← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 62

Sashe 47

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kunun gyada ta yi musu da kosai kamar yadda Asiya ta fada mata tun jiya,sai dai ta kara da farfesun kayan ciki wanda Halifa ya samu ya yi ta sha da alamu ya yi masa dadi. Domin magana ta gaskiya ya yi dadin kuma Fati ta iya girki. Haka ranar da ta yi miyar kubewa Halifa bai boye santin shi ba. Sannan ko shayi mara madara sai yace kisa yarinyar nan ta dafo min shayi. Asiya ta fara jin haushin Fati to amma sai ta lallashi zuciyar ta domin kuwa fushin fari ba nata bane. Za dai ta dauki mataki ne. Fati ta fito bayan ta gama gyara dakin har lokacin suna kan Dining yana fada mata zai je gidan yarine ziyarar wani dan kasuwar su. Asiya ta daga murya ta kira Fati. Fati ta zo gurin tana satar kallon Halifa wanda ya ki dago kai,yana danna waya. Asiya tace Fati da Allah in zaki zo gidan nan daga yau kar ki kara saka wannan turaren. Cike da mamaki Fati ta kalleta "Saboda me Anty?" Asiya ta kalli Halifa, saboda Yaya yace baya son kamshin yana tada masa zuciya. Fati tace To insha Allah ba zan sake sakawa ba,ta kalli Halifa wanda kunya da mamaki suka hana shi ya dago kai. Tace "Alhaji a gafarce ni bazan sake ba. Halifa ya dago ya dube ta, kar ki damu. Abinda ya iya furtawa ke nan ta juya ya bita da kallo,reshen zuciyar sa yana kawata masa surarta, sai ya sunkuyar da kai. Tana fita Hajjo na sallama. Suka mike a tare Asiya ta saba Danta a kafada suka nufi falon Hajjo ta amshe shi suna gaisawa. Halifa ya nufi daki bayan sun gaisa Asiya ma ta nufi dakin dan dakko wa Jariri kayan da za a sa masa in anyi wanka. Halifa yana bakin gado yace "Ke zonan ki fada min yaushe kika soma karya da kulla sharri? Asiya tace bari in bawa Hajjo kaya inzo in fada maka.

Ta maida kofa ta kulle sannan ta zo ta same shi, ta zauna a cinyarsa. Da me kake tambaya? Ya kama kunnenta ya matsa har ta yi dan kara,yaushe ki ka soma karya? Tace yau na fara, kuma akan ka bazan daina ba. Ta haye kirjin shi bayan ta tura shi ya kwanta ta rike masa kunne tana fadin kar ka sake ka kara cewa turaren wata da dadi, nawa kadai zaka yaba kaji ko? Yace "Ai ban fada mata ba fa ke na fadawa." Tace shine saukin ai. Ta soma yi masa wasu wasanni da ya fara neman rasa nutsuwar shi, yace Kar ki haukata ni Baby ke gashi kina cikin wani yanayi da sai hakuri. Tace Ai tunda ka fara kwadayin aure ka daina fita ba nutsuwa. Zan gwada maka banbancin mai mace daya da gwauron da ka ke fada. Haka kuwa da wasanni saida ta sa shi ya nutsu, yace lallai yarinya ashe kinsan yadda zaki yi dani in kina fashin salla amma kike kyale ni ? Tana ta dariya, sannan ya yi wanka ya fita zuwa Gidan Yari.

Anty ta kira Hajiya Talatu yafi a kirga bata same ta ba, layinta ma baya shiga,tun ranar da tijararren nan ya kwashe mata kaya. Amma yau sai ga kiran Hajiya Talatu, cike da mamaki Anty ta daga, ta soma zazzaga masifa Lallai Talatu kin nuna min ke cinnaka ce baki san na gida ba. Ni zaki cuta shiyasa ina ta kiran ki amma ki ka ki daga min waya. "Ba haka bane wallahi." Hajiya Talatu ta katse Anty, Ma u bata fada miki bane, Ina gidan yari a Kaduna, yau din nan na fito ke na fara kira Sahiba yanzu haka kin gani a gida ko ruwan gidan ban kai ga shaba.

Ina tun ranar da na baro gidan ki,to tun ranar ina dira Zariya ko minti talatin ban yi ba a gida, wasu mutane suka kamani suka danna a mota na zata ko yan kidinafin ne, kai tsaye muka tsaya bakin wata kotu a Kaduna aka amshi wata takarda aka kaini aka jefa ni gidan yari ba tare da nasan abinda na yi ba.kuma har zuwa yau da aka je aka kira sunana akace in fito za akaini kotu sai aka tsaya a hanya aka ba wani mai mashin ni aka ce ya kaini tasha ya sa ni a motar Zariya kin ganni nan dirata kenan.

Anty ta cika da mamaki,tace "Ke to da waye ba kya ga maciji ne har haka? Hajiya Talatu tace Wallahi Sahiba ba na ce ba, nasan dai akwai masu jin haushina da yawa, wanda ba su da yadda za su yi dani,dan haka dole sai na nutsu zan gane waye, duk ba yadda ban yi ba amma ko damar yin magana da wani ban samu ba.
Anty tace "Tabdi, to Allah ya kyauta ki ce dai kina cikin matsala ni dai nan damuwar da sauki Asiya ta haukace ta ma bace ba a kara ganin ta ba. Kuma anyi bikin Wannan dan naki, sai dai kuma kamar fa na debo ruwan dafa kaina ne, amma zanji da ita. Kije ku huta ki kuma samo bakin zaren matsalar ki sai ki zo mu san ta kwatanci. Haka dai suka yi sallama.

Da Sulaiman sukaje da kuma lauyan shi, Dan haka kai tsaye suka shiga suka bada suna,an dan samu jinkiri kafin aka gano Kayi nayi. Yana ganin Halifa ya gane shi,nan take hantar cikin shi ta kada. Bayan sun zauna kayi nayi ya soma fadin mai gida dan Allah ka taimaka min wallahi ni ba kwarto bane wallahi san kudi ne zan kai kudin aure gidan su budurwata gashi son zuciya na kare a nan. Kuma yarinyar nan nasan na rasa ta
"ka shirya fadin gaskiya kenan ko? " Zan fada megida, domin na gane cewa Allah daya ne kuma bashi da abokin tarayya. Lauya yace ka bamu labarin yadda aka yi kaje dakin matarsa,daga nan sai mugani me ya kamata ayi?

Mansur kayi nayi. Yace To ni dai wani malami ne zan kira shi ko boka,naje gurinsa da neman taimako akan sana'ata abubuwan basa tafiya yadda ake so, sai yace ga aikin kudi in zanyi,nace zanyi indai ba sata bane.
Yace min zan shiga dakin wata mata ne a wani gida in yi kamar minti talatin, sai in fito za a bani dubu dari kawai dai in yi kamar naje kwartanci. Gaskiya farko na tsorata nace kar mijinta ya dake ni, sai yace Za a bani kudin magani daban. Na ce sai nayi tunani,bayan kwana biyu sai suka sake cewa sun kara min dubu hamsin to daga nan fa sai na yarda tunda sun min alkawarin baza su bari a kamani ba.
Ranar da na yarda matar ta zo har gidanmu ita da kawarta tace bazata bari a tabani ba,dan a gidanta zan yi aikin. Halifa ya katse shi, Kace ta ce a gidan ta? Yace kwarai kuwa. Lauya ya Dakatar da Halifa yace "Ka bari ya gama sai ka tambaye shi abinda ka ke son sani. Mansur ya ci gaba da fadin, nace amma kar a yi min Video tace sun yarda. Naje gidan na yi komai kamar yadda suka ce, amma sai gashi an dake ni, da kyar na gudu ta gurin da ta nuna min,kuma bayan kwana kadan aka kamani aka kai ni gidan yari ba tare da an kaini kotu ba, yanzu haka bansan zaman da nake yi ba, domin so daya mukaje kotu ko gaban alkali ba a kaini ba aka amso wata takarda aka kawo nan.

Halifa ya numfasa yace "Me kasani game da takardar saki da aka rubutawa mata ta? " Kayi nayi yace Megida wallahi bansan wannan ba, iya bayanin nan wallahi su na sani. Kuma wallahi ni ko ganin matarka ban yi ba har sai da ta fito ,ina shiga kicin na shige na boye har sai da suka kira wayata suka ce in fito, kuma duk maganganun da na fada mata na cewa tana zuwa guna wallahi sharri ne ku yafe min. Halifa ya yi murmushin takaici, yace Kasan cewa sanadiyar abinda ka yi yanzu matar ta bace ana zaton ma ta haukace ko?" Kayi nayi ya dauki salati yana fadin ya shiga uku. Halifa yace "Abinda ke bata min rai yadda gaba daya abin ke nuna cewa Anty ce ta hada shi." Kayi nayi yace Yawwa ita ce duk Anty ce ta hada komai wallahi. Da wata kawarta. Halifa suka fita suna tattauna wa akan abinda ya kamata ayi, Sulaiman yace zuwa za ayi a samu Anty a nuna mata ansan komai ina mai tabbatar maka sakin ma ita ce ta hada shi ba wani ba. Lauya yace "Ita ce mana, ai babu dogon bincike kai yanzu Halifa ya ka ke ganin za ayi, musa yansanda su kamota ne ayi case ko me kake gani? Halifa wanda idanun sa suka yi ja,zuciyar sa ta yi zafi a fusace yake ya daki gilashin motarsa na gefen da yake tsaye take ya fashe, suka rike shi suna fadin Haba haba wannan ai ba dabi'a bace. Halifa yace Me kuke son inyi ku fada min. Ya yi maganar murya a sama, har mutane suka fara tahowa,nan suka tura shi mota suna kwantar masa da hankali, Yace "Kamar kaine Barrister mahaifiyar ka ta yi maka haka, Yaya zaka mata ka fadamin?"
Duk suka cika da mamaki,yace wai mahaifiyar ka ce? Halifa yace haihuwata ne kawai bata yi ba,amma tun ina tsumma itace ta raine ni.Uwarmu daya.Barrister yace To zamu tattauna yadda za a bullo wa abin. Bayan su sauke Sulaiman sai Barrister yace Kasan ni na aje wannan yaron a gidan nan tun lokacin da ka turo min Video na abinda ya faru,kawar Anty ku din ma ni na saka aka aje min ita a Kaduna sai jiya na sa aka sake ta, da ka sanar dani halin da ake ciki, amma dole zamu sake dakko ta zuwa nan Kano din, sannan zamu kawo ta nan ayi case din in kuma baza ka yi case da suba,to dole mu hada su guri daya mu warware matsala,sannan shi yaron mu sa ya yi video ya wanke matar ka.

*✍🏻✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[11/15, 17:31] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt
Chapter 47 · 0% Book details