← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 62

Sashe 21

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da karfin gwiwa Asiya tace ke zance ki fadi tsakanin ki da ALLAH. Hafsi tace " "Humm kamar nasan zata musa na yi recording a wayata ta. Ta dakko wayar wadda ta zauna ta gama editing ta cire maganganun ta. Gaban Asiya ya fadi da ta ji yadda aka jera maganganun tiryan tiryan, ita kanta banda ta san yadda suka yi ita da kanta da sai tace tabbas haka ne. Halifa ya cika da mamaki ya kalli Asiya a fuskar shi ta ga Bacin rai karara. "Me kuma zaki fada yanzu? Asiya ta ce bani dashi domin ko na fada bazaka yarda ba tun da na riga nayi karya tun a farko nace ba ayi ba.

Gaskiya dai tazo kuma duk maganganun na da ta dauka amsar magaganunta ne, da ta fada min inda za a sake kunnawa tsaf zan fidda yadda zantukan suka faru a tsakanin mu. Anty ta amshe, da fadin ni dai abar maganar kawai ke Asiya ki daina gorin aure ga budurwa komai lokaci ne. Ke kuma kiyi hakuri. Ta kallo Halifa wanda har lokacin bai ce komai ba ka rinƙa yi mata faɗa duk da cewa harda kuruciya. Halifa ya Ja tsaki yace wace kuruciya a nan. Ya juya.

Asiya ta kalli Hafsi sannan ta kalli Anty tace Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Ta wuce tabarsu suna dariya, basu san wannan addu ar da ta yi ta ce Allah ya isar mata komai babbar magana ba ce.

Kamar yadda ta zata Halifa ya bude daki ya shiga, ranta ya sosu, kenan sun fasa fitar, ta daure ta cije domin dai fushin fari ba nata bane. Ya yi matukar bata rai yana zaune akan kujera. Ta kwantar da hankalin ta kafin ta ce Yaya munfasa zuwa duba su Innar tamu ne? Tun kafin ta rufe baki ya ce, na fasa. Asiya. tace saboda me? Ya dube ta cikin daga murya "Kina ganin cewa abinda ki ka yi ba laifi bane ke nan? Asiya kin bani mamaki kin iya karya har haka? Ina son ki sani duk duniya na tsani karya, duk lokacin da mutum ya zama makaryaci a idona darajar shi zubewa ta ke yi, yanzu fa ba wata magana da zaki fada min inji cewa gaskiya ne ko da kuwa gaskiya ce sai na tsaya kokwanto. Sai yanzu Asiya ta gano illar da suka yi mata. Ta kwantar da muryar ka yi hakuri, na yarda cewa na yi karya, kuma karyar cewa duk yau banga Hafsi ba iya itace laifina na zabi in faɗi haka saboda kawo karshen rigimar da tazo har daki ta takale ni da ita.

Yace Malama yi min shiru, me ya hana ki fada tun a lokacin gaban kowa, ina son ki sani a duk yadda Duniya ta rikice miki ko rayuwa ta riske ki kar ki taba daukar karya wai ta zame miki mafita. Kirike wannan domin bazan sake maimaita shi ba. Asiya ta lumshe ido hawaye suka kwaranyo cike da nutsuwa tace na rike kuma insha Allaahu bazan sake yi maka karya ba, ta silalo kasa ta zube gwaiwa biyu a gaban sa cikin sanyi murya tace natuba.

Halifa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya yi mata alama da hannu wai ta tashi. Ta mike ta nufi cikin dakinta tana kuka yanzu kam ta tabbatar yaki dan zamba ne kuma dole ta kara sanin da suwa take zaune.

Anty ta saka dariya bayan Nur tace Anty naji Uncle yana ta yi wa Amarya fada tana kuka shine ban shiga ba na dawo dama kince in naji yana fada in dawo. Anty tace jeki kuyi kallon ku kin gama aikin ki. Dama ta tura tane wai ta amso mata chajar waya amma in taji Uncle Halifa yana fada to ta dawo. Sako ya fado wayarta ta dauka ta duba Hajiya Talatu ce. A fili tace lalatacciya har na manta da rayuwar ki, sakon uban me kika turo min in bashi ki ke nema dai bani da shi.

"" Ki duba whatsapp din ki. " Abinda aka rubuta Kenan, bata iya magana ba sai dai ta wuce kai tsaye zuwa whatsapp din nata. Odiyo ne Ta kunna wayar su da Malam ne tiryan tiryan kafin Anty ta gama saurara zufa ta rufe ta, sannan ta tsine wa Hajiya Talatu babu Adadi.

Ta danna kiran Hajiya Talatu cike da karfin hali tace, Talatu manya, to wannan Odiyo din da kika turo min me zai amfane ni da shi? Talatu ta yi yar Dariya. "Kawata ta kaina, ke kuwa zai amfana da zarar angoge shi, amma in aka tura musamman ga Halifa ko da bana nan nasan kin aiwatar da abinda kika yi kuduri, daga nan sai asirin ya tonu." Anty ta zaro ido amma sai ta cije tace. Ba shakka na cika kuduri na, amma ki sani shi kanshi Halifa ko yaji wannan babu abinda zai iya, domin na samu damar juya shi a yanzu haka.

Hajiya Talatu ta danyi shiru cikin sanyin jiki, jin haka sai Anty ta san cewa karyarta ta samu shiga dan haka cike da kwarin gwiwa ta ce. Amma zaki iya tura masa din ki gwada ki gani. Talatu kin bani mamaki shiyasa naki kai ki gidan malamin tunda na fahimci da sharri kika zo min gida. Kuma duk abinda kike ciki wannan malamin yana sanar dani hatta wannan kuduri naki, da wannan Wayar da zamu yi duk ya fada min. Kuma ni da na so zan saka ya cutar da ku ke da Ma'u din amma nace masa zan sake baki lokaci ko zaki nemi yafiya ta.

Talatu ta tsorata matuka Tace "Sahiba to duk ba wani abu bane, kawai dai ina son Halifa ya auri Ma'u ne, duk kan haka ne na miki rakodin kuma da zan tura mishi ai da tuni na tura. Anty ta yi dariyar samun nasara, tace Talatu baki gama sanina ba har yanzu, ni yanzu jini nake ba aljanu suna kawo min bayanai yanzu haka sunce min maganar da muke yi dake kin sake kunna rakodin to ina gargaɗin ki, zanyi hadaya dake matsawar baki goge duk wadannan Odiyo din ba, zan basu jinin ki ba ruwana. Hajiya Talatu jiki ya soma rawa domin ta danna din dan samun wasu bayanan. Ta kashe wayar Tana mamakin Anty gaskiya ta zama abin tsoro dole ne ta goge su. "

Anty kuwa ta shiga tintsira dariya tana cewa Kai gaskiya barazana ta yi, da na tsaya rokonta da yanzu tana nan zata hada min jangwal. Da Hafsi ta dawo take bata labarin abinda ya faru suna ta dariya.

Kiran Hajiya Talatu ya shigo. Hafsi tace Anty kar ki daga sai a kira na uku dan tasan abinda gaske ne, kuma in tace ta goge sai kice Aljanun sunce saura daya ne bata goge ba, kinga in ta makale wani zata kara gaskata hakan kuma zata goge, in kuma ta yi ta rantsuwa akan ta goge sai kice mata dayan shine wanda ta turo miki ta goge shi da kanta.

Anty tace kai gaskiya kin haifu Hafsi ina ma ace haka yayanku yake, da yaushe zan sha wahala.

Haka kuwa suka yi wa Hajiya Talatu kuma ba shakka lissafin ya tafi yadda Hafsi ta tsara.

Cikin bacci Asiya taji Halifa yana lalubarta, duk da cewa harta kwanta yana fushi da ita hakan bai hana ta bashi hakkinsa ba, ya kunna wuta ya kalli fuskarta, ya kai hannu ya shafi busassun hawayenta kina yawan kuka sai dai nafi son irin wanda kike yi din nan idan mun kasance tare. Ina jin dadin da farin ciki. Asiya ta rufe fuska ita fa batasan tana wani kuka da yake yawan fada mata ba.

Zuwa da safe kamar babu wani abu da ya faru na fitina tsakanin su. Ya dai kara yi mara nasiha akan karya, yace "Bana son karya sam sam kuma bana zama inuwa daya da me yinta. Asiya tace zan kiyaye nima ba ɗabi ata bace.

Tace to ya kira Yaya Sulaiman ya kai waya gidan su, sai yace ta bari da dare zasuje.

Anty ta cika da mamakin ganin Halifa sun sake zuwa sallama kamar dai jiya. Dole ta wage baki tana yake tare da fadin ki gaida Innar taku, sannan Halifa kar aje hannu rabbana. Yace "ai dama."
Sahat suka fara zuwa kayan abinci ya saiwa su inna sannan suka wuce. Murna Asiya ba a magana Inna ta kara yi mata nasiha da shawarwari, sannan suka tafi.

Kwana biyu tsakani Asiya ta shiga gaida Anty sai tace mata anjima masu allurar riga kafi za su zo, za a yi ta annobar sankarau saboda zuwan zafi. Asiya ta tsorata dan ita bata son allura sam. Tace Ni kam ba sai anyi min ba. Anty tace ai kuwa yi ya zama dole domin bazan bari ki kamu da cuta ki yada mana ba.

Da rana da ya dawo take fadawa Halifa ita bata son allura. Yace Anty ta faɗa min tun jiya wai za ayi riga kafi ki hakura a yi miki don bana son magana yanzu Sai wannan karamin abun ya zama issue.

" Asiya tace shike nan.
Tana bacci aka tashe ta ake faɗa mata ga me allura. Tayi mamakin ganin an tsaga mata hannu an saka wani abu an like. Ta sha kuka sosai domin azaba da kuma rasa ko me aka sa mata. Halifa ya yi mamakin ganin yadda gurin allura ya yi tsagu, da ya yi wa Anty magana wai ita ce Taki tsayawa shine ya sa har aka karce ta.

Bayan kwana biyu sai jini ya balle wa Asiya wanda bata san kanshi ba. Ta zaci lokacin al adarta ne ya canza. Tun abin baya damunta har ta shiga tsoro. Halifa kuma ya shiga takura, saboda jini yafi sati kuma sai ya dawo kwana biyu uku da daukewa sai ya kuma dawowa. Halifa ya samu Anty ya fada mata. Tace Aljanu ke yin haka, an fada maka yarinyar nan Aljanu ne suka aureta amma ka ki yarda.gashi sun nuna kansu gidan magani kawai za a kai ta. Hankalin Halifa ya tashi sosai, kuma ya amince da suje gidan magani. Asiya tace masa bata da komai ita babu gidan maganin da zataje. Hakan ya kawo musu matsala wadda ta sa Halifan Kauracewa gadon su.
Chapter 21 · 0% Book details