Sashe 25
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bros ya Iso gidan cikin wani mugun gudu ya yi fakin sam bai kula da su Dady ba zai yi ciki. Dady ya ce "Kai Adamu.! Bros ya dawo da sauri ya ce Dady ban kula da Kuba, ya gaishe su. sannan yace da safen nan naga sakon Hafsi wai suna ta kirana ban daga ba, wai ƴan kidinafin sun sace Halifa da matarsa.! Dady yace" To, abinda dai muke ta zato kenan Mamanku da zata bamu tabbaci sai kuka take Taki fadin yadda a kayi ta samu labari.... Ya katse maganar sakamakon motar Halifa da ta shigo cikin gidan. Cike da al ajabin ganin Baffansa a gidan da sassafe haka ya fito a motar yana fadin Baffa lafiya da sassafe haka da ka kira ai da sai in zo?
Ya kula da yadda duk suke kallon shi, har ya dubi jikin shi ko wani abu ne, yaga ba komai a jikin shi. Daidai lokacin Asiya ta katse su da fadin ina kwanan ku? Babu wanda ya iya amsa mata, sai Baffa da ya dubi Halifa yace "Ina wayarka?" Halifa yace tana mota.Ya juya da sauri ya dakko yana fadin ashe ma a kashe take. Dady yace me yasa ka kashe kuma baka sanar da Antynka ina kaje ba? Sai lokacin Halifa ya tuna da ya kashe wayar sa tun da suka shiga gidan domin su samu sakewa.
Yace Tab aini na shafa'a cewa na kashe wayar, Anty ma shafa a nayi munje ganin gidana ne domin ina son mu koma cikin satin nan, to munyi yan gyare gyare muka gaji sai kawai muka kwanta. Bros ya ja tsaki, amma ka dauki alhakinmu ka taso kowa tsaye. Halifa yace Ya Salam! Bros ya ci gaba da fadin "Antynka ta ce yan kidnafin sun sace ka. Asiya ta zaro ido. Baffa yace mikawa Dady hannu yana fadin to ni zan koma tunda Allah ya takaita. Ya dubi Halifa Kai kuma Malam Umar ka daina kashe waya sannan ko baka sanar da kowa cewar ga inda kake ba, lallai Antynka ta sani.
Zan kiyaye Baffa ina neman afwa na fito da kai tunda safe. Babu komai yarinya kije ciki ko? " Baffa ya fada yana Kallon Asiya. Ta rusuna a gaida gida. Ta wuce sasanta tana jimanta abin yayin da Halifa da Dady da Bros suka nufi cikin gida.
Anty ta mike da sauri lokacin da Halifa ya shigo falon ta na fadin Allah na gode maka ta fashe da sabon kuka ta zo ta rungume shi tana fadin Halifa ba su taba ka ba ko? Da.ma Malam yace zaka dawo da safe. Halifa ya dago ta daga jikinta cike da kauna yace, Anty babu wanda ya kama ni, kuskure na yi na kashe wayata Mun bita gida na ne, dan inason mu koma ciki sai na biya Inga me gidan ke bukata kawai daga kallo muka yi bacci. abin daya daure min kai wa ya fada muku barayi sun kama mu? Anty ta cika da mamaki har anzo lokacin da Halifa zai yanke wata shawara ba tare da ya fada mata ba?! Tadanne abinda take ji na takaici muryar ta a disashe tace shikenan Dan uwana tunda Allah yasa ka dawo lafiya kana cikin koshin lafiya Na gode wa Allah. Sauran yan uwa suka yi ta jajantawa Halifa.
Yayi musu alheri kowa ta koma gidanta.
Asiya kam ta hada masa abin kari harta canza kaya. Ya kalleta ke ce kika yi kidinafin dina fa, tun jiya kika tada hankalin kowa a dangi na . Asiya ta lumshe ido tana tuno yanayin da suka samu kansu a jiya.
Ta bude idanu ta zuba su akan nashi, tace "Jiyan nan ji nake mu kadai ne a Duniya daga ni sai kai, akwai wasu kalamai da ka furta ka yi ta maimaita su, tun jiya ni kam da na tuno su sai inji babu macen da ta kaini sa'a a Duniya. Ta mika mishi tafin hannun ta sai ya dora nashi, tace kamin wani Alkawari guda daya. Ya matso "Fadi inji" Duk yadda rayuwa zata juya mana baza ka sake ni ba? Sosai ya jawo ta jikin shi ya rungume kam. "Babyna kar ki kawo maganar rabuwa ni dake ina fata mutuwa ce zata rabamu, nima kuma ina rokon ki kiyaye. duk abinda zai iya haifar da hakan." Ta dago fuskarta ta dube shi, ta kai hannu ta kama dan gemun sa na gayu tace, Wane irin laifi ne zan maka har ka iya rabuwa dani? Yace Ki ci gaba da girmama magabata na iyayena sun mutu amma suna da madadi kamar Anty da Dady. Kalli yadda suka rude iya jiya da basu jini ba. Dan Allah ki girmama su. "Asiya ta fita daga jikin shi ta koma ta zauna. Idanun ta cikin nashi tace. Zan zame maka rabin Duniya mace ta gari zaka yi alfari da ni insha Allah. Ban san menene so ba, amma ina matukar son ka, ina kaunar ka. Ta kai karshen maganar tare da kai hannu ta shafi kumatun shi.
Kalaman suka yi masa dadi. Ya janyo ta jikin shi tare da fadin " Ki gode wa Anty da ta kawo shawarar cewa sai mun gwada gidan su Bilkisu. Har ga Allah lokacin da na ganki banji komai ba, amma yanzu da gaske ina son ki. Dadi ya kama Asiya. Ta shiga hango irin rayuwar da za su shimfida ita da Halifa a sabon gida.
Anty tana kwance cikin bargo zazzabi ne ya rufe ta tun da Halifa ya fada mata cewa zai tare kuma har ya iya tafiya ya kwana ba tare da ya kira ta ba, abin ya kona mata zuciya. Wannan ya hadda sa mata zazzabi.
Halifa ya shigo yana fadin Subhanallah Anty aje Asibiti mana a duba jikin naki? Tace "Zazzabi ne zai sauka, zuwa anjima. Halifa dama kiranka na yi wannan abu da ka yi ka saka ni a damuwa, ace zaka tashi amma ban isa ka sanar dani ba harma ka dauki matar ka kukaje gyaran gida?" Ba gyaran gida mukaje ba kawai dai mun biya ne, amma to ki yi hakuri Anty bazan sake ba. Idan kin samu sauki kuma sai mu tsaida ranar da zamu tare din. Sannan Anty zan baiwa Asiya kayan lefen nan a gurinki saboda ta yi sabbin dunkuna amma za mu cire wadanda suka yi mata yawa kamar jallabiyun ciki sai a canzo mata daidai ita ko Anty.?
Wani sabon takaici ya cikata duk ta saida rabin kayan kuma ta zaci ba zai sake magana ba.
Ta cije tace to ba damuwa. Yace to Bari na tafi Na shirya Na fita tun jiya oder ta ta zo,ban samu nutsuwa ba bare a bude kayan. "Anty tace Allah ya taimaka. Halifa yana fita Anty ta tashi zaune ta dakko waya tana tunanin wane malamin zata kira.
Wanda ya yi wannan aikin yana da zafin hannu shine ya dace ta kira, domin ai dama ita ce tace yan kidnafin sun kama Halifa, shi cewa ya yi yana mugun hannu kuma wannan yarinyar itama ai mugun hannun ce. Yace mata zai dawo gida da sassafe kuma dai abinda ya faru kenan.
Ta danna kiran shi suka gaisa tana sake yi masa godiya tace Dan Allah wani aikin zata bashi tana son ya kulle mata bakin Halifa domin ya bata ajiyar kaya ta siyar da kusan rabi ta kashe kudin. Sannan zai tare a wani gidan sa, tana son ayi abinda gidan zai gagare su zama su dawo kusa da ita.
Yace "To yanzu dai yana son ta fada mishi abinda suka fi tsoron maciji ko mage ko dai wani abu a kwari, sannan maganar rufe baki angama amma kudin aikin sa dubu dari biyar. Tace Haba Malam kai matsalar ka cika kudi Dan Allah ka min sauki dubu dari biyu zan bada.
Yace "Haka ne kudin, ba wai suna na saka ba, ina son aikin nan harda aljanu zan hada kinsan me za su bukata ni a gurina? Ko zaki iya basu jinin mutum? Anty ta yi shiru tana tunanin kudin inda zata samu. Tace Malam zan bada dubu dari kafin alkalami. Ya ce duk lokacin da kika shirya ki sanar dani, ina nufin in kin tanadi kudin. " Ya kashe wayar sa. Tace Shege mayen kudi duk da nasan cewa aikin shi kamar yanka wuka, dole in San ya zanyi in yaga dari uku cash zai yi aikin,domin dai da kunya Halifa ya zo kan kayan nan ace ba su. Yanzu aciki zan dibi sarkokin nan in yi kasuwa da su.
*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*
*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[7/14, 07:16] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w
Kamar da wasa Anty ta hade kan sarkoki ta cefanar, ta shirya ta kaiwa Malami kudi ya amshe dari uku da saba'in ya mata laminin sauran ya bata magungunan da zata yi, yace mata duk ranar da ta gama amfani da maganin ta tunkari Abba ta fada masa cewa bata son ya bar gidan sannan ta sanar da shi cewa ta yi amfani da kayan shi. Yace babu abinda zai iya.