Sashe 13
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mijin Anty shine ya shiga da alawa da goro da kuma dabino yana sanar da ita an daura Auren Halifa. Kamar saukar aradu haka Anty da kawarta suka samu labarin, Cikin rawar baki Tace "Halifa munafirta ta ya yi kenan." Kar ki zarge shi. Inji Dady Baban yarinyar ne ya bar wasiyyar lallai a daura auren ko da bai tashi ba, sukuma dangi suka ga da cewar a daura bayan an dawo daga jana iza tunda duk watse wa za suyi ba zaman makoki za ayi ba.
Cike da izgili Anty tace ba dole a watse ba, tunda in sun zauna me zasu ci, sai dai ma su ci da su. " Dady yace Ai dama haka musulunci ya koyar ba a ce wai dan an yi maka mutuwa ba ka zo kana ci da mutane, cewa a kayi mutane su tausayawa iyalan mamaci su basu sadakar abinci. Dan haka na yi waya Singa nace a kawo musu buhun shinkafa da taliya. Anty ta ja tsaki "Wannan Auren ban yarda da shi ba, sannan kuma ka kira waya ka sa a dakatar da kai wani abu gidan. Alama ta rashin sa a ta bayyana ga yarinyar nan ba yar albarka bace, ubanta ya mutu ana maganar aurenta kai gaskiya akwai abin dubawa a lamarin nan. Tsaki ya ja sannan ya wuce.
Halifa suna tsaye da su Sulaiman mutane suna ta zuwa suna yin hannu da shi tare da masa murna. Shi dai amsawa kawai ya ke yi yana dan yake. Kana gani ka ga angon da ba shiri domin sanye yake da jallabiyya mai ruwan kasa wadda yake zuwa masallaci sallar asubashi da ita. Kiran Bros ya shigo cikin sauri ya daga yana cewa Bros ka dawo ne.? Yace na dawo tunda an daura maka aure yanzu haka ina kan titin IBB yi min kwatance in same ka a gidan inyi ta aziyya. Halifa ya yi masa kwatance . Sulaiman ya ce ya kamata mu shiga cikin gidan nan muyi ta aziyya. Halifa yace "Kalli jikina duk da dai gaisuwa zamuyi amma daga ni sai jallabiyar salla.
Asiya ma bata san sun zo ba, sai ji tayi Ana cewa wannan shine angon. Bata ko leka ba dan babu wani abu dake birge ta.
Halifa ya kira Bilkisu ya sanar da ita abinda ya faru ta zube tana kuka wiwi. abin ya zo mata a bazata sam bata taba zato ba. domin Malamin ta ya bata tabbacin cewa Halifa zai dawo fiye da baya kuma za su yi aure.
Sulaiman ya kira sauran abokan su ya sanar da su abinda ya faru,bajimawa suka nufo gidan su Asiya. Daf da magariba Sulaiman ya kira Halifa Dan jin ya ake ciki game da kai Amarya? Yace to shi bai yi wani shiri game da haka ba, amma yana ganin zai fi kyau a bar shi sai anyi uku. Duk da haka Sulaiman yace yana ina za su same shi, yace yana gida.
Can gidan suka same shi ya fito suka gaisa saura suka yi masa gaisuwa da murna ya amsa. Sulaiman yace na so a ce da ka yarda an kai ta yau an wuce gurin. Halifa Yace " Abarta sai anyi ukun kawai zai fi.kafin nan na gama abinda ya dan saura a gidan. Suka amince da haka.
Halifa kwance a kangadon shi, ya rasa wane tunani zai yi tsawon dare har ƙarfe uku, ya mike ya dauro alwala ya fuskaci Ubangiji. Bai tashi ba har aka soma kiran salla ya fita zuwa masallaci, ko da aka idar da salla bai fito ba sai da ya zauna ya yi karatun safe wanda suka saba yi ya gama ya dawo gida kanshi har sarawa yake, idanun sa sun yi masa nauyi, ya kwanta bacci ya tafi dashi, sha daya bugun kofa ya farkar da shi. Sai ya ji zuciyar sa ta yi masa fes ya bude Hafsi ce ta sanar da shi Anty na kira. Tare suka tafi.
Anty tace Halifa lafiya tun jiya nake neman ka. Yace "Ina gida jiya da yamma bakya nan, saboda rasuwar nan da kuma daurin auran nan shiyasa banje kasuwa baa." Ga mamakin sa sai yaji tace "To Allah ya jikan sa, ita kuma Allah ya sa matar gida ce, ga abinci can na sa a dafa anjima zamuje gaisuwa. Ya ce Anty ni gaba daya kuma abin ya dame ni, naji haushin kaina da banyi wa Bilkisu uzri ba. Tace" Halifa ka gane matar mutum kabarin sa, nima shiyasa na zubar da komai Allah ya baku zama lafiya. Yau she za a dauki amaryar ne? "Yace sai ranar uku ni yanzu zan shirya ne in tafi kasuwa. Tace" To bari in shirya mu tafi ka kaimu da abincin kuma ka kara gaisuwa ya kamata ace yau ka hakura da kasuwar kaje gidan ka yini. Yace jiya ban leka kasuwa ba shine dalilin amma ku shirya na kai ku din sai mu kara gaisawa.
Duk an watse sai wasu daga cikin dangi kadan sai makota da suka dan kara shigowa. Asiya tana zaune tana kara tun ƙur ani iya abinda ta ke iya yi kenan ta ji sanyi, sai ta jiyo ana fadin sannun ku da zuwa ku shigo. Ta baza kunne sai taji ana ayi musu shinfida a dakin Baba inda a nan take a zaune. Kanwar innarmu ta shigo tana cewa ku shigo nan, har barin jiki take yi dan ta yi musu shinfida. Hajiya Talatu ce a kan gaban shigowa dakin sannan sai Anty A gigice Asiya ta Mike tsaye.
*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*
*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[5/29, 13:51] Ummi Tandama😇: Suka kalli juna da Anty, ta yi wani murmushi mai wuyar fassara ga Asiya Allahumma ajirni fi musibati Asiya ta fada a kasan zuciyar ta. Anty tace Allah Sarki baiwar Allah sannu kinji Allah ya baku hakuri ina Uwar ta ku? Asiya ta fita da sauri tana fadin Inna kije ku gaisa.
Inna ta zauna daga bakin kofa, suka gaisa. Anty tace "Allah Sarki sannu da kayan lada gaskiya wannan mutuwa ta dake ni ta fashe da kuka. Hajiya Talatu ta saki baki tana kallon al ajabi Anty tana kuka tana fatar hanci ana ta bata hakuri. Lallai akwai wani makirci Babba da ta hada.
Inna tana sharar kwalla tana fadin Kiyi hakuri muma dai hakuri muka yi. Ta ce Ina Amarya mijinta yana waje ta leka su gaisa. Nan take kanwar Innar su Harira ta ce ki saka hijabi ki fita. A soro ta tsaya ta leka, yana zaune a dakalin gidan su Sulaiman yana waya.
ta daure ta fita tana isa ya katse wayar ya kalle ta ta risina ta gaishe shi. ya amsa tare da fadin "Ya hakuri?" tace Alhamdulilah. Yace Alllah ya jikan Baba tace ameen ya rabbi. Ta ce sai anjima ta juyo ya bita da kallo cike da tausayinta. Duk ta kara ramewa dama ya lafiyar giwa. Ta koma cikin gida. Bayan tafiyar su aka yi ta maganar yadda Anty ta ci kuka Ana bata hakuri, nan aka shiga nuna wa Asiya cewa ta rike Anty ƙauna ce ya sa ta nuna kulawar ta gare su. ta yi mata biyyaya kuma ta rike ta tunda ita ce ta tamkar uwarshi kamar dai yadda ta basu labari. Asiya dai tana sauraron kowa amma zuciyarta ta kasa nutsuwa da abinda Anty ta yi, ta tuno zagi da kuma gargaɗin da ta yi mata cewar karta sake ko da wasa ta auri kaninta, ta nuna kyama da kyankyami gare su amma yanzu wai tana kukan mutuwar wanda ta ciwa zarafi. To duk da haka ta kudurce zata yi mata biyayya fiye da yadda aka fada mata..
Halifa yana kwance yana tunanin gobe za a kai Amarya duk da gida ya kammala amma ya san su Asiya ba su da abinda za su zuba a gidan dan haka dole ya yi daya cikin biyu ko dai ya sayi kaya ya zuba a gidan ko kokuma ya bata bangaren bakin gidan tunda bashi da girma abinda Allah ya hore masu sai su zuba mata a gurin. Wata zuciya tace ka zuba kaya kawai. To shi komai lissafine a gurin dan kasuwa. Ya tura oder bata karaso ba, sannan ga wasu kudade da yake jira shiru ba su shigo ba. A haka bacci ya kwasheshi.