Sashe 31
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya Juya a fusace. Baki Anty ta saki ta bishi da kallo lallai wannan sai ta yi da gaske.
Yana shiga daki ya dauki waya Sam bai damu da hawa Internet ba, amma sai ya kunna data da nufin duba Tiktok. Kiran Bros ne ya katse shi ya daga cikin sauri domin yana bukatar jin ta bakin wani. Cike da tashin hankali yace Uncle me yake faruwa ne dazu maman Nihal take nuna min Matar ka a Tiktok. " Ina zan same ka yanzu? Halifa ya tambaye shi cike da damuwa. Bros yace ina gida kuma kaga muna da tazara Amma mu hadu a zoo road yanzu." To Halifa ya furta ba tare da ya tsaya tunani ba.
Jikin motar Halifa suka jingina inda Halifa ya zayyano wa Bros komai. Ya kara da cewa kasan menene Bros sam zuciyata ta ki aminta cewa yarinyar nan zata aikata abinda ya faru. Tana ta kawo min hujjoji masu karfi, Bros yace "To ina yarinyar yanzu? Tana gidan su. Halifa ya amsa tare da girgiza kai, ya furzar da huci, ya ci gaba da fadin ban so ta tafi ba, abinda ya bashi haushi ke nan na kyaleta ya kamata ta min uzri a lokacin domin abinda na gani ya isa hujja ko a gaban Alkali cewa ta yi laifin. Bros yace Uncle Baka da wata hujja da ka ke fadin ko a gaban Alkali ka yi mata kamun shara a ne. Ina son ka nutsu ka saurari zuciyar ka wadda ta ki amincewa da zargin da ake yi wa matar ka, kuma dorashi da akayi a Soshiyal midiya ya kamata kasan cewa akwai masu yakar ka da nufi aka yi Allah kuma shine ya san masu yin da kuma dalilin su na yi din.
Halifa ya sauke ajiyar zuciya yace yanzu ka bani shawara menene abinda zanyi? Bros yace ka fara kare matar ka daga sharrin yan Soshiyal midiya dinnan Sannan ka sameta ka bata hakuri kuma ka tashi daga gidan nan ka koma gidan ka. Halifa yace tafiyar da ta yi bayan na hanata ya bata min rai sosai har yanzu ina jin haushin abin. Bros yace ka bari nan da sati daya kowa ya huce kai da ita sai kaje ka same ta ku sasanta.
Da safe ya gama shirin fita ya dauki kayan sawar Asiya da wayarta ya je har kofar gidan ya ba wani yaro yace ya kai yace gashi a bawa Asiya. Tana kwance ta kasa karin kummalo ta rasa yadda zata yi tare damuwar ta. Bata San tana mugun son Halifa ba sai yanzu da auren su ke gargarar mutuwa. Ta tabbatar in har auren nan ya mutu ita ma mutuwa zata yi.
Sai ga yaro da kaya niki niki wai inji Halifa. Ta kalli Inna hawaye suka zubo mata tace ya tabbata Haliifa ya gama yarda cewa na ci amanar sa. Inna cike da tausayawa yar ta cikin lallashi tace. "Bana zaton hakan yana nufin ya yarda muci gaba da addu’ar neman mafita ga Allah.
Sallamar Sulaiman ce ta dakatar dani take na fara rokon Allah ya sa tare suka zo da Halifa.
Na fito daga daki ina fadin sannu da zuwa yaya Sulaiman. Ko amsawa bai yi ba ya shiga tambayar Asiya wai kuwa me kika aikata na ganki a Tiktok? Gaban Asiya ya yanke ya yi wata muguwar faduwa, Wani sabon Sharrin ya sauka kenan, ta furta tana Kallon idon Sulaiman. Ya ce kalli kiga ni yadda abin ya yadu mutane sai sharhi suke yi suna kara yada abin. Asiya ta gama kallo gaba daya zuciyar ta tana bugawa da sauri, ta mika mishi Wayar ta koma ta zauna Sulaiman ya ci gaba da fadin wallahi nasan sharri ne sai dai na yi mamaki yadda Halifa ya yarda. Asiya tace dole ya yarda ta fada masa duk yadda abin ya faru da kuma yadda ta sani.
Sulaiman ya yi ta mamaki tare da yi mata addu"a Allah ya fidda ita, sannan yace yanzu ya za ayi da mutanen Soshiyal midiya din nan? Yan jarida ma nasan in suka ji labari sai sun zo gidan nan yadda abin nan ya yadu kyau ki bar garin nan zuwa nan da kura ta lafa. Inna ta fito cikin mamaki tace "Abin har ya kai Haka? Gaskiya dai ina ganin ba sai taje wani guri ba, kawai dai baza ta fita ko ina ba." Sulaiman yace to shike nan Amma ina mai tabbatar miki cewar yanda kowa ya zama dan jarida yanzu ba sai ta fita ba, har gida zaki ga ana zuwa domin gani da kuma jin ta bakinta. Asiya tace inaga zan zauna a daki kawai. Sulaiman ya ce Allah ya kyauta ya fita.
Maganar Sulaiman. ce ta ke neman tabbata, yayan makota suka. soma shigowa daga nan sai iyayen sai kuma ga wani gida radio wai sun zo jin ta bakin Asiya. Ta kulle kanta adaki. Dole Asiya tabi duhun magriba ta tafi gidan wata yar Uwar su a Kurna ta kwana washe gari ta yi asubanci hanyar Malumfashi dangin Innar su.....
*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*
*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[8/6, 20:53] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w
Kwatsam Baba Tabawa ta ga Asiya Baba Tabawa Kanwar mahaifiyar Innar su Asiya ce, itace autar su. Itace ta rike Inna har ta yi aure. Ta jima a Kano lokacin rasuwa da bikin Asiya. Taji mamakin ganin Asiya afujajan ta tabbatar ba lafiya ba. Asiya kam bata fada mata komai ba, sai kuka data ishe ta da shi har zuwa washegari da Inna ta iso ita ta sanar da Baba tabawa komai, ta zowa da Asiya kayanta da wayar ta. Tana hawa Tiktok ta ga har yanzu video dinsu ke tashe dan har wasu sun kafe hoton ta sun hada wata murya tana kuka tana fadin ta yi nadamar yin soyayya da wani bayan ga mijina Asiya ta saka kuka wannan wane irin sharri ne me ta yi wa wani har haka. Ta kashe wayar ta maida ita can kasan kayanta.
Washegari sai Inna ta hada yan komaatsanta ta koma Kano.
Halifa bai san illar yada wannan Video ba sai da yaga yan jarida sun same shi har shagon sa a kasuwa wai suna son su samu labari game da abinda ya faru ga abokai da yan kasuwar su zancen yana ta yawo. Har ya soma tunanin kowa ma shi yake kallo ana ta nuna shi, Hakan ya tilasta masa zaman gida. Bros ya same shi kwance a sabon gidan shi kamar yadda suka yi zai same shi.
Yace Bros Ina ganin zan Dan motsa ko zan samu nutsuwa. Bros ya dube shi zaka motsa zuwa ina? " Ya tambayi Halifa cike da mamaki domin ya san shi mutum ne mai nacin gida. Zan tafi China gurin harkokin kasuwanci na, daga can in wuce Saudiyya inyi Umra, zan dawo lokacin abubuwa sun lafa, ina son ka zama shaida bana zargin Asiya kuma aurena yana nan dana ne a cikin ta., ya zama dole ne in bata rata komai ya lafa ita ma ta huce tukunna.
Bros yace to amma ko zaka bata rata kar ka wofintar da ita, ka kira ta ka sanar mata cewa za ka yi tafiya dan kar ta dauka cewa kaima kana zarginta.
Halifa ya numfasa, Na kira wayarta tun jiya amma a kashe kuma ta tafi gida bayan na hana ta fita kawai sai naga kamar ta soma raina ni, dole ina bukatar uzri ya yin da naga kato ya fito daga dakina. I zuwa yanzu wallahi na gane akwai mai bina da sharri kuma zan kai karansa gurin Allah in naje Umra din nan.
..
Ya sani ina ta zargin kowa. Bros yace To nidai addu a zan taya ka Allah ya bayyana maka gaskiya ka ganta da idon ka, amma ko waye zai zama na kusa da Kai ne wanda baza ka taba kawo shi ba. Halifa ya numfasa sannan yace Allah ya fishi.
Sai ranar da zai tafi Abuja dan ta can zai tashi sannan ya sanar da Anty ta yi mamaki sosai wai yau Halifa ne ya ke boye mata abubuwa, sannan ta kasa fahimtar me yake nufi da matar sa da bai sake ta ba. Tace "Wai Halifa naga duk ka canza min tun da wannan masifun suke faruwa kai ni wannan auran ma gara dai ya kare kaima ka huta." Yace Anty Asiya fa har yanzu matata ce, Na yi tambaya cikin ta nawa ne ko da ta aikata abinda ake zarginta da shi shari'a ta bani ɗan balle zuciya ta taki sam ta amince cewa ta aikata laifin, kuma dorawa da akayi a shoshiyal midiya shine ya sa na gane cewa tabbas wanda ya so ya hanani haihuwa ta hanyar saka mata abin tsarin iyali shine dai ya bata guba dan ta mutu kar in haihu kuma dai shine ya shigar min daki dan ya yi mata sharri zanje na roko Allah ya nuna min wannan babban makiyin nawa ko da a mafarki ne.
Anty ta girgiza da jin kalaman bakin Halifa kamar ya ganeta kuma kamar bai gane ba. Sai ta wayance da fadin "Gaskiya Allah dai ya sa mu gano ko waye in har ta tabbata abinda ka ke zargi haka to kuwa sai na yi shari' a da ko waye. Halifa yace Anty kar ki daga hankali Allah baya zalinci za ayi walkiya abinda ke boye zai bayyana. Anty ta sake zare ido kamar fa ya gane. Halifa dai ya koma ya ci gaba da shirin sa.
Yaje har gidan su Asiya ya samu Inna bata nan haka ma Asiya. Maman Annur ta je aikin gidan aikin ta, sai Abba ya fada masa Inna tana kauye.