu su ce ance ta haukace ne har mutane suka soma ba Inna shawara wai su bi bololi su duba.

Haka Inna suka gama yawo har sha daya na dare suka fawwala wa Allah suka dawo gida suka zauna. Sai kuma gobe su ga ta inda za su fara.

Asiya bata farka ba sai karfe biyu na rana. Halifa ya tsorata amma likitan ya ce masa babu komai da yake suna waya.

Ta yi mika da salati ta bude ido, ashe dai ba a mafarki bane gidan Halifa ta ke, ta tashi da sauri ta zauna a tsakiyar gadon. Halifa ya fita ya karbo abinci a restaurant yana shigowa ya ganta a zaune.

Da sauri ya kara so ya na fadin kin tashi babyna,baby na ya jikin naki? Asiya ta lumshe ido tana kallon abincin da ke hannun shi. Ya ce zaki ci? Ta daga kai alamun e. Ta kama abinci ta cinye a take away din ko plate bata bari an dakko ba,cikin mamaki yace ko a karo miki? Sai lokacin ta yi magana ",Na koshi. Yace Alhamdulillah tun jiya sai yanzu kika yi magana har na fara tsorata,yanzu me yake miki ciwo? Tace "Kai na ne ya ke yi kadan kadan kuma ya yi min nauyi sosai." Yace zai bari likita yana zuwa.
Kiran likitan ya katse masa magana. Ya daga yace masa ya shigo.

Likitan ya duba hawan jininta ya dan ragu akan jiya,yace Insha Allah zai sauka da sauri tunda bata kumbura ba saboda ciki hakan ba zai shafi abinda ke cikin ba.

Saidai tana bukatar a kwantar mata da hankali,duk abinda zai daga mata hankali ko ya sata tunani a yi kokarin kauce masa. Yace shi kanshi likitan da ke kula da ita bai san aikin shi ba,tana da irin wannan hawan jinin bai sha kan matsalar ba kuma zai tura su wani Asibitin. Ya bada magunguna kuma zai ci gaba da zuwa duba ta har ta warke,sannan ya sake bada shawarar kar a barta cikin hayaniya. Halifa ya kudirci ba wanda zai san inda take.

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*

*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

[10/16, 10:31] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w

Inna sun gama sarewa amma dai sun kai rahoto tare da hoton Asiya karkashin jagorancin Sulaiman.

Sulaiman sun yi magana da Halifa ta chat cewa ba a ga Asiya ba. Halifa ya nuna wa Sulaiman damuwar sa musamman saboda cikin da Asiya take dauke da shi, yace yana Dubai amma zai dawo duk da bai gama abinda ya kai shi ba sannan
Yace wa Sulaiman dan Allah ya yi iya kokari shi dan ganin an samu labarin Asiya.
Labari ya riski Anty farin ciki kamar me bata boye ba sai ma tunaninta ya tsaya akan aikin da ta sa malaman ta ne ya ci Asiya.

,. Inna ta rasa wane irin tunani zata yi ta yi kuka ta yi addu'a tace dama Asiya mutuwa ta yi ta ga gawar a gaban ta da sai ya fiye mata wannan bakin cikin.

Wasa gaske yau gashi har kwana uku,Inna ta gama debe tsammanin har wata gawa suka je suka duba da aka ce an tsinta a ruwan jima, su ka ga ba ita bace ta dawo gida ta ci gaba da addu'a amma a kasan zuciyar ta tana zargin wani abu.

Cikin kwana uku Asiya ta dan murmure ta dawo ciki hankalin ta. Halifa ya siyo mata jallabiyoyi da riga da wanduna dan ta ke sakawa. Suka fita da dare suka tafi dan a wanke mata kai. Ta yi kyau matuka sosai, ga turaruka ya saya mata tana ta kamshi, ya kai hannu ya shimfida su akan nata da ta aje a gefen ta, ya dan murza yace Asiya har yanzu ina mamakin yadda ki ka iya share ni tsawon watanni baki tunanin halin da zan shiga ba ki kusa da ni ko bayan ke kinsan mijinki bashi da juriya? Sannan wai har ki ka iya kaini kara kotu Asiya ina mamakin ki fa. Asiya tace Yaya wallahi ba ni bace itama Inna taji haushin takardar sakin da ka aiko min ne.Bai san lokacin da ya taka birki ba, tare da fadin saki? Har ya rage kaɗan wata mota ta daki bayan su.Bai damu da me mutane suke fada ba, a gurin ganin yadda ya kusan hada hatsari. Tambayar Asiya ye ke yana maimaitawa . Saki fa ki ka ce,waye ya kawo takardar? Asiya tace "Kana nufin baka aiko min da saki ba?" Yace Haba Asiya ke yanzu sai ki yarda in aka ce miki na sake ki? Asiya tace dama ni banyarda ba tun da aka kawo sakin, saki uku kuma aka ce in nemi Uban dana kai ba cikinka bane. Takai karshen maganar tana kuka. Ya gungura motar gefen titi lokacin da ya fahimci mutane sun fara ce masa bari su tura masa ita ya tare hanya,a zaton su ta lalace ne.

Asiya taci gaba da fadin "Nafadawa Inna ba kai bane baza ka sake ni ba munyi alkawarin hakan,kuma yadda nayi Imani cewa ban kawo namiji daki na ba,haka na yi Imani cewa kai ma sharri ne. Shi ne su Inna suka ce kaina ya tabu wai na haukace,Ina ji ina gani aka dora min hauka. Dole na karba domin sun fini hujja, wannan damuwar ce ta hanani bacci na kwanaki ta hana ni ci da sha,domin gara in mutu bani da wani amfani ina raye kana raye bama tare. Ban san so ba kai ka koya min,ban san namiji ba kai ka sanar da ni,kai ne ka sa nasan cewa ni din mace ce kuma mai dauke da wata daraja da ni'ima da Allah ya bani ta Yaya zan barka. Halifa ya rungumo Asiya cikin wani irin yanayi ya ce 'Muje gidan su Inna yanzu in tabbatar mata da sharri ne ake binmu da shi ba ni ne na sake ki ba, Asiya hakika lokacin da na aure ki wallahi fushin zuciya ne ba wai son zuciya bane,amma da na zauna da ke sai na gane ashe da sha awa da kyale kyale ke ɗiba na, ke nake yi wa asalin so da kauna yanzu. Dan Allah muje in fadakar da su."

Asiya ta kai hannu ta shafi kumatun Halifa Kar muje yanzu domin Inna tana da matukar sauki amma kafin ta hau dokin naki,yanzu abu daya ne zai sa Inna ta yarda, shine aje mata da hujjar cewa baka sake ni ba,abin nufi sai ka nemo wanda ya shirya sakin iya maganar fatar baki baza ta wadatar ba. Sannan zaka iya yin abu daya,ka je a zuwan ka dawo daga tafiya kuma kaji labarin ɓata na, nasan maganar saki zata ta so sai ka fada mata ba kai bane,daga nan sai ta sanar da kai wanda ya kawo takardar ta haka zaka iya binciko ko wanene.

Halifa yace Allah ya min baiwa da ya bani ke, kina da basira. Yanzu bari muje gida sai mu kara tattauna yadda zamu bullowa lamarin.

Inna ta kalli Sadiya bayan sun dawo daga dan kara zagawa neman Asiya,tace nifa jikina yana bani Asiya ko gurin mijin nan nata ta gudu, ki leka shagon Sulaiman ki ce ina nemansa. Sadlya tace "Anya kuwa Inna, nafa tambayi Yaya Sulaiman din yace min ya yi tafiya amma bari na dubo miki shi.

Bayan sun gaisa Sulaiman ya ce Inna an samu wani labari ne? Inna tace 'Ko kadan,kawai dai wani zargi na ke yi game da mijin Asiya, kamar tana gunsa bayan ya yi mata sakin nan har uku,kasan ance Allah yasa jarabtar su da son macen da suka yi wa saki uku.ko ya jarrabe su shi da ita.'

Sulaiman yace Kai Inna ina shakka,domin a sanin da na yi wa Halifa ba zai yi hakan ba,shifa ba ma ya nan yana Dubai yace min dai zai dawo saboda faruwar wannan matsalar,kuma za a ganta insha Allahu zai kokarta. Inna tace To Allah ya sa a dace,dama wannan ne dalilin kiran. Saidai ya bar kokarin shi bana so,yaje ya samu wadda ta dace dashi zamu nemota da kan mu,indai addu'ar Mahaifiya tana aiki. Sulaiman yace Inna Allah dai ya sa mu dace.
Chapter 42 · 0% Book details