← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 62

Sashe 43

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yawan addu'a ya sa wa Inna dangana da kuma yan uwanta da suka zo jaje suka kwantar mata da hankali. Sai dai kukan zuci. Halifa yana kwance rigin gine Asiya ta tada kai da kirjin shi tana lallashin sa akan ya tashi ya tafi gidan su Inna dan ya gano mata halin da Inna ke ciki. Shi kuma yana cewa shima a yi masa alkawarin yau za a bashi hakkin shi tunda dai sauki ya samu kuma sun tambayi likita yace babu matsala za su iya yin mu amalar su ta aure.
Tace to naji amma so daya.Yace Haba baby ko ba a dade haka ba kin san dai ya yi kadan. Wayar shi da ta hau ruri ce ta hanata magana.

Yace Anty ke kira kinsan na bude wayar domin na nuna musu cewa na dawo.

Ya daga da sallama. Tace "Halifa manyan gari, duk yadda na so in yi fushi da kai bana iyawa, amma kai yanzu ka ma tare a gidan ka ni ban isa ka sanar da ni ba saboda na taɓa maka abin duniya, to ba komai Halifa zan biya ka ka rubuta ko nawane in ma bansamu ba ya zama bashi ko na mutu yarana su dauki nauyi su biya ka....Takai karshen maganar tare da fashe wa da kuka. Hankalin Halifa ya tashi yace "Anty ai kinji ke matsalar ki komai kuka dan Allah ki yi hakuri ni na yafe kayan kin fi karfin su a gurina kawai naji haushin a bin ne amma ya wuce."

Ta ce Ya kuma labarin yarinyar nan ashe ta bace ko? Halifa ya kai hannu ya shafi cikin Asiya sannan yace" Abinda ya dawo da ni kenan daga Dubai Anty ya za ace yarinya ta bata kamar wata kaza."

Anty tace ni da zaka yarda wallahi da ka share su kar ka shiga zancan nan tunda kai ba a gidan ka ta bace ba, ai danake fada maka tana da ciwon hauka ai baka yarda ba,yanzu dai gashi yar fara ta nuna.

.Halifa yace "Ta ya zan kyaleta da cikina a jikinta?"Anty dan Allah kar ki fadi wani abu da zanji babu dadi. Ta dan yi shiru sannan tace "Shike nan Halifa amma ka bi a hankali Allah ya bayyana ta,dama ni dan naga yanda yarinyar ta kawo mana kwar.... "Antyy" Ya katse ta da sauri, ya ci gaba da fadin, karki karasa wannan maganar bana bukatar ta.! Tace Na yi shiru kana sabon gidanka ne? Yace Hotel na sauka,anjima zan shiga gidana,zan shigo nan gidan ma zuwa dare ya katse wayar domin tuni idanunshi sun kada sunyi jajir.

Mai siyan akwatuna ya Isa kofar gidan Anty da babbar mota,ya shiga yana sallama. Nihal ce to sanar da Anty ta yi bako.
Gaban Anty ya fadi lokacin da ta yi ido biyu da shi. Ta daure fuska ta iso gabanshi. Lafiya malam da sasafen nan zaka diro min gida? Yace dole In diro kin ki daga min waya bayan yarjejeniyar mu ta cika shiyasa na shigo cikin biyu a yi daya a bani kudina ko kayan kudi ga mota can waje.
Anty ta ce "In kuma babu fa?" Yace dole ma akwai.

Hayaniyar su ta tada duk yan gidan. Dady ya tsaya kallon mutumin cike da takaici yace kai me ya kawo ka cikin gidan matar aure? Mutumin yace ita ta gayyato ni,ai ni na zata ma bata da miji. Dady yace "Ni ba abinda na tambaye ka kenan ba, abinda kawai nake son in sani me ya kawo ka yanzu?"

Yace kudi na ta ara akan zata saida min akwatuna, miliyan daya, daga baya tace dama na kaninta ne kuma ya kwashe kayansa, amma kudin ta ara,na fada mata sati biyu zata dora min ribar dubu dari biyu da hamsin ta yarda,gashi yanzu an kusa wata bata daga kirana,yanzu dai kudina a gurin ta miliyan daya da rabi da dubu saba'in, dan kullum kwanan Duniya kudi na karuwa suke yi. Dady ya dubi Anty rai bace, yace ki bishi waje kuje ku yi case dinku a can dan Allah. Ku fita waje! Anty Ta dubi Dady cikin wulakanci tace sai dai kai in bazaka iya ji ba ka fita domin dai gidan ba naka bane kuma bana wanin ka ba. Dady yace "Ko sarkin gori,to albishirin ki, yanzu wannan gidan mallakina ne, Halifa ya mallaka min shi ya bani takardun sa haka wanda Adamu ke ciki ya mallaka masa ya bashi takardunsa!!
Anty bata san lokacin da ta kai kasa ta zauna ba,sai da taji su Hafsa na fadin Anty kiyi a hankali.ta dafa ta. Ta kalli Dady Kasan Allah bazata sabu ba, kura da shan bugu gardi da kwashe kudi. "Kiji da ni dan Allah. "Mutumin ya katse ta,cike da bala'i tace kai bani da su bani da dalilin su ,haukatani za ku yi ? Ta fashe da wani irin kuka na tsananin takaici. Dady ya dube shi yace shigo ka duba duk abinda ya kai darajar kudin ka ka dauka amma kaima ka yi Don Allah. Ya koma ciki ya shirya zai fita lokacin suna fita da kujeru Ko kallon su bai yi ba ya wuce.

Anty ta na kwance ta sa Hafsi ta kira mata layin Yayansu ya daga Anty ta karba ta ce kazo yanzun nan ina nemanka duk inda kake ko me kake ka bari kazo.

Bros ya saki baki yana kallon Falon Anty ba komai ba kujeru bare firji ba TV Ya nufi dakin ta,turus ya yi da ya ganta a kan katifa ga shirgin kaya wandan da su ke cikin sif An tule su gefe. Cike da mamaki yace Anty lafiya?

Ta dubeshi "Wato har na yi lalacewar da zaku hada kai da Dadynku da Halifa ya baku gida ya mallaka muku amma ban sani ba, kuma ban isa ayi shawara da ni ba ko?"
Bros ya ce wallahi Halifa ne ya hana mu fada wai zai fada miki in lokacin hakan ya yi,amma ya ba Dady takardun gidan nan da ya amsa a hannun lauyoyin sa,sannan nima ya bani nawa gidan da nake ciki.Anty tace magana dai ta tabbata. Hummm lallai Halifa ya dauka da zafi daga taba kayan akwatin sa shine yake ta min irin wannan ramuwar gayyar!!
Hafsa tace "Kema Anty na fada miki fushin fari ba naki bane ki kira shi a waya kiyi masa godiya karki nuna kinji haushin komai sai kiga ya baki naki rabon ki samu ko gado ki saya." Uban gado Anty ta katse Hafsa suma ba su wahala da shi ba ya basu gidaje bare ni da nai rainon sa? Adamu yace 'Haba Anty infa ya bamu tamkar ya baki ne, ke yanzu me zakiyi da gida? Burinki bai wuce ki barma gado ba,to mun yafe karki damu, kina karkashin Dady ne,shine cinki da komai,dun radda babu Dady mu gamu zamu rike ki.....'.Kai Adamu sa idonka cikin nawa. Anty ta fadi tare da Mikewa zumbur. Kana nufin ni yanzu na tsufa bani da sauran lokacin da zanyi wata rayuwa mai dadi?In yi gayu in hau mota in fita kasashe inga gari.....

✍🏻 *HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[10/27, 09:26] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt

Adamu yace Haha Anty ya kamata ki daina zafafa al amura,kina dagawa kanki hankali ko masu yawo kasashen da kike magana da yawa dalili ke kai su daga kasuwanci sai ciwo masu yawan shakatawar a wannan karnin ba su da yawa. Amma in kin yadda,ki yi zamanki kiyi istigfari in Allah ya kawo hajji ko Umra sai ki je kiyi adda"a kema ki huta da damuwa.

Anty ta girgiza kai tare da fadin "Bashakka,dole ka fadi haka tunda kun rufe min alkhairin da dan uwana ya yi muku, amma ba komai. Yanzu sai ka fada min dalilin da ka daina zuwa gidan su yarinyar can." Ya dan yi jim sannan ya ce Anty In fada miki gaskiya ko kuwa in yi miki karya? Ta dube shi menene ribar karya,kawai ka fada min gaskiya. Yace kiyi hakuri Anty wallahi bana son yarinyar nan ne. "Kayi kadan ta katse shi ,ciki. daga murya ta ci gaba indai ni ce na haife ka wallahi sai ka aureta....Jiri ne ya debeta sai gata wanwar ta fadi kasa ba tare da kowa ya ankara ba.

Agigice suka kama ta suna mata sannu.Adamu yace muje Asibiti Anty ta dafe kai tana fadin kaina ciwo yake min. Aka kwashe ta zuwa Asibiti Bayan gwaji likita ya gano cewa Anty jininta ya hau dan haka ya kamata ta kwanta a Asibiti . Anty ta buga kafa tace ita fa baza ta kwanta ba, gida zata koma dan tana da abubuwa a gabanta. Hafsi tace to Anty gida kuma akan me zaki kwanta ba gado ba kujera. Sai suka ga Anty ta saka kuka.

Abinda ke bawa Adamu haushi duk wannan halin da Anty ke ciki babu wata nadama a tare da ita. Badan ta so ba ta kwanta. Adamu ne ya kira Halifa ya sanar da shi cewa Anty tana Asibiti. Sai dare yaje tare suke da Asiya sai ya barta a mota.
Ya kalli Anty duk ta rame, yace "Anty wallahi ki daina damun kanki game da wa su lamura da basu shafe ki ba. Yanzu me likitan yace? Tace "Ni kawai ka ce masa ya sallame ni zan sha magani a gida ina da sabgogi da yawa a gaba na, wannan kwanciyar zata kawo min cikas.

Wane irin sabgogi kenan kike magana? Halifa ya katse ta. Hafsi tace Uncle ko ta koma gida fa wani mutum ya zo da mota ya kwashe kayan gidan duka. ,"Kamar Yaya? Halifa ya tambaya. Kafin Hafsi ta amsa Anty ta fara wani irin nishi da kuka ,dole suka maida hankali a kanta. Kuma ta yi haka ne dan kar ta fadawa Halifa maganar.
Halifa dai ya fada wa likita lallai kar a sallameta sannan duka abinda take bukata a yi mata.

Da suka bar Asibiti kai tsaye unguwar su Asiya sukaje ya aje motar Inda ya saba ajewa sannan ya tafi gidan su ya bar Asiya amotar yace ta jira shi kar ta fito.

Ya kira Sulaiman suka tafi gurin Inna.
Chapter 43 · 0% Book details