← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 62

Sashe 23

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta kira Hafsi ta ce tattara kan ƙanannan naki da su Nihal da Nur ki kai su shoprite su hau lilo kar ku dawo sai gaf da magariba. Hafsi ta soma murna amma dai Anty da abinda ki ke kullawa, ko wata kyauta kika samu? Ta yi murmushi kawai yau naga ya dace su shakata. Nima zanyi baki ne za su yi wani aiki a gidan.

Suna tafiya ta sake kiran Malam a waya taji ko ya kusa. Yace "A kwatancen da kika bani direban yace muna gab.

Ta fito ta nufi sasansu Asiya. Tana zaune tana Kallon TV Anty ta kwankwasa kofa tare da fadin Asiya. Gaban Asiya ya yi wata mummunan faduwa bata san daliliba sai ta kama fadin La ilaha'illallahul Azimul Halim! La'ilaha'illallahu rabbul arshil Azim!! La'ilahaillallahu Rabbussamawati wa Rabbul Ardi Wa Rabbul Arshil Azim!!

Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*

*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

[7/3, 08:23] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w/9223372036854675807

Asiya ta bude Aunty ta danna kai cikin falon. Tace "Asiya Dan uwan Babanmu zai zo yanzu zan rako shi ku gaisa,ya jima bai zoba a Saudiya ya ke da zama. Asiya tace to amma da yaya ya sani ai da ya jira shi, ko kiransa za ayi?

" Ba sai an kira shi ba... Anty ta katse ta," Ki barshi kawai, ya tafi kasuwarsa shi Halifa ai suna waya. Asiya tace to Allah ya kawo shi lafiya.
Sam bata kawo komai a zuciyarta ba.

Anty Na tafiya ta ji karan mota dan haka ta daga labulen windo dan taga ko waye. Bros ne ya shigo a motarsa Abban su Nur ta koma ta ci gaba da sabgoginta. Ba jimawa sai taji kwankwasa kofa tana budewa sai taga Sadiya su maman Annur harda su Annur din ta zo. Ihun murna tayi ta dane ta. Sadiya cikin dariya tace kai Asiya Allah ya shirye ki. Suna zama ta zubo musu abinci ta hado musu shayi mai kauri, tace su sha inma basu koshi ba zata sake dafa musu wani abin. Ta kira Halifa cike da murna ta sanar dashi. Yace ta gaishe su kafin ya zo.
Sadiya tace kafin ya dawo mun gudu, ina jin nauyinsa. Asiya tace "La shi ai Yaya bashi da damuwa sam dan Allah ku jira shi.

Anty ta gimtse fuska lokacin da suka hada ido da Bros," Uban me ya zo yi yanzu. " Ta furta a zuciyar ta.
Ya zauna yana gaishe ta. Ta amsa babu walwala ya soma bata uzrinshi ga zaton sa dan bai zo kiran da tace tana yi masa ba a jiya.

"Anty Dan Allah ki min afuwa jiya baƙin mu ne na nijar nan suka kwana har goma na dare muna tare yanzu ma ba mu dade da rabuwa da su ba na yo nan.

Cike da kagara Anty tace kaje yau Nima inada uzuri gobe ma yi maganar. Ga zaton shi haushi ta ji dan haka sai ya shiga ba ta hakuri. Ta kalle shi baka gane yaren Hausa ne ko? To baƙi zanyi yanzun.... Ta katse maganar daidai lokacin da kiran ya shigo wayarta. Ta daga tana sake yi wa su Malam kwatance. Ta dube shi "Ka iya tafiya domin zanyi baki.
Ya mike yana fadin ina su Nur ne? Tace Sun tafi can gurin lilo na wasan yara. Mamaki ya cika Adamu yau Anty ce zata ce a kai su Nihal shakatawa. Ya dake tare da fadin To Allah ya dawo da su lafiya. Ni to bari in tafi. Cikin sauri tace "Kaje gobe ka dawo.

Yana fita harabar gidan motar su Malam tana tsayawa. Ya tsaya yana Kallon su Malam ya fito rike da wani abu kamar carbi amma ba irin diyan carbi bane, ya sha wata alkyabba kamar basarake. Bros ya cika da mamakin ina Anty ta samo wadannan kuma. Bros ya mika masa hannu Malam ya dafa hannun sa a kirjin sa yana fadin "Lafiya lau. Hajiyar tana ciki? " Kafin Bros ya yi magana tuni Hajiya ta bayyana tana yi wa Malam sannu da zuwa. Dan haka Bros ya yi gefen matar Uncle dan su gaisa. Anty tace bata nan dama tafiyar ka kayi.
Adamu ya zargi wani Abu tunda ya ga yadda Hajiya take gaida wannan mutum kamar wani abin bauta sai sunkuyawa take yi yaji yana zargin cewa kodai bokane dan ya yi kama da su.

Ya juya zai fi ce sai ga Sadiya da Asiya da kuma yaran za su gaida Anty. Bros ya tsaya suka gaisa sannan ya tafi. Ran Anty ya baci da ganin Sadiya dole ta kai Malam falon ta ya jira ta san yadda za ta yi ta kori bakin. Asiya bata ga fuskar Malam ba amma dai tabbas shine wannan mutumin da Anty ta kaita gurin shi, dan haka ta gigice.

A Ciki ta amsa gaisuwar Sadiya sannan tace wa Asiya ba nace bako zai zo dan ke ya gan ki matar Halifa ya yi murna shine kuma zaki gayyato wa mutane tarkace. "Asiya tace Anty yayata ce fa, Uwar mu daya Uban mu daya ai kuwa ta wuce ace tarkace. Tace to ki min rashin Kuya ina son ki sallame su yanzun nan. Asiya ta bata fuska tace Anty Yaya Halifa yace su jira shi sai dare in ya dawo. Anty tace ok kice kwadayi da maula suka zo. Sadiya ta kalli Anty cike da mamaki tace Allah ya baki hakuri bari mu tafi yanzu. Dama haka Antyn ke so shiyasa ta yi haka a gaban Sadiyar dan ta yi zuciya ta tafi. Tace dadai ya fi miki ta wuce.
Asiya tana ta kuka tana dan Allah kada ki tafi wannan mutumin boka ne zasu cutar da ni.Ta kwashe labarin baya ta fadawa Sadiya tace amma dan girman Allah kar ta fadawa Inna zata shiga tashin hankali. Sadiya tace kira Halifa ki fada masa cewa Anty tace mu tafi saboda zuwan wani bako da zai gana da ke. Asiya tace bana son yin abinda zai kawo sabani tsakanin su ina dai rokon Allah ya sa Halifa ya fahimci wacece Anty. Halifa ya yarda da yar uwarshi, zai shiga tashin hankali sosai in har ya kasance ya fahimci tana cutar da shi. Kawai ki tsaya a nan din in har kina nan wallahi baza su min komai ba.

Sadiya tace danno kiran shi kawai ki bani cikin hikima zan fada masa abinda zai taho gidan.
Sai dai cikin rashin sa a kira biyar Halifa bai daga ba. Dan haka Sadiya tace dole kam in tsaya Allah ne ma ya turo ni, domin ban tashi da niyyar zuwa gidan ki ba, kawai dazu ina dawowa daga gidan aiki sai na yanke shawarar zuwa gidan nan.
Asiya tace Allah ne ya kawo min ke..... "Asiya.! Kiran Anty ya katse mata zance. Gaban Asiya ya fadi, Ta mike tare da fadin gani Anty. Ta shigo dakin ganin Sadiya sai ta yi turus ta daure fuska. Baku tafi ba?
Sadiya tace sai mun yi magariba Halifa yace mu jira shi. Nan take Anty ta rikice ta shiga fadin "Akan me zaki ce wai sai magariba ina ce kanwar ki ce ba yarki ba? Ke wannan ba abin kunya bane? Sadiya tana da wata dabi'a sai ta yi banza da mutum dan yana magana ba lallai bane ta tanka. Dan haka ta inda Anty take shiga ba ta nan take fita ba amma Sadiya sai ta zuba wa TV ido kamar ba da ita ake ba.
Anty ta koma ta kasa shiga gurin Malam tana ta kai da kawowa a harabar gidan, ta dauki lokaci kafin ta dawo ta kira Asiya tace ta zo su gaisa da bako. Sadiya ta kalla cike da tsoro. Sadiya ta daga mata kai.

Yadda Anty ta sata a gaba ne yafi bata tsoro amma ta san Sadiya zata yi wani abu.
Wata kwarya ce a gaban shi cike da wani abu kamar tsimi yace "Zonan yata kinji ko insha Allah yau zaki rabu da duk wasu matsalolin ki. Asiya cike da tsoro tace ai bani da wata matsala anyi min magani a Asibiti. Anty ta daka mata tsawa tare da fadin" Kijini da kyau ki matsa kusa ya yi miki magani ana taimakon ki ke kina ganin kamar cutar ki ake yi. Malam yace yi mata a hankali ai bata san tana da matsalar ba.

Halifa ya kira wayar Asiya bayan ya gama da kwastomomi ya ga kira da yawa. Sadiya ce ta daga tace taje gurin Anty wai anyi wani bako za su gaisa, amma kuma duk fa naga ta tsorata. Yace "" Kamar yaya ta tsorata ki kai mata wayar please. A kulle kofar Anty Na buga ba a bude ba.. Halifa ya kasa nutsuwa. Kira uku ya yi wa wayar Anty bata daga ba.
Chapter 23 · 0% Book details