← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 62

Sashe 10

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*

[5/24, 10:05] Ummi Tandama😇: ____
Daga ni sai Baba a gidan Inna da Maman Annur sunje kasuwar kurmi za sai min tukwane da ɗan tsince tsince.
Ina hura gawayi zan dora taliya wadda Halifa ya sai mana ajiya, kamar yadda Inna ta barmin sallahu tunda yanzu na daina awara su kuma sai bayan biki za su ci gaba.

Cike nake da shauƙi da kuma nishadi nan da wasu kwanaki kadan ina gida na kuma zan ɗora girki nawa na kaina ba tare da wani ya bani Umarni yin abinda zan yi ba. Ko iya haka aure ni ima ne ba shakka. Allah kenan duk yadda ya so haka yake faruwa kamar yadda na kabari bai san cewa zai mutuba ya wayi gari ya ganshi an turbuda shi cikin kasa, haka ma wanda zai yi aure ko haihuwa sai dai mutum ya yi hasashe.

Fargaba takan darsu a zuciyata idan na tuna zan koma rayuwa ta har abada da mutanan da ban san su ba, ko sati ban yi da sanin abokin rayuwata ba amma ina yi masa kyakyawan zato.

Sallama ce ta katse Asiya daga tunani ta amsa tare mikewa tana yi musu sannu da zuwa, ba Wai dan ta san su ba, sai dan girmamawa.
Sai dai kuma kallon da taga baƙin suna yiwa ko ina na gidan nasu tare da yatsina fuska gami da taɓe baki shine abinda ya fi daure mata kai. Ba shakka waɗannan ba alkairi ya kawo su ba. Ta ɗarsa haka a zuciyar ta,. "Ina matar gidan?" Anty ta tambaya cikin daga murya da izgilanci. Bata nan Asiya ta bata amsa cike da tsoro. Anty tace "Ina amaryar da Halifa zai aura? " Asiya ta ji gabanta ya yi wata mummunan faduwa, ta sunkuyar da kai alamun kunya. Hafsi tace Innalillahi kar dai ke ce? Asiya ta kalli Hafsi ta kasa magana. Hafsi ta matso ta kama fuskar Asiya ta dago tace kalli Anty munshiga uku wannan ai bakwaini ce kalli ta, ta kama hannun Asiya ta saki kamar kara. Gaskiya dai Anty kiyi wani abu dan kuwa karshen abin fadi ne zai faru a zur"iar mu. Baba daga cikin daki ya yi karfin hali yace "Wai su waye ke magana?" Mu ne Anty ta amsa tare da nufar gurin tana cewa " Wai dama megidan yana nan?" Bakin ƙofa ta tsaya tare da toshe hanci " Wai ɗaɗɗaɗoya, ta fada tana duban Asiya. Ta ci gaba Baba zuwa nayi in bada sako a baka ashe ma kana gidan to hakan ya yi, Baba Kana ji? Ƙanina dai ba zai auri wannan yarinyar taka ba haka sai kace sullen kara, Haka a tsiyace, kwarya ta bi kwarya wannan ai matar yan dako ce. ba irin Halifa ba shi ba ajinta bane. " Baba yace Au haka ne? To ko ya makance ne lokacin da yazo yana neman a bashi ita? Ya cije lefe dan karfin Hali ya ci gaba da fadin, to kije ki ce da yaron ya zo da kansa ya ce ya fasa kamar yadda ya zo yace yana so, ko da kike uwarsa ce ba yayarsa ba. Ko kuma ki turo waliyyan sa, wannan yarinyar a yanzu matarsa ce domin na bashi.
Anty tace zanga kuwa yadda za a fara tusa ta hura wuta. Dole ka bashi mana kullum burin matsiyaci shine ya hada kafada da mai arziki. Na san ta inda zan biyo wannan auren bazai taba faruwa ba. Baba Yace Ko bana raye za a daura.
Ta dawo gaban Asiya "Ke kuma munafuka mai kama da muciya in har kika yarda kaddara ta kawo ki Auren Halifa zaki gwammaci kida da karatu.. Asiya jiki na bari tace Kuyi hakuri. Hafsi tace Ke in har kika shigo zuri armu Ba Anty ba ko ni sai na gallabi rayuwar ki. Ta yi gaba tana faɗin Anty waɗannan ba su kai kiyi cacar baki da su ba, ki zo muje ni amai nake ji ma.

Suna fita ta shiga gurin Baba da sauri tana fadin Baba Dan Allah a janye maganar Auren nan ni tsoro nake ji. Yace "Shigo Asiya," Ta shiga ta zauna tana kuka, ya ce "Share hawayen ki. Ta share, ya ci gaba da fadin, wannan shine ya nuna cewa akwai alkairi a cikin wannan Auren na ki, kin san dalilin?" Ya jeho mata tambaya. Ta girgiza kai. Yace " Duk abinda ya fara da ƙalubale ba shakka nasara ce ke biyo baya. Babu abinda hargaginta zai sa, ko ya hana dan haka ko Innar ku karki sake ki fada mata in su dawo, ki bar abin tsakaninmu." Asiya tace Saboda me Baba ai da ka bari na fada musu, wallahi duk na tsorata. Yace" Asiya alkairi ake fada ba sharri ba, ki zama mai fadin alkairi karki tada mata hankali,kinji ko yar albarka. Ki fara da shanye kalubalen ki, ki koyi aje sirrin miji ki a kirjinki ki yarda Allah shine mai maganin duk wata masifa. da haka zaki zama Jaruma ranar da ki ka rasa Innarki ko ni zaki iya daukan damuwar ki, Asiya tace to Baba bazan
fada mata ba insha Allah.

*** *** ***

Anty ta wuce gidan Baffa Halifa wannan shine karo na farko da taje gidan sa, domin tana mugun Jin haushinsa yadda suka saka lauyoyi a kan dukiyar Halifa in tana son wani abu dole sai Halifa ya saka hannu anbi wasu kaidojin banza, karshe ace aro ne, har sai in Halifa yace mata ya yafe. ita da kullum burinta yadda zata hau kan dukiyar ta barje gumin ta yadda take so. Taje America taje Dubai irin na wayayyun mata masu kafasiti da aji.
Bayan sun gaisa tace Baffan Halifa zuwa nayi a yiwa Halifa fada kuma a bashi shawara, gaskiya yanzu duk ya canza, baya saurarona ko wannan Auren da ya rungumo na waccan yar matsiyatan bai kamace shi ba, yarinyar bata ma da lafiya aljanu gare ta naje na bincika har unguwar sun rufe masa ne. Baffa Yace "Kin tabatta haka ne? Tace ko kaffara ba zanyi ba inna rantse. Ance su ke tsotseta in sun tashi kuwa hauka tuburan. Baffa yace" In maganar nan ta tabbata ba shakka basu kyauta ba sun yi abinda Manzo Rahma ya hana a yi, sun boye aibinta a neman aure. Amma In Dan su ba masu kudi bane wannan baya cikin sharadin da musulunci ya saka akan aure.
Anty tace shiyasa nace Bari inzo in fada maka tun wuri kar ayi aikin nadama. Yace "Ba damuwa zan kira shi a waya domin ya zo ya janye wannan maganar. Anty ta fashe da kuka tana fadin Na gode Baffa dama na san kai kadai ne zaka taimake ni in cika a amanar da mahaifiyarmu ta barmin.
Yace Dai na kuka ni ba zan barshi da kanshi ba, duk taurin kansa sai ya hakura. ai mu iyayensa ne, Anty ta bar gidan Baffa cike da kwarin gwiwa.

Asiya ta kalli wayar Halifa dake ringing shine yake kira, a sanyaye ta dauka muryarta can kasa ta gaishe shi. Yace " Amma dai kina lafiya?" Ta ce to lafiya lau.zance. Yace "Naji muryar ki wani iri bayan ba haka muka rabu ba." Tace An tsoratani ne Yaya, wai kana ganin idan. na zo gurinka da zama zan zama cikin aminci kuwa? Cikin mamaki
Yace "Zaki zama cikin aminci bana shakkar haka insha Allah." Ta sauke wata ajiyar zuciya mai karfi. Sai yanzu ta da ji sanyi a ranta. Yace wani Abu ya faru daga jin yadda ki ke magana sanar da ni. Asiya tace ya wuce ai tunda na samu tabbacin cewa barazana ce aka zo aka min. ina rokon ka kar ka ce sai ka matsa na fada maka. Yace "Shikenan zan dai kira ki anjima Baffa na ke kira bari na daga.

Bayan sun gaisa yace Umaru wai kuwa kayi bincike game da yarinyar nan da ka canza? Halifa yace sosai kuwa. Baffa yace ciwon hauka fa aka ce tana fama da shi. Halifa yace Baffa gaskiya da Sulaiman zai fada min Sannan ba abokin ka ne makoci su ba, ka buga masa waya domin ka samu tabbaci. Baffa ya yarda da haka.
Mamaki ya kama Halifa duk yadda aka yi wani Abu yana faruwa in ya auna kalaman Asiya da na Baffa. Da wannan tunanin ya kai gida. Yarinyar nan ya fara karo da ita bayan ya fito a mota wato Ma u tsigar jikinshi ya ji ta tashi, yace Auzubikalimati lahitammat min sharri ma kalaka. Take ya ji wata tsanarta a zuciyar shi. Ta nufo shi tana yanga tana fadin sannu da zuwa Yayana. Tsawa ya daka mata, karki sake ki karaso nan shedaniya. Ni bana son ko ganinki a rayuwata. Mamaki ya cika Ma u Mamanta ta bata tabbacin cewa yau dai Halifa ko dame yake takama sai ya rusuna kuma zai birkice yace sai an daura musu aure nan take kuma wata sha awar ta ce zata kama shi harma ya ji yana da bukatar saduwa da ita, in ya nemi hakan su amince, domin daga ranar kuma sai yadda suka yi da shi. To ya kuma abin ya fara da haka tafi awa tana wanka na magani ta jima tana kwalliya amma tana zuwa ga abinda ya biyo baya.
Chapter 10 · 0% Book details