← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 62

Sashe 26

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asiya ta ga har ankai sati amma Hailfa bai kara batun tariya ba, ita kuma tana son yi masa maganar amma tana tunani. Ta daure tace Yaya wai kuwa ya batun tarewar mu tunda naga jikin Anty da sauki. Yace Anty ta sameni taroke ni akan wai in taimaka in hakura da tashi zuwa gaba kadan. Sannan ta bani hakuri akan kayan ki na lefe wai ta taba. Duk da banji dadin abin ba, amma dai bani da yadda zan yi tunda matsayin Uwa ta ke. a guri na. Dole in yi hakuri da wasu abubuwan dan haka kar ki damu mu bata lokaci insha Allah komai zai zama daidai. Duk da Asiya bata ji dadin abinda ya faru ba amma bata nuna komai ba, cike da fara a, take fadawa Halifa Allah Sarki Anty tana kaunar ka shiyasa ta haka. Dan ma kaine ka damu mu koma can amma ni gwara nan din da motsin mutane. Halifa cike da jin dadi yace Allah ya yi miki albarka wallahi har ina tsoron ta ina zan fara magana.

Asiya tace 'Haba Yayana nifa abin ikon ka ce, umarni kawai zaka bani a kan komai. Ya kama hannuwanta shi yasa nake kara son ki. Anty ta yarda aikin Malam ne ya ci. Dan haka ta kuma wankar jiki ta kuma zuwa gunsa da wasu bukatun tace Tana son a yi wani a bu tsakanin Halifa da matarsa wanda zai hana su zaman lafiya domin bata son ace matar Halifa ta haihu ya samu mai gadon abinda ya mallaka,Malam yaron yana da dukiya da shi kanshi saidai ya yi kiyasi kuma gashi da nasibi, dan abinda aka tsakura mishi a kudin sa yanzu ya ninka yafi sau dari. Ni dana sha wahalar shi har yanzu banda komai in matar shi ta haihu. Malma yace Kash da kin zo nan kafin bikin nashi kika zo da ko auren ma ba zai taba yi ba. Kinga yana mutuwa kin tabbata ke ce mai gadon sa." Anty taja tsaki tace ai lokacin ban San nan ba. Amma yanzu ma in dai da yadda za'ayi a toshe mahaifar ta kar ma ta dauki ciki bare ta haife shi. Ina da burika game da Halifa sosai.

Malam ya mata Alkawarin matsa war da kudi magana ta kare.

Asiya ta kara so falon da gudu tana ihu,. Anty ta taso a gigice tana cewa waye meye! Gadangare ne ya biyo ni Anty ta ja tsaki tana fadin meye abin gudu a kadangare? Asiya harda shidewa Dan tsoro. Tace "Wallahi Anty sam ni bana son kadangare ina tsoron sa sosai.
Bayan fitar Asiya take Anty ta kira Wayar Malamin tana sanar dashi cewa Allah ya saukaka mata yarinyar nan kadangare ke firgita ta. Malam yace sa kudin aiki yau gidan ba za a kwana lafiya ba.

Cikin bacci Asiya ta shiga firgita tana tsorata domin farkawa tayi taji ta a jikin Halifa ya rumgume ta gam yana tofa mata addu'o'i ta kalleshi ta hada zufa sharkaf sai ta sake kankame shi. Yace kinyi bacci babu addu'a ko? A wahalce tace na yi adduo'in dana saba kawai dai jiya ne wani kadangare ya biyo ni dama ina tsoron sa, sosai. shi ne nayi mafarkin sa yana ta bina. Halifa yace "Shiya sa cikin baccin naji kina nishi kina karanta addua, to kar ki damu ki canza yanayin kwanciyar ki sai ki sake yin adduo'in,ta yi yadda yace shima ya tofa mata, saidai kuma da bacci ya soma fizgarta zata ga kadangaru bakake sun cika mata kan gado sai ta farka a gigice. Haka suka kwana. Da safe yake fadawa Anty Halin da ake ciki ta yi murna sosai amma sai ta boye ta jajanta tace "To Halifa me zan muku baya ga addu'a ance tana da jinnu kunce ba haka ba, Na kawo mai magani ta masa sharri ka hau kai ka zauna, yanzu kam ai sai dai ku nemi magani da kanku ko ka sanar da iyayen ta. Halifa dai ya mike ya koma ya samu Asiya zazzabi ya rufe ta sai rawar sanyi take yi. Ya rasa ina zai saka kan sa yace tashi ki sa hijabi mu tafi Asibiti.
Halifa ya yi wa likitan baya ni game da yadda suka kwana da kuma yadda take fama da zazzabi. Likitan ya tambayi Asiya ta sanar da shi yadda abin ya faru. Yace "Ta tsorata ne sosai, saboda tana jin tsoron kadangare duk da ni ba likitan kwakwalwa bane amma ina da wata yar masaniya kasan, kasan Ita kwakwalwa kamar kwamfiyuta take in ta Karbi abu ba a cikin shiri da tsaro ba sai ta birkice ta yi ta abubuwa ba daidai ba. To itama abin ya zo mata ba zato ta tsorata da yawa ne ba komai da ta samu bacci komai zai zama daidai. Sai dai shi zazzabin ta yuwu rashin bacci ne ko maleriya bari a yi mata gwaji mugani. Kusan gwaji kala uku likitan ya sa aka yi mata. Bayan kawo sakamakon ya tabbata akwai malaria likitan yace to ko wannan maleriya ta isa ta saka ta yin abinda yafi haka. Sannan ya duba daya sakamakon yace saukin ta kuma ba taifot. Ya kalli dayar yace ko wannan ma zai iya saka komai dama tana dauke da ciki ne?
Halifa ya mike tsaye da sauri, tare da fadin me kace likita. Yace tana dauke da ciki karami Dan sati biyu. Sai kawai suka ga Halifa ya zube a tsakiyar ofishin ya yi sujjada yana fadin Allahu Akbar. Ya Mike ya rungume likitan yana fadin likita na gode da wannan albushirin naka. Ka dai tabbatar ko? Gani nake yi kamar a cikin mafarki.
Likitan yana dariya yana Dan buga ka fadar Halifa yace ko shakka babu mutumina matar ka tana dauke da ciki kamar yadda yake a rububuce. Halifa yace ina mamaki Wai ni ne na yi ciki ya Allah ya juya gurin Asiya wadda kunyar kalaman da Halifa ke furtawa suka sa ta sunjuyar da Kai. Ya rungume ta yana fadin ina kaunar ki maman yarinyata. Ya kalli likitan mace ce ko. Cike da dariya likitan yace "Sai dai in kunje hoto za a fada muku,suma sai ya dan kara kwari. Halifa ya saka hannu a aljihunsa ya ciro kudin dake ciki bai kirga ba ya mikawa likitan Ba yawa goron albishir ne, ina son ka rubuta abinda ya kama ta ci Sannan ka fada mata dokoki kaga yarinya ce karama kar ta yi ganganci. " Likita ya sa dariya yace ba komai zata iya Allah da ya bata shine zai bata kariya da danta. Halifa yace ka gama magana Allah ya baka lada. Tamkar ya yi wa Asiya tafiya haka ya ruko ta, yana fadin ko in dauke ki? Asiya kuwa ji ta yi karfi ya zo mata tama daina jin komai tunda likitan ya ambaci ciki. Tace "Yaya kana sani jin kunya sosai ka sake ni zan iya tafiya." Duk da haka ya rike mata Hannu duk kunya ta ishe ta cikin mutane, Haka suka ratso har mota. Ya bude mata ta Shiga ta zauna ya rufe ya zagayo cike da farin ciki ya bude gefen shi ya shiga. Ya kallo Asiya wadda take jin ranar yau ta musamman ce a gurinta. Yace " Ina son ki sosai Asiya ya kai hannu ya daga hijabin ta ya zura hannu ya shinfida a cikin ta yace Yanzu dai dana yana kwance a nan ko? To ya naji be yi girma ba? Asiya tace to duka baka ji ance sati biyu ba?
Halifa ya dauki waya ya fara danna number dole in fara yi wa Anty albishir sai dai wayar Anty Busy. ya kira Mijin Anty ya fada mishi, ban sha mamaki ba sai da naga ya kira Baffa. Nace Yaya yanzu kuma sai ka fada mishi? Sosai ma zan fada mishi kuwa ai abokin kuka shi ake fadawa mutuwa. Haka dai ya yi ta kiran abokai da yan uwansa. Yace bari dai zan kira Sulaiman ya kaiwa su Inna waya sai ki fada musu. Asiya tace kunya zanji sosai ka bari a hankali sai in fada musu ko sugani. "Anty har yanzu tana waya, ya fada cike da haushi bayan ya sake kiran ta. Ya kira layin Hafsi ta daga yace kina gida ko"? Tace ina gida. Ya ce ki kaima Anty wayar akwai abinda ya kamata ace ita ce farkon ji yanzu za ta zama itace karshe. Hafsi tace menene ya faru Uncle? Yace Anty zata fada miki.
Ta shiga gurin Anty daidai lokacin da take fadawa Malaminta cewa ga shi nan ta turo masa kudin aikin daure mahaifar Asiya. Hafcy ta mika wa Anty wayar tare da fadin Uncle zai miki albishir. Anty ta amsa tare da fadin ya wuce kaya sunyi riba oder ta yi kyau. Daidai lokacin ya sake kira. Ta daga yace "Anty albishir mai dadi." Tace miliyan nawa aka samu? Ciike da jin dadi yace Anty girman lamarin nan yafi batun kudi. Zan zama Baba kyautar Dan mutum Allah ya bani sati uku kenan.....

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*

*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[7/22, 21:10] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w

*🔉 NASIHOHIN MALAMAI🔉*

*ADDU'O'I MASU MAHIMMANCI. Vol 2👇🏼*

1️⃣ *Addu'ar da ake yi domin ganewa da fahimta da hadda, haka nan gurin warkar da in ina. Wannan ce addu'ar da Annabi Musa,Aminci Allah ya tabbata a gareshi ya yi lokacin da aka umarce shi da ya tafi wajen Fir'auna*. Alƙur'ani sura ta 20 aya ta 25-28

رَبِّ اشْرَحْ لِي صَدْرِي، وَيَسِّرْ لِي أَمْرِي، وَاحْلُلْ عُقْدَةً مِّن لِّسَانِي، يَفْقَهُوا قَوْلِي

Rabbi ishrah li sadri, wa yassir li amri, wahlul 'uqdatan min lisani, yafqahu qawli.
_Al-Qur’ani, Surah Taha._
Chapter 26 · 0% Book details