Sashe 61
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Halifa ya daure fuska yana kallon Asiya. Ta sun kuyar da kai, ya shigo ya zauna ya gaida Baffa . Asiya da Sadiya suka gaida shi, ya ƙi amsawa Yace Baffa ga ni.
Jikin Asiya ya yi sanyi amma ta saka aranta duk abinda zai faru sai dai ya faru domin kuwa tunda har ya zo sai ta sha kanshi.
Baffa ya Katse mata tunani da faɗin.
Matar ka ce ta zo kuma ta min bayani komai, ba tare da an maimaita zance ba ina son ka dauke ta ku tafi gida. Ka yi hakuri.
Halifa ya sunkuyar da kai “Baffa Umarni ne ka bani?” Baffa Yace A a shawara ce kawai. Halifa ya mike Tare da faɗin Baffa ka yi hakuri ba zan iya yafe wannan zargin ba, na so in yi hakan na kasa, Baffa ban taba aikata zina ba ko da ina saurayi Allah shine shaida ta, amma ace matar ka wadda ka auro ka aje a gida ita ce zata dinga bin al amuran ka dan kawai ta gano wani laifin ka.Baffa yace Ka yi hakuri Su mata haka suke. Halifa yace Anya ta fada maka abinda ta aikata kuwa ka ke bani hakuri ? Ta fada inji Baffa.
Halifa yace in kuwa haka mata suke to su sha zaman su na hakura. Asiya bata san lokacin da ta mike ba ta isa gaban Halifa ta zube tana fadin Dan girma Allah dan soyayyarka da manzo Allah dan darajar maihaifan ka da suke kasa dan kimar Baffa da muke gaban shi ka yafe min. Wallahi ba zan sake ko kawo hakan a raina ba, na tuba. Ta soma kuka, in kuma na sake ka dauki dukkan mataki a kaina. Baffa ka zama sheda. Halifa ya yi shiru domin dai Asiya ta gama daure shi ta hada shi da kokoluwar abinda za a hada kowane dan Adam da shi ya saduda.
Baffa bai ce kala ba domin in har Halifa bai duba kalaman Asiya ya ba su kima ba, to ido zai zuba.
Dakin ya yi tsit sai kukan Asiya da take yi na debe tsammani domin wadannan sune kalaman da kaɗai take da su in yaƙi sai dai ta koma gida ta rungumi kaddara. Ya sabule kafar shi ya nufi fita. Sadiya da Baffa suka bishi da kallo ya yin da Asiya ta saki sabon kuka.
Dafda zai fita ya furta Ki koma gidan ku zanzo. Baijira Jin komai ba ya fice.
Baffa ya ce zashi tunda yace za shi, amma dan Allah ki kiyaye gaba dan Allah Asiya tace Insha Allah. “Ya ce Allah ya shi muku albarka . Bayan sun dawo gida suka sanar da Inna komai tace To Allah ya kawo shi lafiya.
Sai dai ya zo yau ya zo gobe Asiya har da yin kitso aka yi lalle ana jiran zuwan miji amma shiru.Sai ranar Juma a daidai da cikar su kwanaki takwas da zuwa gidan Baffa Asiya tana kwance a tsakar daki ta yi nisa cikin tunanin mafita. Kamar daga sama taji Inna tana fadin sannu da zuwa Halifa kai ne da rana haka?
Yace Nine Inna kafin Asiya ta tashi ta kimtsa har ya iso dakin kofar ta yi masa shinfida cike da rawar jiki tana yi masa sannu da zuwa.Ya amsa fuska ba annuri
Suna gama gaisa wa da Inna yace Inna idan ta shirya ta same ni a waje kuma ta hanzarta. Inna tace ai gata nan tana jinka.
Yana fita Inna tace Anya Asiya kya koma gidan Halifa kuwa? Dubi yadda ko ta danki baya yi bare ke. Asiya tace Inna ya kike fadin haka? Ta tashi tana tattara Yan shirginta tana fadin Ance miji da mata sai Allah zamu shirya abinmu Inna ke dai ki yi mana addu a. Sadiya ta fitar mata da akwati ya bata leda da kayan sha yi da danyan Kwai.
Asiya ta yi sallama da Inna Abba da Sadiya suka rakota tana ce musu sai sun zo.
Asiya tana ta satar kallon Halifa wanda yake tuki yana waya da abokan kasuwanci sa, ya sa Bluetooth a kunne Ko da ya gama har suka isa gida kala bai hada su da shi ba.. Ya dakko mata kaya har cikin daki. Ya aje ya fita. Ta kwantar da yaron yana bacci a kan gado ta fada ban ɗaki dama bata yi wanka a gida ba, tana faɗin dakin kai da dadi ya ke ba wai batun talauci bane komai karfin iyayenka dakin kai Duniya ne.
Ta fesa wanka ta zata zata same shi a dakin Sai da taje daukar kaya ta lura ba komai nashi a dakin. Jikinta ya yi sanyi ta zura doguwar riga ta fita.
Rataye da jaka wadda yake zuba wayoyi wani lokacin ya fito daga ɗaya dakin. “Kasuwa zaka? Ta furta a hankali batare da ya dube ta ba yace A a Hotel zani. Ya kulle kofar tare da cire makullin ya zura a aljihu. Asiya gabanta ya fadi sabon canji ta darsa a zuciyar ta.
“To ka yi hakuri Yaya Allah ya tsare me za a dafa da dare? Ta fada jiki a sanyaye.
Abinda duk ranki yake so ya furta tare da ficewa.
Asiya ta zo kan kujera ta zauna. Ga dai gida na dawo amma kuma gidan ya jagwale. Ke kika dawo ke kika yi biko dole ki ga cin kashi da bakaken magana da kin share shi sai kin samu wanda ya fishi. Zuciyar ta ta faɗa.
Asiya girgiza kai, a fili tace. “Na dai na sauraro dukkan abinda zaki fada sheɗaniyar zuciyar nan kina yi min mugayen Hasashe ga inda kika jefani.
Da dare Asiya ta fesa wanka ta yi kyau sosai cikin kayan bacci bayan ta yi wa ɗanta wanka yana bacci . Ta ji tsaiwar motar Halifa ta aje yaron akan kujera ta je tana yi masa sannu da zuwa zata amshi jakar yace No barta. Ta bi bayanshi zuwa ɗakin . Tabi ɗakin da kallo ya canza masa tsari ya saka duk wani abu da yake buƙata . Ya camza kayan shi zuwa jallabiya Aisiya tace ga abinci can tuwo na yi da miyar kubewa na kuma yi maka farfesu na kan sa dinnan.
Ba tare da ya kalle ta ba yace ‘ sannu da kokari amma ni yau doya nake son ci na siyo tana mota bari ma na dakko. Ya fita ya bar Asiya baki bude. Kan Dining ta same shi ya zuba a plate ya ture abincin da ta jere a gefe.
Ya dube ta Ki zuba ki ci in kina so. Asiya ta danne wani kululun bakin ciki ta ce ni tuwon zan ci amma bari na rage maka kayan ta kwashe ta maida kicin ta share ɗan hawaye sannan ta dawo. Yana ta cin doyar shi da wani kunun gyada da ya siyo. Sai da ya gama ya du be ta ba wata walwala Ina kika bar ɗan naki? Ta ɗan yi shiru ta na maimaita ɗan ta a zuciya. Ta ɗan ƙago yaƙe ta ce yana falo in ɗakko maka shine?
Yace a a barshi ma haɗu da safe amma kije ki maida shi ma kwancinsa . Asiya Ta ɗan yi dim kenan yana nufin ba zai kwana da su ba.
Dan ta tabbatar tace. Yayi kewar Dadyn sa,dan yau gunsa zai kwana. Halifa ya mike yana fadin ya kwana da Maman sa Allah ya bamu alkhairi.
Asiya ta yi ta juyi a gado ita kam tana bukatar mijinta bare shi da tasan bashi da hakuri.
Wasa wasa sai gashi sun shafe kwana uku Halifa ko hannun Asiya bai yi shauƙin tabawa ba. Kamar ba gaske ba haka take kallon abin. Ranar Asabar da dare tana daki zaune wayarta ta yi ringin ta kalla Halifa ne ya ce ki same ni a falo
Yayi kyau cikin shadda mai ruwan kasa, gashi yanzu kara wani kyau da kwar jini yake yi. Ta gaida shi ya amsa. Yace ki shirya nan da minti goma zan dawo zamuje Unguwa. Gaba daya ta sadakar gida zai kaita baya cin abicinta baya kwana da ita baya daukar ɗanta sakin fuska ma babu a ranta tace Ta gaji wannan karon matsawar ya kaita gida ta hakura da shi.
Ta dawo ta saka jallabiya da mayafin ta ta fito sabe da ɗanta ya kalleta in baki da kaya masu kyau to kawai ki zauna a gida.
Tace bari in canza . Yace Shima wannan yaron asa mishi kaya masu kyau.
Ta gane fita zasuyi dan haka ta saka kayan fitar sunan ɗanta shima ta saka masa sabbi .Suna ta kamshi Halifa sarkin son gayu sai satar kallon Asiya ya ke yi.
Bata san ina zasuje ba kuma bata tambaya ba.
Sai ga su a layin gidan su Anty Gaban Asiya ya fadi ta kalle shi tana tuna rabonta da gidan tun lokacin da aka yi
mata sharri. Muryar tana rawa tace Yaya dan Allah….. Kar ki damu ya katse ta gani nan tare da ku.
*✍🏻 HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[2/10, 11:24] Ummi Tandama😇: *Alhamdulillah masu jiran a gama littafin HASASHE na HALIMA K MASHI document ya kammala ga duk me buƙata zai iya turo kuɗin shi ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank, shedar biya ta wannan number 0814 000 4302*
Asiya ta dubi Halifa naga kamar gidan da jama a me ake yi? Gajen hakuri ya ke saka unguwarzoma tambayar me aka samu? Ba shiga za kiyi ba? Ya fada yana gyara paking . Suka fito Asiya ta tsaya tana hasaso abinda ya faru. Ko ma dai menene shi a ni ne gaskiya. Dan ta ga su Nihal cikin sabbin Kaya.