Sashe 19
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta Mike. Ko shakka banayi Maman Nihal ta shiga malamai ne ta dawo da Yayanku cikin rayuwar ta. Bazan taba kyale wannan ba. Ta soma danna waya ta kira Numbar shi daidai lokacin sun tsaya a gurin wani mai takalman yara tana zabar wa su Nihal da Nur.
Ya daga tare da fadin Anty barka da yamma. Adamu!!! Anty ta furta cikin ihu da kara ji. Cike da firgici yace na'am Anty me ya faru? Domin a duk lokacin da yaji ta ambaci sunan sa, ya tabbatar cewa wani babban bala'ine zai faru. Ubanka ne ya faru. Ta furta a fusace, me ya hada ka da Maman su Nihal? Gaban shi ya yanke ya fadi, wanene ya fada mata kenan. "Ina tambayar ka ne fa."!! Ta sake katse shi. Yace Anty mamaki nake yi kuma waye da wannan maganar ni dai ina Kaduna tun sassafe? Tace "Kana nufin ban ma san ka ba kenan, to nice da kaina na ganka ko ni da na haife ka ma bazan gane ka ba?"
Zufa ta shiga keto masa ya yin da Maman Nihal ta shiga tashin hankali. Ya daure yace Bazan taba karyata ki ba Anty amma zaki iya bincikawa ki tabbatar idan ina gari, kila wani kika gani da irin mota ta na yi miki gizo, to amma a wajen inane haka? Hafsa dake gefe tana jin su ta ce a kofar famfo a danja.
Anty ta ce. "Adanja ta kofar Famfo tunda so kake sai ka titsiye ni.. " Ya jiyo wata muryar tana fada mata Dan haka ya tabbatar ba ita bace ta ganshi ba, yanzu haka munafukar yarinyar nan ce Hafsi. Dan haka ya samu kwarin gwiwar faɗin to ni kuma me zai hada ni da kofar Famfo ko ina garin ma Anty kinsan ba hanyata bace, amma dai ki bincika din dan ki tabbatar ba na ma garin ni.
Ya jefa mata shakku dan haka sai ta dan sassauta murya tace ai dai ina son ka sani ko a mafarki na ganka kai da wannan mai kashin tsiyar mai farar kafa tauraruwa mai wutsiya sai na yi maka baki bare kuma ace a fili kaji na fada maka. " Yace To!
Da sauri ya kalli Maman Nihal ina wayar ki? Tace tana mota yace su tafi su bar batun takalma ɗin nan, a mota ya yi amfani da wayarta ya kira Halifa yace Dan Allah ko da Anty zata kira ka, ina Kaduna. Halifa yace" Yanzun kuwa ta kirani kana ina na ce mata wallahi ba sani ba, sai dai ina zaton baka gari domin hakan nake tsammani da gaske, amma me ya faru? " Bros ya bashi labarin komai. Halifa yace" Kasan Allah Ramin karya kurarrene kawai ka fito a mutum a yi wacce za ayi. " Bros yace Halifa bawai bazan iya bane muna da banbancin, kai kani ne, ni kuwa ɗa ne dole inyi taka tsantsan in ta jefeni da kalaman la ana sai in lalace. Halifa yace Allah ya kyauta sai ka yi ta addua.
Ya kira yaran shagon sa ya fada musu duk wanda ya kira ya tambaye shi ace yana Kaduna. Kiran Hafsi ya shigo wayarsa Maman Nihal ta Mika masa yana daga wa ta katse. Ya yi dariya yace kinsan me yasa na kira da wayar ki, zasu yi ta kira na wai ko zasuji tana busy sai su ce ina fadawa mutane ace bana gari. Har ta kira Uncle Halifa. Maman Nihal ta sauke ajiyar zuciya har lokacin a tsorace ta ke, tace "Baban Nihal kullum zullumina Anty ta san muna tare, shiyasa nace maka da mun hakura.
Ya kai hannu ya shafi cikinta. to da ta yaya zakiyi da wannan? Ta lumshe ido tare
da fadin"Allah gamu gare ka."
*** *** ***
Nihal ta kwankwasa kofa Asiya ta bude ta ga yarinya tsaye tace shigo ta zaunar da ita a kusa da ita tana tambayarta sunan ta. Ta ce Nihal kanwata kuma Nur.Asiya Tace ina ne gidan ku? Cike da wayo yarinyar tace nan gidan muke Bros ne fa Dadynmu."Asiya ta danyi shiru tana jin sunan Bros amma batasan shidin waye ba. Dan haka tace ya yi kyau,mamanku ma tana cikin gidan? Nihal Uwar zuba tace a a, Momin mu ai Anty ta koreta shine ta kwace mu ta kawo mu nan gidan."
Gaban Asiya ya yi mummunan faduwa Tofa! Yarinyar ta ce, Anty kullum sai muce ta kaimu gurin mamanmu amma ta ki sam sam". Cikin tausayi Asiya ta shafa mata kai, karki damu zaki ga Maman ki kinji. Nihal ta daga kai, alamun eh.
Tun bayan zuwan su gidan malamin Anty tace a daina kaiwa Asiya abincin rana da na safe, shima na daren ta ce a kai ne domin ko wani dalili zai samu na zuba mata wani maganin.
Halifa ya samu Anty da maganar rashin kai abincin, tace ita gaskiya tunda suka fita aka fadi maganar nan akan Asiya yarinyar ta fice mata a rai, dan haka su yi girkin su na dare kawai za a ba su, kuma shima ya shirya ya koma kasuwa, ranar kwanan Asiya uku a gidan. Shine da ya dawo daki ya samu Nihal a dakin. Har yanzu ya kasa natsuwa da Asiya akan abinda Anty ta fada hakan ya sa yanke ɗan dake mata, sai kawai ta dake ita ma, domin bazata yarda da irin wannan sharrin ba.
Nihal ta Kalle shi Tace Uncle Halifa kana da Number Momin mu ka kira min ita? Yace kullum sai kin tambaya bakya gajiya Nihal Number Dady ku gare ni ki bari in ya zo sai ya kira miki ita. " Tace ai shima haka yake cewa bashi da Number Momyn mu." Halifa yace to tashi kije Anty Hafsa ta shirya ki lokacin islamiya ya yi.
Bayan fitar su Asiya ta mike ta nufi cikin daki dan tana jiyo kiran sallar la asar. Halifa ya bi bayan ta da kallo wani abu ya tsirga mishi, ya so ya dake amma sai tsigar jikin shi ta kama tashi. Ya mike yana mika ya nufi cikin dakin ta aje dankwalinta a kan gado, dogon gashin ta ya zubo, ta daga ido ta kalle shi ya iso daf da ita ya tsaya. Ya kai hannu ya shafa gashin sai kuma ya janyo ta zuwa jikin shi, ta tuna wuyar da tasha ranar tace dan Allah Yaya Halifa karka sake da zafi bazan iya ba. , cike da shagwaba ta yi maganar. Yace a hankali zan miki ai na yau bazakiji zafi ba,. Tace " To ba kana jin haushi na ba." . Yace Inji wa na isa inji Haushin ki kawai duk shedan ne ya ke so ya shiga tsakaninmu. Zata sake magana ya datse mata baki da nashi sai labarin kuma ya canza.
Abinda Anty ta manta su mata da miji sai Allah, alaka ta saduwa a gurin ma aurata tana kara kusanci da shakuwa dan haka ko an shiga dole aji kunya bare sabbin ma aurata. Shi Halifa da alamu yana da karfin shi awa dan haka ko a daren ranar bai barta ba haka kuma da safe, duk ta jure musamman da ta lura da yadda tsakanin jiyan zuwa yau wani tattalin ta ya ke yi, sai ta sha alwashin in zai zo so goma a rana zata amshe shi ba tare da nuna gajiyawarta ba.
Halifa ya koma kasuwa zuciyar sa tas ga hasken angwanci duk tunanin shi yana gida, kadan kadan yake kira yaji halin da Asiya take ciki, domin ya baro mata wayar shi, da zai koma gida ya duba a shagon sa ya daukar mata waya IPhone komai ya gani na kwadayi sai ya sai mata.
*** *** ***
Wajen ƙarfe shida Asiya fesa wanka bayan ta gama girka taliyarta jolop ta ji kifi. Tana bude masa kofa ya shigo ya aje ledojin sai ya rungume ta. Tace muje ka watsa ruwa ka warware Yayana ko mai yana nan fiye da jiya. Haka tayi ta janshi har aka yi Isha I bayan ya ci taliya yana mamakin ashe ta iya girki.
Kicin ta koma ta fashe kwai guda biyu ta rumtse ido ta shanye ta zo ta dibi madararr da ya kawo musu mai sanyi ta shiga dakin tana sha. Ya na waya da wani kwastoma ya nuna mata jikinsa ta lafe a cinyar sa zuwa kirjinsa sai maganar sa ta soma canzawa yace zai kira shi da safe yanzu akwai matsalar network. Asiya ta sa masa kofin madarar a baki tana fadin nice Network din ko? Yace ""Ai ke kin fi network karfi Babyna. " Sunan ya mata dadi, ashe itama za a kirata baby kamar dai yadda take karantawa a littattafai. Gaskiya ne labarin littafin yana faruwa akan mutum......
*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*
*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[6/18, 20:04] Ummi Tandama😇: A tsawon sati biyu ma"auratan sunyi kaffa kaffa da juna, sun shaku da yawa ta yadda Halifa yake ganin ba shakka ya dace da abokiyar rayuwa matsalar guda daya ce akwai wasu girke girke wadanda bata iya ba daga taliya sai wake da shinkafa sai tuwon masara bata boye ba ta sanar da shi, ta bukaci ya sai mata littafin girki yace ai yanzu ko a Soshiyal midiya zaki koyi yadda ake girke girke na zamani ya sa mata data ya bude mata kafofin sadarwa na zamani ya ce duk ta koya.