Sashe 22
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A kasuwa yake fadawa wani abokinsa abinda ke faruwa da matarsa, yace gaskiya ana samun haka shima wata kanwar su budurwa haka aljanu suke sakar mata jini. Halifa ya sake yarda dan haka yace lallai Asiya ta shirya Anty ta kai ta gidan magani.
Farin ciki ya cika Anty domin malamin nan ne ya bukaci ta kawo masa Asiya zai yi mata wani wanka wanda zai wanke abinda ya sa aljanun ba su yarda sun karbeta a waccan ranar ba, wato da suka ce ba budurwa bace. Sun bincika sosai ba su samu mai irin tauraro ta ba....
*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*
*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[6/28, 21:44] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w/9223372036854675807
Tace masa sha biyu za su fita dan haka ya basu kudin kekenapep ya bawa Anty kudi yace su dauki shatar abin hawa kuma duk yadda ake ciki su kira shi. Ƙala Asiya bata ce ba lokacin da zai fita ya kalleta yace "Kiyi hakuri baby gaskiya dole ayi maganin wannan ciwo yana shiga hakkina da yawa yanzu yau kwana nawa rabon mu da ke? Ta kalle shi, me yasa baka yi tunanin mu fara zuwa Asibiti likita ya tabbatar ciwon ba? Na yi mamaki yadda ka ke ahalissuna kuma ka yarda a kaini gurin yan tsibbu masu amfani da aljanu. Yaya Halifa bani da kowa a kaina ban taba ko mummunan mafarki ba, to yawanci masu bada maganin nan wallahi ance suna lalata da yaya da kuma matan mutane yanzu kai ka yarda a kaini wani ba kai ba ya kwanta da ni? Ta kai karshen maganar tana kuka.
Halifa ya ji wani abu ya soki zuciyar shi yace amma ai Anty ba irin gurin zata kai ki ba, Anty bata hulda da masu zuwa irin wannan gurin. Asiya ta yi shiru tana tunanin dole fa ta sa Halifa ya janye zuwanta gurin wannan maganin. Babbar matsalar shine Halifa bai san wacece Anty ba.
Ta sau ke ajiyar zuciya cike da kwanciyar zuciya tace. Zanfi yarda muje tare da kai a yi komai a gaban ka kokuma yanzu muje Asibiti muga likita ya tabbatar mana da matsalar bata su bace,, domin nifa tundaga wannan ranar da aka min allurar riga kafi komai nawa ya canza ina zargin likitan bai yi abinda Anty ta saka shi ba. Halifa yace "Kin tabbatar tun daga ranar ne kika fara samun canji? "
Asiya tace gaskiya haka ne. Halifa yace me ya sa baki fada min ba? Bari in yi magana da Anty. " Asiya tace Yaya kar ka fadawa Anty domin zata ga kamar munki shawarar ta ko taji babu dadi akan ita ta kawo me allurar aka samu matsala. Inda zaka yarda kawai mu tafi in mun dawo sai mu fada mata, in kuma likitan yace ba na Asibiti bane shike nan sai mu yi shiru. To muje ya fada ya na daukar wayar shi akan kujera. Hijab Asiya ta saka suka fice.
Likita ya kalli Asiya "Baki yi makaranta bane?" Asiya tace nayi makaranta amma bangama ba. Ya kalli Halifa wannan gurin ba allurar riga kafi bane, tsinke aka sa mata na tsarin iyali wato tazarar haihuwa,, tana me bata sani ba? Halifa yace likita wallahi ta fada min cewa kamar an saka mata wani abu amma sai aka ce min taki tsayawa ne ayi mata allurar kuma dama tun farko ta nuna cewa tana jin tsoron allurar dan haka sai kawai na yarda da abinda Antyna ta fada.
Likita yace gaskiya babu wani kuskure wannan abin ana sane aka yi shi dan karta haihu. mamaki ya cika Halifa yana kokwanto cewa anya Anty tana sani zata yi haka. Likita ya kira nurse ta cire mata abin Halifa ya kalla yace tabbas wannan babu kuskure daga cewa yi allura sai kawai mutum ya saka wannan. Ya dai yi godiya tare da tambayar jini ko zai daidaita. Likita yace zai daidaita insha Allah.
Asiya ta lura da yanayin da Halifa ya shiga na tashin hankali yana ta maimaita me ke nan Anty ta yi? Ta sanyaya muryar tace, kar ka zargi Anty fa babu mamaki laifin shi mai allurar ne. Halifa ya sauke ajiyar zuciya yace ina fatan ya zama haka, dan zaifi yi min sauki a bisa a ce wai Anty da nake mata kallon mahaifiyata nake mata kauna irin ta ɗa da mahaifiya, ace tana da hannu a yunkurin hana ni samun ɗa.
Ga mamakin Asiya sai taga hawaye sun kwaranyo daga idanunsa. A firgice Asiya tace ka samu guri ka dan tsaya dan Allah. Kamar mai kar ɓar umarnin ta sai ya tsaya cak. Sannan ya yi gefe. Asiya ta matsa ta rungume shi, kamar hakan yake bukata sai shima ya rungume ta tsam sai kuma ya saki kuka. Asiya bata hana Shiba har kusan minti daya sannan ta fara fadin "Ya isa haka Yaya, ka yi hakuri dan Allah insha Allah ba ruwan Anty, ni da zaka yarda ma da sai mu yi shiru mubar maganar kawai kace mata gurin wani maganin mukaje shike nan. muryar Halifa a dashe yace" Kinsan matsalata daya da zarar na zargi abu in har na cika bibiya sai ya zama gaskiya.
Asiya tace ka yi hakuri insha Allah ba haka bane.
Sun iso gida suka samu Anty tana ta faɗa. Halifa ya kalleta cike da zargi lokacin da take cewa "Sakar cin banza kawai banda shashanci sai ku fice bayan kun san zamu fita, ba sai ku bari sai mun dawo ba. Halifa ya yi karfin halin cewa mun samu magani a Asibiti yanzu da muka je.
A firgice Anty ta ce," Asibiti kuma bafa ciwo Asibiti bane". Halifa yace tsinken da kika sa a saka mata ne aka cire. Ta dau salati wane tsinke kuma ni Habi. Halifa yace Na allurar riga kafi mana wanda aka ce min karcewa ta yi. Anty ta dauki salati ta sallame. Ta dakko waya tana fadin sai na sa an daure dakta din nan, tsarin iyali kuma yaya ya yi haka ne. Ta kira ya daga ta saka a free. Tace kai "Dakta dama haka Na fada maka daga allurar riga kafi kuma sai ka saka mata tsarin iyali? Yace Hajiya dan Allah kiyi hakuri, ranar gida biyu zani da nan gurin ku da wani gidan wancan gidan suma ni ke duba su. Mijinta ya kira ni ya fada min inje in saka mata wannan tsinke to kuma nima ina fama da matsalar mura a ranar sai na saka mata sai da naje wancan gidan sannan na gane abinda na yi.
Halifa ya fisge wayar tare da fadin To amma kai jahilin ina ne da zaka sawa matar wani abin tsarin iyali, ina son ka sani daga yau ka daina domin sai na shigar da korafin ka a hukumar lafiya ya kamata su bincika lasisinka. Sai an dakatar da kai. Anfy ta karba tace dole kuwa mu kai kararsa. Bani wayar in kira masa yan Sanda.
Halifa yace "Anty ai wannan ba karamar matsala bace ni zai tsarawa yayan da zan haifa, ni da ubana yake da yaya sama da talatin kuma sai na gaje shi. Bazan taba kyale shi ba ko waye ma ya turo shi sai ya fada, domin yadda nake ji zan iya kashe mutum ko waye shi. Ya nufi dakin sa a fusace.
Asiya Ta kalli Anty sai tsuma take tana zufa tana fadin ina bayan ka wallahi karka yarda zan kaika har gidansa. Asiya ta girgiza kai tare da fadin Allah ya kyauta.
A ban daki ta samu Halifa ya sakarwa jikin shi shawa ko single da gajeran wando bai cire ba. Ta aje hijabin taje ta shige jikinsa ita ma da kayan jikinta. Kam ya rungume ta ruwan yana ratsa su, tsawon minti hudu sannan ta ce muje ka kwanta. Baya shige umarnin ta suka kwanta tana shafa masa baya har bacci ya dauke shi. Asiya ta zame a hankali taje kicin tana girki. Anty ta aiko wai taje.
Ta samu Anty a falo. Tace "Kije ki shirya mu tafi gurin magani ba biye tashi za ayi ba, lafiyar ki ce. da kin lalace wata zai auri" Asiya tace Anty kiyi hakuri kawai in ya huce sai ki tambaye shi, yana cike da tashin hankali. Anty ta mike tana magana cikin lallashi, ki daure muje banda shirmen ki harna mallaka ba sai ki samo ba namiji fa ba dan goyo bane dan yana nawa bazan ƙi ki ba. Asiya ta juya tare da fadin Na tuna na saka mai a wuta Anty, zan dawo.
Hankalin Anty ya gama tashi, ko da wasa ta san Halifa bazai taba yarda ya bar Asiya Zuwa gurin Malam ba. Ta kira Malam din ta sanar da shi halin da ake ciki. Yace Wannan kuma ke ta shafa ba ni ba. Anty sai kai da kawo take a falo. akwai bukatar ta samu mafita cikin gaggawa.
Halifa ya dawo sallar azahar ya ci abinci sannan ya ce zai tafi kasuwa. Asiya tace Anty tace min ko zamu je gidan magani ɗin, ni kuma dai nace insha Allah ai ciwon ya warke ko? Yace babu inda zaki je zan ma fada mata dan ta sani. Asiya ta rakashi ya tafi.
Anty ta na ganin fitarsa ta kira Malam tace "Dan Allah Malam ka zo ka yi mata wankan a gidan nan mijin ya fita baya nan sai dare zai dawo. Malam wanda ke cike da tashin hankali tun bayan da ya ji cewa a hakan ma yarinyar bazata samu ba. Sai da ya bi matakai ya bi sharudda ya yi hadaya sannan aljanun suka kawo wannan hanyar. Ko me zai faru kam dole ne yaje gidan.
Yace kin tabbatar ba wata matsala? Anty tace ba matsa ka taho kawai.