Sashe 28
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daya daga cikin likitocin ya shigo yace "Kayi hakuri fa, kar ku sakata magana da yawa domin Allah ne yasa ta tashi mu kammu mun kasa gane ko wace nau in guba aka bata amma zamu tura Asibitin Aminu Kano. Babban likita zai yi maka bayani. Sannan bisa shawara ka sanar da Yan sanda dan su yi bincike akan lamarin nan. Anty dai ta kasa magana tsabar fargaba. Halifa yace gaskiya dole muje gaban Hukuma gaba daya na kasa gane ma al'amarin Ya kalli Anty. Duk yadda aka kayi wanda ya turo aka sa wa yarinyar nan abin hana daukar ciki, shine dai ya sa aka zo aka bata guba. kuma wallahi na jikina ne. Har lokacin Anty ta kasa magana. Sai da yace Anty tace ki kwantar da hankalin ki tunda Allah ya sa ta farka zata mike. Anty tace "lnsha Allah ta matsa kusa da gadon tace. Sannu Asiya." Asiya ta saki murmushi, gaban Anty ya fadi ta rasa murmushi me Asiya ke yi. Ta ɗan ja baya tana fadin Allah dai ya baki lafiya.
Babban likita ya kira Halifa ofishin sa, yadda wannan likita ya shigo yana bayani haka ya fada masa. Ya kara da cewa a jikin guntun muka samu gubar an canza ainihin Apple din dan kar a gane Allah ne ya sa ka dakko guntun dan haka wannan matsalar tana bukatar jami an tsaro ko da na sirri ne dan su bincika su gano ina ne matsalar take.
Halifa ya ce babu damuwa insha Allah da mun bar nan zanje na sanar da su. Halifa yace zaije ya sanar da inna dan ya taho da Sadiya ta zauna da ita. Sai Asiya ta rike masa hannu tace karkaje ka kyale su in Innarmu tana da hawan jini zata damu ko na fito dan Allah kar ka fada musu, ni da zaka yarda daka rufe maganar domin kowa ya ji zai zargi yan gidan. Halifa ya ce To amma kuma sai in zura idanu a kashe min ke da dana, me yin abin nan fa bai fara Dan ya daina ba. " Asiya tace kawai kace wa Anty ko ita ko Hafsa nace wa, ni ya zo ya zauna da ni.
Cikin kwana biyu Asiya ta samu sauki ciki kuma yana nan babu abinda ya shafe shi, Hafsa ce ta zauna da Asiya likita ya jaddada wa Halifa lallai gubar mai tsanani ce badan taimakon Allah ba minti biyar Asiya baza ta kara ba a Duniya Dan haka ya hana ta cin kowane abu daga hannun kowaye, domin gudun kar a sake samun matsala.
Suka dawo gida Halifa yana cike da zarge-zarge a zuciyar sa. Suna kwance ya kama hannun Asiya wadda har ta soma bacci ta bude ido tace Yaya kana son wani abu? Yace Yace magana zamuyi Asiya ina cike da tsoro ne kar in zargi wanda bai kamata ba, Dadyn gidan nan na ji ina zargi kuma na kasa goge zargin. ". A uzubillahi Mina shaidanirrajim gaskiya kar ka dauki alhakin sa, me zai sa ka zarge shi? "Shine ya hanani in sanar da jami an tsaro kamar yana tsoron asiri ya tonu" ya faɗi mata dalilin zargin.
Asiya ta fada masa yadda abin ya faru sai ta kara da cewa ina sunan Dadi zai fito a nan? Yace kenan Bros ne? Asiya tace gaskiya bashi ya kawo Apple ba, Anty ta siyo kuma ina zargin wanda ya kawo Apple dinnan bayan na shiga wanka ya zo ya canza. Dan haka kabar zargin kowa kawai mu kyalle koma waye da Allah yake fada bada mu ba. Halifa ya rungumo Asiya yace yanzu ji nake kamar ke kadai na yarda da ke duk Duniya wallahi Asiya kowama zarginsa nake har Anty. Sai lokacin na yi magana. Ka yi hakuri insha Allah ba wani na jikinka insha Allah.
Haka dai suka ci gaba da rainon ciki Halifa ya hana Asiya cin duk wani abu da ya fito daga hannun kowa, kuma ya kasa ya tsare da adduo'i Baffan ya basu ruwan addu a na neman tsari ya zama shine ruwan shanta. Duk inda zata Halifa ke kaita Asibiti kuwa sai ya jirata. Wani lokacin yace kar ta yi girki ya dauke ta su tafi gidan cin abinci. In gurin su Inna ne sai ya kaita in ya taso kasuwa ya jibgo tsaraba ya kai musu.
Anty ta na cike da tashin hankali amma dole ta lafa tukunna tunda ta samu Halifa ya hakura da kiran Hukuma.
Cikin bacci Asiya taji hayaniya; a tsakar gida amma sai bata fito ba, dan ta saba tunda bata zuwa Kallon fada. Kamar saukar aradu Asiya taji muryar Halifa a fusace, yace, Asiya!!
Ta ta shi da sauri tana fadin lafiya? Yace Dan Allah malama ya kike yi kamar baki san komai ba!! Mamaki ya cika ta, ta sakko a gigice ta bi bayan sa zugwi,har tsakar gida. Wani matashi ta gani yasha duka yana durkushe jini na zuba. Ga su Anty da su Hafsa harda da wasu maza wadanda ta ke tunanin cewa maƙota ne...
*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*
*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[7/29, 21:25] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w
Ga zaton ta barawo aka kama, ta dubi Halifa ta ce a ina ya yi sata? Kafin Halifa ya bata amsa sai taji barawo na cewa Dan Allah ku yi hakuri wallahi sai da nace wa Asi baby kawai ta zo inda muka saba haduwa gidan abokina wanda ya rabu da matarsa can take zuwa idan Halifa ya tafi kasuwa, to da yake ina zuwa wasu lokutan a nan idan ya fita yauma wallahi na musa amma tace yanayin jikinta ya sa ta kasa...... Halifa ya sa kafa ya tokari cikin sa, sai da ya yi kara sannan jini ta hanci ta baki aka rike Halifa yana fizgewa akan cewa a sake shi sai ya kashe shi. Sai lokacin Asiya ta fahimci sharrin da aka yi mata ta daga ido ta kalli Anty sai ta saki wani murmushi irin na takaici. Tace tanan aka sake bullo min? Ta je gaban mutumin ta kalle shi. Ina son ka fadi tsakanin ka da Allah ka taba ganina? Ya fashe da kuka tare da fadin Asiya kalli ki gani kefa ki ka ce inzo gidan ki ke kika ce mijin ya tafi kasuwa amma shine kike alaye kamar baki san komai ba. Zufa ta karyo wa Asiya lallai sun tsara abin su. Ta kalli Halifa Dan Allah Yaya kar ka yarda da shi wallahi ban san shiba.
Anty tace amma wannan yazo gidan nan ba so daya ba akwai ranar da na ta tambaye shi ya ce min yayanku ne, to amma ganin yadda in ya fito yake sanda shiyasa na kasa yarda da shi. Halifa wanda takaici ya hana shi magana ya fidda hannu ya wanka wa Asiya mari yace kinsan tin yaushe nake a gidan nan tun ina fita kasuwa Anty ta kira ni tace ga wani ya zo tana ganin shi yana yawan zuwa, har nace kila Dan Uwa ku ne sai kuma na kasa nutsuwa kasancewar yadda mata suka koma a wanna zamanin. Nayi awa daya ina jiran fitowar shi sannan ya fito daga dakin mu dakin auren mu Asiya yana gyara wando ya dakko takalmanshi a inda ya boye ya saka ina Kallon shi ba zan iya barin shi ya fita ba, ni ne nayi masa wannan dukan. Sai Halifa ya fashe da kuka. Asiya cikin firgici da tashin hankali, ta kama hannun shi tace "Yaya kar ka yarda wallahi wannan shiryayyen al amari ne ka yi tunani sosai wallahi ni bacci nake ina kwance a dakina wannan hayaniyar ce ta farkar da ni. Halifa ya hankade ta da karfi ta fadi, yace ki daina taba ni hakikar ke abar kyamace,kin bani mamaki. Zafin maganganun Halifa sun fi mata zafin faduwar kuma ta tabbatar Allah ne kawai zai wanke ta. Sai lokacin ta soma kuka tana furta Allahumma ajirni fimusibati. Ta mike domin bata da sauran wani abu da zata fadawa mijin nata giyar kishi da bakin cikin abinda ya gani ke dibar sa, ta yi masa uzri a yanzu tasan lokacin yi nadamar hakan zai zo a gaba. Bazata yanke hukunci cikin fushi ba, amma tasan auren ta ya gama lalacewa.
Ta mike da nufin ta tafi dakin ta ta saurari hukuncin Ubangiji sai taji ana ku rike shi ta bishi da kallo ya kama bishiya ya haye katanga ya dira ta baya wanda kafin a zagaya ta tabbata ya gudu.
Ta zauna akan kujera ta fashe da sabon kuka. Tana fadin Allah yau kuma da wannan na wayi gari ya Allah! Allah ka kubutar dani kamar yadda ka kubutar da Annabi Yusuf daga khaidin mata. Allah ka wanke ni kamar yadda ka wanke Uwar muminai Nana Aisha daga sharrin masu sharri. Alwala ta yi da ta samu sanyi a zuciyar ta. Ina ma ace mafarki ne.