Sashe 3
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Halifa ya shiga gidan cike da gajiya ga damuwar abinda Bilkisu ta yi masa, ya kalli bangaren Anty bazashi yanzu ba ta kara masa wani zafin bandaki ya fada ya sakar wa jikinsa shawa sanyin ruwan ya ratsa shi, Har ya ji kamar zazzabi zai rufe shi ya fito ya dauki jallabiyya ya zura, ya nufi gadon sa zai kwanta idanunsa suka sauka kan hoton Bilki wanda ya kafa shi domin sanyaya idanunsa a duk lokacin da ya kalla. Ya isa gurin hoton cikin rangaji ya sa hannu ya ciro. kalamanta suna kaikawo a zuciyar sa ya nufi kwandon shara zai saka ya yin da wasu hawayen takaici suka sulalo akan kumatun shi.
Kafadar shi ya ji an dafa lokaci guda kuma ta soma magana.
"Dan uwana ka bani zuwa gobe zan gyara komai tsakanin ka da Bilki tunda ka zubda hawaye a kanta lallai sai ta karbi hukunci, ina son ka auro ta kuma ka rama abinda ta yi maka."
Ya dubi Anty bai ji ko matsin ta ba bare takun ta,sai kalamanta da suka dirar masa. Ya sa hannu ya sauke nata hannun a Kafadar sa Sannan yace Kar kiji cewa kin damu Anty, bana bukatar cutar da ita, na gode da hasashe ki domin kadan ya rage inyi kitso da kwarkwata na samu madadin ta ina hasashen alkhairi ga sabuwar yarinyar da na kaiwa kaya kuma zai tabbata khairan insha Allah. Ya kai karshe maganar tare da zama bakin gado.
Anty tace "Halifa ina kasan wannan yarinyar mecece nasabarta, menene matakin karatunta, wace gogewa gare ta game da duniya, wacce yadda kai mata?"
Ya zame ya kwanta, tare da fadin duk ba sune a binda ya kamata in duba ga uwar 'ya'yana ba.
Ta kara matsowa" Halifa ka tashi muyi magana ban amince da wannan huce haushin da za ka yi ba, kai ba mijin kowace irin mace bace, kana da bukatar macen zamani yar gidan girma."
Ya tashi da sauri ya dauki makullin mota dake kan durowar gefen gado tare da fadin, zan nemi wani gurin in kwanta ko hotel haka dan ina son zafin da kaina ya dauka ya sauka ko zan samu bacci.
Da sauri ta nufi kofa dan tasan halinsa ficewa zai yi, tana fadin yi kwanciyar ka da safe zamu yi magana domin bazan laminta ba. Har ta kai kofa sai ta tuna sunan yarinyar tazo tambaya, dan Haka ta tako ta dawo, to "Wai ya sunan yarinyar ne ma? "
Cikin kagara yace ban rike ba Anty amma kamar Sadiya ko wa, ina ga kamar haka.
Tafice cikin sauri.
*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[5/24, 10:05] Ummi Tandama😇: *🧳 HASASHE🧳*
*Sabon littafin*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
*Page 3*
*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*
Daga sallar asuba Halifa ya wuce gidan Baffan sa Alhaji Ali wanda babu nisa mai yawa da gidan nasu, kanin mahaifin sane wanda shine ya rage masa Uba duk sai Yayinsa wanda suke uba daya a bangaren Mahaifinsa. Kamar yadda ya zata ya same shi yana karawa wa su dattijai karatu ya zauna gefe yana sauraro Har suka gama, ya sallame su, sannan ya dubi Halifa yace " Umaru kai ne da safe Haka?" Halifa yace ni ne Baffa, ya gaida shi cikin girmamawa sannan ya soma magana akan abinda ya kawo shi.
Baffa zuwa na yi in sanar da kai anjima kamar sha daya in ba wani uzri zamuje kai da Dady Mijin Anty gidan su yarinyar da zan aura. Baffa Ali ya dube shi.
" Lokacin daurin auran za a ɗaga ne, naga sai rana ita yau ne, koko wani abin ne ya taso?" Nan dai Halifa ya zayyane wa Baffansa komai game da matsalan su da gidan su Bilki da kuma canjin da aka samu na Asiya.
Baffa yace "Wannan dalilin ya sa yanzu maza ke kai lefe in da mazane ba za a tsaya wannan shirme ba, to sai muce Allah ya sa hakan shine alkairi sai mu tafi kamar shadayan ya yi."
A hanyar Halifa ta komawa gida ya kira mijin Anty a waya ya san lokacin basa tare da ita ya sanar da shi sha daya zasuje gidan surukansa.
Hafsi ta kawo masa karin kumallo bayan ta gaida shi tace " Anty tace tana jiranka" . Ya dan kurbi kunun kadan sannan ya ce ki fada mata sai na dawo tukunna.
Anty ta kalli Hafsi me yake yi to? Hafsi tace na dai same shi yana danna waya ne, ta mike bari ni inje. Ta same shi yana kokarin shiga wanka, ta kalli wayar shi da ke ta ringing ta ce, "Ka daga mana." Yace barta Bilkisu ce tun asubahin fari take kirana kuma ni na rufe shafin ta inna zauna ma zanyi blocking din number ta ne, gaba daya.
Anty tace "Haba Halifa, ka sawa zuciyar ka salama mana, yanzu ya ake ciki ne?" Ta yi maganar cikin sigar lallashi. Yace game da me kenan? Tace kajika, maganar yarinyar nan mana aikwai bukatar ka nutsu ka yi adduo'i kafin ka fadawa wata maganar auren. "
Halifa ya dube ta Anty a wannan karon gaskiya sai na yi aure, abin ya isa haka kadan ya rage in kai arba in, dubi Adam Bros nafa girme shi amma yaran shi biyu, auren kawai nake bukata da koma wacece indai sunan ta mace, an wuce gurin sai wance da sauran su. Anty tace "Kaji ka da zaka kawo batun Adam shi da ya yi gaggawar yanzu ina matar ba sai yaran ba, kuma hakan dadi ne? Matar sa fa zagina ta yi kasan komai nace kuma sai ya sake ta. Ta saki huci sannan ta danne zuciyar ta ta kuma tausasa murya. Ta ci gaba da fadin" Halifa ka san dai kai kanina ne maraya ne kuma amana a gurina, duk da ni na Haifi Adam wallahi na fi son ka akan shi, kai ne wanda na fara raino kafin shi, bana son abinda zai cutar da kai yin hakan cin amanar da mahaifiyar mu ta mutu ta bar min ne a tsumman goyo." Ta soma shashshekar kuka. Halifa ya numfasa. Karki damu Anty nima Kallon mahaifiya nake miki, nasan kina kokari a kai na. Ina son kiyarda da batun yarinyar nan ina yi mata Hasashen alkairi. Ta ce shike nan" Ina son ka kaini gidan su yarinyar in gani ko zan samu natsuwa. "
Yace shike nan. Ta fita tana fadin Allah ya yi albarka.
A fili ya furta Anty bazan kai ki ba hakuri kawai zakiyi.
Mijin Anty bai sanar da ita komai ba game da inda za suje domin tunjiya ta ke yi masa mitar abinda Halifa ya yi, shi kuma a nasa gurin yana kallon Halifa a matsayin wanda ya san kanshi kuma duk abinda Halifa zai yi yana da tabbacin abin nan yana kan daidai.