Sashe 15
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Halifa kuwa zantukan, Anty sun tsokano mishi abinda ya sha na maganin basir da sanyi, ga hadin maza da wani abokinsa shima ya sa yake ta banka lokacin maganar su da Bilkisu da abubuwa suka cabe shine ya manta da komai, yanzu kuwa kamar ta masa allura, sai dai bisa adalci ya kamata ya kyaleta ko Don zafin mutuwa, dama ba dan ita ya sha ba. Da sassafe Anty ta kira Halifa wai sun kuwa tashi tana son ta zo su gaisa. Yace "Haba Anty zata zo. ta gaishe ki, ai ko gidan giya akwai Babba.
Tace ai bakonka Annabin ka, ni din ma sai inzo..... .
*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,alfarmar following zata ƙare a 10-june-2025, daga ranar duk wacce batayi following ba,sai dai tabi hanya ta biyu, hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank,*
*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[6/2, 18:43] Ummi Tandama😇: Asiya ta idar da sallah ta zauna tana adduo'in fatan Allah ya jikan Babanta, ta yi godiya da ni imar Allah a gare ta, ɗakin nan irin dai wanda take gani a fim. Insha Allah zata jure komai domin ta samu kan mijinta.
Ya shigo sanye da jallabiya ta tashi da sauri sai ya tsaya Kallon ta ya zata wani abu ta gani. Tace Ina kwana? Yace "Lafiya lau ina zaki naga kin tashi da hanzari?" Tace Aljanna. Ya dan yi dim bai fahimta ba. Tace to ance min gurinka zan samu kuma gaskiya ni dai ina son shiga. Ya yi murmushi" Allah ya baki iko.," Tace Ameen kai kuma ka bani dama ba." Na ma baki tunda na aure ki. Yanzu kiyi wanka ki canza kaya waɗanda suka miki daidai zaki sa ki fito ina jira ki a falo. Tace to mabudin Aljanna ta yanzu zan yi yadda kace. Ya fita yana mamakin Asiya to ko dai ba yarinya bace.
Ta saka riga da siket na atamfa ta yafo mayafi ta fesa turare ya kalleta shi mutum ne ma'abocin kamshi. Ya bita da kallo tace a kwai wani abu da bai yi daidai ba ? Ta tambaya cike da salo. Yace babu tashi muje ku gaisa da Anty. Gabanta ya yanke ya fadi. Tace Anty kuma, bata tafi bane? Yace ina zata? ai nan gidan take. Ta hadiye yawu ai ban sani ba. Ta fada in'ina Yace "Menene naga duk kin canza?" Ta girgiza kai, babu komai kawai dai na zata jiyan sunzo ne.
Suna kan gado ita da Hajiya Talatu suna ta zantukan su da suka saba, Hajiya Talatu tana son taji abinda Anty ke boye mata na game da canzawar ta game da Asiya. Anty ta diro da sauri, a a Halifa kune shigo kinji Asiya ta kama mata kafada Asiya ta zube da sauri tana fadin Ina kwana Anty. Lafiya lau zo nan ki zauna bakin gado mana. Asiya ta zame ta zauna kan kafet tare da fadin nan ma ya isa. Hajiya Talatu tace"jiya da aka kawo ki ba'yi irin yadda ake yi in an kawo Amarya a zo a bada amanarki ba,da kinga dangi sosai. " Asiya ta kalleta ta rasa ita kuma wannan din wacece ta kula da wani kallo da take mata irin na ke kuma ke da wa. Anty ta amshe ai ba komai, zata san kowa tunda an zama daya ki saki jikinki kinji Asiya. Ta daga kai alamun to. Anty ta ce yanzu za a kawo miki abin kari, ki zage ki ci kinji ko? Nasan har yanzu akwai damuwar rabuwa da mahaifinki, Kiyi ta masa adduo'in kin ji? Asiya tace to na gode. Halifa yace ni Bari inje inyi wanka. Asiya ta yi zarab ta mike Hajiya Talatu tace ki dan tsaya mana ana miki nasiha shi yaje ya shirya. Anty tace e dan jira kadan.
Daya fita sai Anty ta ce Asiya ina baki hakuri akan zuwa na gidanku dana ci zarafinku lokacin karya aka zo aka yi min a kanku ance ke mahaukaciya ce kina da aljanu. Ni kam ina tsoron cin amana Halifa maraya ne shiyasa. Amma kii yafe min Allah ya huci zuciyar ki, shiyasa nayi ta kuka ranar da na zo gidanku ba yadda zan nemi afuwar Babanku ya mutu shiyasa, ta sake sassauta murya cikin yanayin tausayi, dan Allah kin yafe min?
Zuciyar Asiya ta karye, tana da saurin yarda ga tausayi ba shakka Anty duk abinda ta fada gaskiya ne dan haka sai ta ji ta yarda da Anty, tace Anty ai ba wani abu ya wuce ba komai. Anty tace "Allah ya miki albarka ki rike mijinki Halifa bashi da matsala.
Hajiya Talatu ta fara kokwanto ko dai Anty har zuciyarta tana son yarinyar nan. Asiya ta kalli Anty wannan ma Antyn Halifa ce? Anty tace e amma kawata ce ba wani abu suka hada ba. Hajiya Talatu ta yatsina baki tana Kallon su. Sam bataji dadin wannan yarfin ba, Asiya ta mike tace to bari inje ko ya gama. Anty ma ta mike zaraf ta biyo ta. "Kina jina ko Asiya. Ta tsaya ta kalleta Anty ta ci gaba da magana kasa kasa, nasan kina cike da jimami na rasuwar mahaifin ki, ina so ki kwantar da hankali ki, shi kuma Halifa na san zai miki uzri ki warware. Duk da Asiya bata fahimce ta ba, sai ta gyada kai alamun eh tace yawwa to jeki maza.
Tasamu ya gama wanka yana sanye da shadda ruwan kasa ya yi kyau. Ta yi murmushi haka ka ke da kyau dama, kamar wani Ango. Ya ce "To da wanene in ba Angon ba?" Tace Gaskiya dai kai ba Ango bane. "Dalili?" Ya tambaye ta cike da wani shuki da yake ji. Tace baka ƙiyin sallar ma'aurata ba. Ya rike baki, wai ke me kike nufi ne? " Ta dube shi bana nufin komai wallahi, kawai dai ban so ka ki yarda muyi sallar ba, to kai me yasa baka zo munyi ba baka son zama lafiya din ne kokuwa dai ni ce matsayi na bai kai a yi sallar da ni ba? Ta kai karshen maganar tana dariya. Halifa ya sauke ajiyar zuciya, in an idar da sallar fa me ake yi. Ta girgiza kai bansani ba gaskiya sallar dai ka dai nasan ana yi. Ya yi murmushi ni kuma na san saura abubuwan da ake yi in kin yarda zamu yi to. " Tace Shima din ibada ne? Yace sosai kuwa har yafi salla din ma. Ta saka dariya, to azumi ne? Yace " A'a tace to ni ko wace ibada ce wannan da ba zan santa ba? Ko kuwa zikiri da salati ne? Yace ki dai yarda kawai zaki gani. " Tace to shike nan na yarda amma na so a daren farko mukayi Sallar nan.
Hafsi ta yi sallama suka amsa ta aje tiren a teburin gaban kujera. Sannan ta ce Uncle ina kwana suka gaida. Asiya ta kalleta, tace sannun ki yama ni kuwa sunan matar? Ta tambaya cike da son nuna kulawar ta. Hafsi ta kalle ta kallon ke kuma a su wa, Sannan ta fice.
Halifa wanda bai kula da abinda Hafsi ta yi ba yana bude abincin yace sunan ta Hafsatu muna ce mata Hafsi. Asiya tace Yawwa na rike.
Bayan sun karya Asiya ta na ta jin kuyar cin abinci gaban Halifa har yana tsokanarta da cewa a haka za mu yi sallar ma auratan da ki ke ta fada? Bayan kina jin kunya? Tace to salla menene damuwarta ita kuma.? Yace shikenan har na matsu dare ya yi muyi salla da sauran ibadu. " Asiya ta shiga daki tana yar dariya.
*** *** ***
Wayar ta shiga ruri ta dakko sunan. Sabon malamin ta ne, ta kalli Talatu wadda ke gyara farce, Anti ta kai makura da gajiya da Talatu lokuta da dama tana son sirri amma ta zo ta yi mata katutu, ya ma zata amsa kiran Malam a gaban ta, bayan bata son ta san shi. Wayar ki ake kira fa. Talatu ta fada tare da kokarin leka fuskar wayar. Anty ta dauke wayarta tare da fadin bana son tsegumi Talatu dan Allah tunda an gama biki sai ku hada kayanku ku koma gida kin bar mijinki shi kadai gashi kin gama da shi ba zai iya cewa kala ba.
Talatu ta taba baki shege yi da mai zina, Allah ya sa kema dai naki Mijin a shanye yake, au korarmu ki ke yi ne, to gobe zamu daga mu bar miki gidan ki. Talatu ta fada tana danna Rikodin na wayarta. Ta aje wayar ta mike bari ince Ma u ta hada kayan ta mu wuce.
Tana fita. Anty ta kira Malam suka gai sa, tace yanzu na ga missed call Malam. Yace Kinga da zaki yi wani abu da kun samu biyan bukata da daukaka sai dai yana da wahala. Anty tace menene zanyi? Malam yace ki kawo min yarinyar nan gobe da safe, ya zama ni ne zan fara kusantar ta akwai wani lakani da rauhanai suka bani yanzu sunce in yi biyan bukata da sabuwar Amarya mai irin tauraron ta, da maijego sabuwar haihuwa da kuma tsohuwa muharramata ko Mahaifiyata ko wata yar uwarta. In na yin wannan aikin Hajiya zan samu wasu damarmaki ne da iko, zan iya yi miki aikin da in kina bukatar dukiyar Halifa ta dawo hannunki kaf zata dawo ba lauyoyi ba ko alkalai ne sai sun kawo komai da kan su na game da dukiyar shi sun baki matsawar ki ka tambaya za su baki, kuma ba wanda zai taba tambayar ki ina wata kadara ta sa.