Sashe 14
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da safe ya shiga ya samu Anty a falo ana yi mata kitso ta can baya ya jiyo hayaniya yace lafiya? Anty tace ango da kanshi ka ke tambaya yaune taron mu na nan tunda yau za a kawo Amarya dukda dai mutuwa a ka yi ai ma Ɗan taru ko? Halifa ya yi murmushi, mata sarakan bidi a. Tacewa me kitson dan tsaya zamuyi magana ta nufi tsakargida tare da fadin Halifa ya zo su yi magana.
Ta dube shi, tace "Ka kai musu makullin gidan ne? Ya yi dan tsaki yace Ni na rasa ma ina za a kaita gidan can ya mata girma sai dai na bata gefen baki sai yanzu nake ganin gaggawa ta da tuni har za a tashi wani cikin kananan gidajan nan na Kundila ya isa a Sakata a ciki . Anty tace zo muje, suka nufi gefen shi, tace dubi dakinka sai anso a kara fenti zata yi zaman ta a ciki in ta kara wayo ta warware sai ku kama can. Ya danyi shiru baya ra ayin zama da matarsa a inda ya yi samartaka. Sai dai dole ayi hakan na wani lokaci. Ya dube ta, to Bari zan kira me fenti in zai yiwu yau din ayi a maida kayan. Anty Tace " Ba zata zo da kaya ba kenan ko yaya?" Ta tambaya cike da kwanciyar hankali. Yace To naga Babansu ya rasu kuma dama yana cikin halin jinya. Anty tace hakane to ka daure ko baka canza komi ba ka canza gado, kayan aikin kicin dai na san ko da sadakin ta zai yi mata.
*** *** ***
Kamar yadda Baban su Sulaiman ya sanar a masallacin sallar asubahi cewa dan Allah kowa ne makoci ana son ya bada gudunmawar abinda Allah ya hore masa za ayi wa yar gidan marigayin kayan daki, abin Allah sai gashi nan da nan an hada kudi masu kauri a ranar bayan gama addu a ya nufi Gwauron dutse shi da daya maƙocin na su inda ya saya mata kayan gado da kujeru katifa kadai ya saya da kudinsa. Innar su Asiya ta saka kuka dan murna ga sadakin ta ya kawo ya danka mata.
Kamar yadda Anty ta tsara hakan ne ya faru, domin da Sulaiman ya kira Halifa yace za a kawo kaya suna son makullin gida, sai yace ai gidan su za a kawo amaryar can gidan ba a gama gyara ba. Lokacin da kayan suka Iso tara da yan jere Kanwar Innar su Asiya itace Amara gashi ta kaunaci Anty tunda Antyn ta nuna kauna da tausayawa dan haka masu jere na yi tace bari taje ta gaida Hajiya mutuniyar kirki.
Gidan cike da mutane Harira kanwar Innar su Asiya ta taje gaban Anty tana mika gaisuwa Anty ta amsa tana kare mata kallo, tace inaga kuwa na san ki ok kawar mai aikin gidan su kawata ko? Harira tace "A a kanwar mahaifiyar, su amaryar. Anty ta kalli Hajiya Talatu, oyoyo sannun ku da zuwa, kai ku bata gurin zama cike da izgili take maganar, ita kuwa Harira dadi ya rufe ta abinka da mutan kauye, sai take jira a bata gurin zama. Hajiya Talatu ta kasa kunshe dariyarta sai da ta sheke da wata dariya tare da wasu ƙawayan su..Anty Umaima kanwar Anty ce itama yayar Halifa ce, sun zo ne kawai dan Halifa amma ko ziyara ta haka kawai ba su cika zuwa gidan Anty ba, yadda ta ke musu gadara akan komai. Ta kalli Harira tace " Baiwar Allah ki koma can gurin jeren naku kar yara su yi muku barna. " Harira tace za ko su iya ta juya da sauri tana cewa Anty Hajiya muna godiya. Anty ta bi bayanta da daƙuwar zagi tare da fadin to ga yan rakiya nan.
Asiya ta fito wanka aka bata sabon Kaya cikin dunkunan da Sulaiman ya yo, ta saka tana hawaye tunda akace ga motoci nan hankali ta ya tashi ta shiga kuka wiwi, Da kyar aka banbareta a jikin Inna tana cewa dan Allah ku barni sai anyi bakwai Inna tace kije gidan ki Allah ya baki sa a. Ta kalli Dakin Baban su zantukan sa suke mata yawo a kai. Inda yake cewa"Asiya bazaki yi da kinsanin yin aure da Halifa ba. Allah ne ya kawo miki shi." A haka aka sa ta a mota sai gidan miji.
Gidan babbane da bishiyoyi a yankin masu hannu da shuni, su Anty ne ke zaune a ainihin gidan ya yin da su Halifa da bros suka yi rayuwar su a gefen daukar baki duk da cewa gidan mallakinsa ne bai taba damuwa da hakan ba. Nan aka kai Asiya Falo ne da daki biyu kichin a falo sai bandaki a dakin da aka sa mata gado. Shi kuma gadon da ya siyo aka sa a ɗaya dakin.
Kamar yadda yake a al ada bayan sallar Isha abokan Halifa har da wasu daga cikin yan kasuwa suka rako shi. Asiya tana zaune ita daya a falo sanye da hijabi ta sunkuyar da kai a haka suka gaisa. Anyi nasihohi suka aje ledojin hannun su suka yi mata sallama ya tafi rakasu. Gaban Asiya ya yawaita faduwa ba wai tana tunanin ko Halifa zai nemi hakinsa ba a a, yaya ma zai karbeta.
Ya shigo da sallama ta amsa tare da bin fuskarshi da kallo ko zata fahimci wani abu. Shima ya kalleta yanayin da ya nuna bai wuce ace kamar yanda yaya zai mu amalanci kanwar sa ba, yace kina jin yunwa, ta girgiza kai alamun a a. Yace ki yi magana da baki mana. Tace "A 'a. Yace me kika ci? Tace" Ba komai bana jin yunwa ne., " Ya ce To, kije ki kwanta,ta kalleshi a wani littafin Hausa da ta karanta ance ango da Amarya suna yin wata salla dan neman samun zama lafiya. Tace" Sallar fa" Wace salla kuma ko bakiyi Isha bane? Tace "Nayi mana naji ne ance ne ana yin salla domin neman zama lafiya." Ya yi dan murmurshi. To kuma gashi ni ban iya ba, ban taba ji ba ma, amma zan tambaya. Tace ka tambaya mana yanzu ance fa a rana irin ta yau ake yi ranar da miji ya fara shiga dakin matar sa, in ya wuce ranar kamar fa baza a karba ba. Dariya ta kufcewa Halifa ya je ya kulle ƙofa. Ke dai ki kira ki tambaya a inda kika ji.
Asiya ta zuba mishi ido cikin mamaki iya gaskiyarta take magana, amma sai taga kamar baima fahimce ta ba, ko kuma auren ta bashi da wani mahimmanci ne a gunsa. Ta sa kai ta nufi dakinta ta cire hijabi jikina ta bude akwati tana duba kayan bacci. Maman Annur ce ta ce mata su zata saka duk in zata kwanta. Lokacin da suke kallon kayan lefen.
Ta saka ta je ban ɗaki ta dauro alwala, ta saba da kwanciya da alwala ta yarda sosai cewa babban tsari ne. Ta mike a kan lallausan gadon, Allah sarki ƴar tabarmarta ta yi kewar ta. Tayi juyi a fili tace Allah ka bamu ni'imar kabari. Ta tuno da mahaifinta wanda yanzu yana can kwance, Allah ya sa yana cikin dausayin Aljanna. Hawaye suka soma kwaranyo mata suna bin gefen fuskarta, kuka take a hankali har bacci ya yi gaba da ita.
Halifa ya shigo dakin, bacci take yi sosai ga iskar fanka ga ta laushin katifa ba sauro. Ya kalli hawayen da ya bushe a gefen fuskarta, sai tausayin ta ya kama shi. Karan wayar sa ya jiyo daga falo, ya tafi ya duba Anty da wannan daren ya furta a fili. Tace Ta katse shi da fadin, "Kana jina ko Halifa nace Dan Allah kar kaji wani iri akan maganar da zanyi maka. Dama zance ne karka takurawa yarinyar nan Dan Allah, ka kyaleta ta gyagije, ga mutuwa anyi mata tasamu kamar sati biyu, ni nasan abincin da za a ke bata yadda zata murje." Maganar ta zo wa Halifa a wani banbarakwai. Yace to sai da safe. Anty tace ina jin dai ka gane me nake nufi?" Yace A haba kar ki damu. Ya kashe cike da mamakin yadda Anty ta iya yi mishi wannan maganar.
Anty ta aje wayar cike da jin daɗin haƙan ta zai cimma ruwa. Saboda malamin ta ya Tabbatar mata da cewa aure ba makawa zai auri yarinyar sannan matsawar zata matsa kar ayi to zata mutu, tauraron ta yana da girma da kuma haske da yafi na shi Halifa, da tazara tsakanin su kamar kimanin Sarki ya ka sa bafaden sa, yace in son samu ne kada ta bari a samu daidai to a tsakanin su, saboda duk ranar da ya sadu da ita sai fa abinda suka gani. Cikin tashin hankali tace Malam yanzu Sai ina saka ido Kenan? Yace ko kusa, aiki za ayi amma yana da sharadi tunda har ankai ga daura aure to ki kwantar da kai ki hana a tare har zuwa daren Alhamis zan hada miki aikin da washegari juma'a zai tafka mata saki.
Kinsan masu irin wannan tauraron da su masu kudi ke hada tsafi ta hanyar dauke musu shi. Shine zaki ga anba yarinya wani abun duniya an karbe mata tauraro ta hanyar saduwa da ita akwai abinda muke sawa su kawo mana muna hada musu asiri da shi. Nima dai ladan aikina shine ku kawo min yarinyar nan zan yi amfani da taurarinta dan samun shuhura. Anty ta yi masa Alkawarin hakan. Da wannan take son hana Halifa aiwatar da komai. da iyalinsa. Ta lissafa auren da Juma a ne, sai aka daura Alhamis ta tare lahadi, zata tsaya tsayin daka dan ganin komai ya kammala.