Sashe 44
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana zaune tsakar gida ta zabga tagumi Sulaiman ya shiga ya sanar mata zuwan Halifa. Inna tace To kuma me ya zo ya yi min bayan ya yi min silar diyar tawa. .Sulaiman yace Inna duk ba wannan bane ki saurare shi muji abinda ya kawo shi, domin shima yana cikin tashin hankali yau din nan ya dawo daga Dubai ya kasa hakura gari ya waye ya taho kuma kin san bai fa gama abinda ya kai shi ba ya dawo. Inna tace "Ummm Ai sai ya shigo din muji kuma wace karyar zai yi min.
Asiya ta ce kai a zo har Unguwar nan in tafi banga Inna ba,kai gaskiya dai da sake, ta duba lokar mota ta dakko face marks ta saka ta fita tunda kayan jikinta irin rigar nan ce wadda ke hade da mayafi ta san ba wanda ya san ta da kayan. Unguwar su ce ta san duk wani langu mara haske dan haka ta sakada ta isa kofar gidan su har ta ci karo da Abba suna fada da wani yaro yaki kamar ta raba su sai kuma ta tuna, ya sheko da gudu ya bige ta ya waigo yana fadin yi hakuri,ta ki kallon shi amma shi sai ya tsaya yana kallonta ta dan waigo ta ga ya tsaya kamar yana son ya gane ta sai kawai ta wuce gidan ta yanke wani lungu ta tsaya, ta dan leko sai taga shima ya biyo zai leko lungun sai kawai ta ci gaba da tafiya.Taji ya daga murya yace "Asiya! Asiya!!! Kai gaskiya sun yi kama ashe ba ita bace." Ya fada tare da juyawa. sai da ta tabbatar ya fita a lungun ta fito ta fada gidan su ta makale a soro. Tana jiyo yadda Halifa ke yi wa Inna rantsuwa da abinda zai kashe shi cewa bashi da wata masaniya akan sakin. Inna kuma ta dage akan cewa gaskiya dai Asiya ta saku duk ranar da Allah ya bayyana ta to gaskiya dai ba matar shi bace. Cikin dai in ka yarda na ka ne to ba maganar kotu. Halifa yace Inna "Dana ne kuma mata ta ce, Asiya Allah shine ya tsare ni da ganin ranar da zan furta kalmar saki ga Asiya, me ma zata yimin har haka,wallahi Inna makircine kawai na wadan da ke bibiyar mu.Abinda kawai za ayi shine in har zaki gane Yaron da ki kace ya kawo sakon to abin zai zo da sauki zan gano wanda ya rubuta wannan takardar.
Inna ta ce "Zai wuce Antyn taka ce ta ke aikatawa,domin dai bata kaunar yarinyar nan,har gidan nan ta zo ta fada min, kai ni ai ko bakai ka yi sakin nan ba, dole ka hakura da yarinyar nan,dan bazan jure ba sam." Halifa yace To Inna yanzu dai ki kwantar da hankalin ki zan yi bincike tare da kokarin gano inda Asiya ta ke, daga nan kuma ko mai zai warware dan Allah Inna kiyi hakuri insha Allah zan nemo Asiya.
Tace "Allahu ya bayyana ta. Sai dai fa kamar yadda nace hakuri dai za ayi ko ka ganta yadda yan uwanka basa sonta. Da sauri Asiya ta fita ta koma gurin mota domin kar Halifa ya fito.
Tana cikin motar tana kallon dawowar shi,Halifa namiji ne kamar irin na littafan nan da zaka ji ana fada, kowace mace zata so ace Halifa mijin tane ya kai namiji ko ta ina. Yana ta dorawa yara tare da Abba kayan abincin da ya sai musu ita bata san ma ya siya ba.
Ya rungumo ta bayan ya shiga motar, yace kyakykyawata insha Allah Inna zata hakura amma ba da gaggawa ba, sai dai munbi mun gano kowaye ke aikata wannan sharrin .Asiya tace "To Allah ya tona shi. Ya sake ta suka kama hanya duk sun yi shiru kowa yana tunani.
Halifa ya katse shirun da fadin, "Baby, shin akwai wani wanda ki ke zargi ne ke? Asiya ta dan yi dim sannan tace "Anya kuwa?" Yace Inna ta fada min wasu abubuwa da Anty ta yi miki wanda ni bansan da su ba,kai tsaye Inna tana zargin Anty ce ke shirya duk wadannan abubuwan.
Asiya tace "Gaskiyar magana Yaya ka yi hakuri amma ka binciki Anty sai dai ina rokon ka kabi a hankali kuma ni abinda ya sa kaga ina ta rufe maka komai saboda na ga irin tashin hankalin da ka ke shiga ne game da lamarin Anty. Halifa ya numfasa ya ce Asiya kamar yadda ki ke so da kaunar Inna haka nake son Anty,bansan Uwata ba ita na sani, duk wata Soyayya da da zai yi wa Uwa ita nake yi wa Anty. Amma a wayi gari tana yimin irn wadannan abubuwan kice bazan shiga tashin hankali ba. Ya kai karshen maganar da kai duka jikin sitiyari tare da rishin kuka.
Asiya cike da tashin hankali tace Yaya to ka tsaya muyi magana yi fakin. Bai saurare ta ba ya ci gaba da tafiya cikin wani mugun gudu har gida.
Ko kashe motar bai yiba yafita ya nufi cikin gida. Asiya ta rasa yadda zata yi ta kashe motar cike da tsoro Allah ya sa ta murda makullin sai kuwa motar ta mutu.
Ta nufi ciki sai dai wani abin tsoro ta same shi ya yi fashe fashe ya yi jifa da abubuwa a falo yana dada kai wa bango duka yana cewa yanzu da wa kuma zan yarda in har uwa zata cutar da danta.
Hannuwan shi suna zubar da jini. Da gudu ta je ta kwakume shi ta baya tana fadin haba Yaya sai kace ba musulmi ba, hankade ta ya yi, ta fadi cikin kirsa ta ce wayyo Allah cikina. Da sauri ya nufo ta cike da tsoro yana cewa Baby ya daga ta cak zuwa kan gado ya kwantar kin gani ko shiyasa bana son in raina ya baci a zo kusa dani, me nene tashi babyna kinji ciwo? Ina waya ta bari in kira likita. Baiga wayar ba dan kuwa can ya baro ta mota. Tashi in kai ki Asibiti. Asiya cikin nishi ta kama hannun shi ba zan iya ba ka bari cikin ya dan lafa sai muje.
Ya zauna yana mata sannu ta ja ji ki ta dora kanta a cinyar sa yana shafa mata kai tana nishi har dai ta gaji sai ta yi lamo kamar ta yi bacci, shi kuma yana zaune ya zuba mata ido wai baya son ya motsa kar ta tashi.
Kusan minti goma sai ta dan motsa ta tashi zaune ya kai hannu ya shafa cikin ta Yaya kinji sauki. Ta tura baki,na ji sauki, Yaya ashe zaka iya duka na?" Yace "kiyi hakuri in raina ya baci ne ban iya fushi ba, ki daina zuwa in kinga na fusata.
Asiya Ta ce "To yanzu sai ka tashi kaje a wanke maka hannun ka ko? Yace ai ya daina zuba zan gyarashi yanzu akwai akwatin gaggawa.
Kwanan Anty uku a Asibiti kullum Halifa yana zuwa kuma shine ya biya kudin Asibiti. Bai nuna wa Anty komai ba.
Yanzu abinda Anty ta gane yin amfani da rashin lafiya dan ta tursasa su. Saboda likita yace kar a dinga bata mata rai . Halifa ya sake sai mata gado da kujeru yace Bros ya sai mata TV da sauran su.
Haka kuma ta uzzura batun auran Bros babu dama ya yi gaddama dan tsoron kar ciwo ya ta shi su ke yi ,dan abu kadan sai ta soma jirin karya kamar zata fadi sai an kamata an zaunar.
Cikin Asiya yana ta girma sauran wata daya ta haihu tuni duk wani abu da ake bukata Halifa ya siyo musu shi. A na tsaka da bikin Bros wanda Anty ta matsa sai anyi, ta tilasta ya gyara gidan da Halifa ya bashi nan zasu zauna da amarya. Bros bai halarci komai na bikin ba,yana gida tare da matar shi yana lallashin ta,kukan ta daya ita dai kar ya canja mata. Ya kuma daukar mata alkawarin kar ta tashi hankalinta ita kadai yake so.
Asiya tana kwance jikin Halifa tana mishi mitar ita dai kar yace zai kara aure dan ita wallahi baza ta zauna da kishiya ba.
Halifa yace bazan miki alkawari ba, Mahaifina matan shi hudu,ance har ya rasu hudu ne suka yi masa takaba,kuma ance ko wata ta mutu ko ta fita baya jimawa yake maye gurbin ta. Ya dago fuskarta suna kallon juna yace nima kuma akwai alamar haka Baby in har zaki kula za ki min adalci ga yadda nake damun ki,da akwai wata yadda cikin nan na ki ya girma ai da kyale ki zan yi sai kin haihu.
Asiya ta turo baki tace "Amma ka fadi tsakani da Allah na taba raki ko in hana ka hakkin ka, ko so nawa ka bukata bana nuna gajiyawata." Halifa yace na sani kina kokari,amma ki sani in kika haihu dole mu hakura. Sam Asiya bata san tana da irin wanna kishin ba, ji ta yi wani abu Yama mata tukuki a kirji,ta soma kuka,kamar wasa sai ciwon baya,sai mara. Duk basu san haihuwa bace, dan sun ga wai EDD dinta da saura yana ta lallahi yana fadin wasa ne amma abu sai ta azzara ya ke ga dare Halifa ya kira likita yace ya kaita Asibiti shima yana gurin zai yi wa wata tiyata ne. Asiya ta ji ciwon da bata taba jin irin sa ba, dan haka ta shiga neman yafiyar Halifa da kuma bada sako zuwa ga Inna...........
*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[10/30, 22:19] Ummi Tandama😇: https://chat.whatsapp.com/K4eDi8FhbXk5887RdW2GrQ?mode=wwt
Ganin yadda ta ke shan wahala likitan ya bada shawarar kawai ayi mata aiki ya kara da cewa dama ta yi karama kwarai da haihuwa kawai dai ya bari ya ga ko zata iya haihuwa ne da kanta.