← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 62

Sashe 18

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Son jin tsegumi me Kekenapep ya ce bata da lafiya ne dama naga da kafarta ta zo? Anty a fusace tace "Shafa kaji mana, ku masu keken nan kun fiye shegen tsegumi gashi bakwa ganin zarau sai kun tsinka." Yace Tofa! daga tambaya? Bani na kar zomon ba. Tace " Ka ga in ka gaji sauke mu. " Daga nan. Yace a a mai ya yi zafi? bai sake magana ba. Sunyi nisa kafin Asiya ta farka jikinta kamar anyi mata duka, ta na son tuna me ya faru amma ta kasa sai wani ciwon kai ta ke ji. Ta kalli Anty take ta tuna sun fita tare sunje gidan wata gyatuma, sun tafi wani kauye nan take komai ya dawo mata sabo. A firgice tace wa Anty me Baffa ya yi min? A tsorace Anty tace ba Baffa bane wani Dan uwan sune yanzu zamuje gidan Baffan. Asiya tace Anty kaina ciwo yake min muje gida kawai, tace ai gidan Baffan hanyar gida ne.

Asiya bata sake magana ba, amma fa tana tunanin abinda ya wanzu ita da tsohon nan ya kamata ta san waye shi kuma ya samu nasarar yin amfani da ita.? A tsorace ta shiga gidan Baffa nutsuwa da kamalarsa ya sa ta dan rage firgici ya yi mata nasiha suka tafi. A zuciyarta kuwa tana ganin ta fada fushin Allah in har wannan tsohon ya samu damar cin zarafinta.

Halifa ya fita kasuwa tun fitar su. ya yi ta kokarin kiranta amma ya kasa samu. Ji yake wata dangantaka ta shiga tsakanin su da Asiya mai karfi. Wata kimarta yake gani a yanayin da ya same ta.

Kira da sakon Bilkisu sun fara sosa masa zuciya har ma ya yanke shawarar saka ta a cikin wadan da ya toshe layin su.

Ya shigo gidan dauke da leda wadda ya siyo kayan marmari dangin kankana. Ganin ya murda kofar ta budu sai ya Tabbatar cewa sun dawo. Kwance ya sameta kan doguwa kujera tamkar wadda aka zarewa lakka. Ta jiyo fuskarta cike da tsoro ta Kalle shi ga hawaye na zuba, ganin shine sai taji wani kwari ta tashi da sauri ta rungume shi kam, tana kuka. ya matseta a jikin shi yana shafa bayan ta, yana tambayarta menene?
ga abin a ranta amma ta kasa fada masa ta kuma rasa dalilin hakan bata san ya zai amshi abin ba. Abinda ta iya fadi kawai shine bazan sake zuwa Unguwa ba. Ya zauna tana jikin shi, ya gyara mata zama a cinyar shi tamkar dai yadda zaka yi wa kara min yaro, cike da sanyi murya gami da lallashi yace "Me ya faru a unguwar." ta girgiza kai, nifa ina jin tsoro. "Na me" Ya kuma tambaya. cikin sauri. Ta girgiza kai alamun babu. Abin mamaki ta hanashi motsi ko ina, hatta salla magriba da isha i duk agida ya yi suka yi tare abinci kuwa kasa ci ta yi dan haka shima bai iya cin na kirki ba. Ya rasa dalilin faruwar duk wadannan abubuwan. Ya tofa addu'o'i a ruwa ya bata ta sha ya shafe mata jiki suka kwanta ta kudundune masa ajiki kamar yaro irin mai kiwar nan anzo cikin mutane.

A haka suka kwana da safe, yace su je su gaida Anty Ya kula kamar ta dan tsorata amma baice komai ba. Anty ta na falo zaune Halifa yace Anty lafiya kuwa yau da sassafe a falo jiya na dawo na samu wannan agigice kamar wani Abu ya sameta. Anty wadda ta yi kamar mara lafiya ta kalli Halifa ta kuma kalli Asiya, cikin tsana " Matar ka tana da matsalar aljanu ta tayar min cikin a daidaita kamar matacciya muka dawo. " Sannan ina son zan maka wata tambaya ta dan bamu guri. Asiya ta mike da sauri ta fita daga falon domin zuwa yanzu tana zargin Anty kuma tana son sani waye wanda suka je gurin shi. Kamar ta tafi sai ta dawo bakin kofa ta makale. Anty tace" Halifa yarinyar nan da nace ka kyale ta sai ta warware ashe abinda nake tunani ba haka bane, yarinyar nan ta gama lalacewa tun a waje, abin ya dame ni kwarai.

" Halifa yace kamar yaya ban fahimta ba? Tace jiya muna cikin a daidaitasahu sai muka tsaya a danja, wani yaro yana cikin dan sahunsa ya kwala mata kira Asiya gaba daya sai naga tana Kallon shi ta gigice, ta tsorata amma sai ta ki ta kula shi, sai yace ke Asiya ni zaki yarfa dan kinga kinyi aure to kije dakin Bangis ki dauki breziyar ki da fant. Tun daga jin haka shike nan na dauki salati yarinyar nan ta rikice ta gigice ta fita hayyacinta ta tada min aljanu har muka zo gida.

Halifa ya yi shiru yana mamaki tabbas ya sameta a rikice to kuma dai duk da bai san ya 'ya mace ta ke ba sai a kanta, irin wahalar da suka sha ita da shi har rauni yaji mata, shima yaji dan rauni irin kuka da neman dauki da ta yi gaskiya wadda ta taba sanin namiji hakan baza ta faru gareta ba.

Ya kalleta Anty kinsan mutane da sharri ba mamaki kazafi ne kawai, tace "To ai zaka gane hakan dan kuwa zaka sameta fanko ragowar maza. " Yace Dan Allah Anty a bar wannan maganar duk shirme ce, ya mike ni bari in tafi. Asiya ta wuce da gudu cike da mamakin wannan sharrin da Anty ta ƙaga mata bayan ta kai ta gurin wani tsoho zai yi lalata da ita, ko ma ya yi shine abinda bata sani ba har zuwa yanzu kuma shine abinda ke firgita ta, duk da ta duba jikinta babu wata alama da ke nuna an kusance ta, amma fa tana zargin kanta.

*** *** ***

Ya zuba mata ido, Anty ta jefa mishi shakku, domin nashi ganin babu wani dalilin da zai sa Anty ta yi mishi karya ko ta shirya labarin da ta bashi, tsorata da firgita da Anty ta yi magana gashi ya gani. Yace Asiya fada min jiya da su wa kuka hadu a dan sahu suka miki magana? Ta girgiza kai, ni bamu hadu da kowa ba babu wanda ya yi min magana mai kama da wannan.

Ni da muka tashi kai tsaye gidan wata dattijuwa mukaje har ta bani kudi gasu can a kan gado, sai muka je wani kauye tafiya mai nisa gidan wani tsoho yace in zauna akan buzu in rufe ido ya soma zagayani Ina ta adduo'in. Ta fashe da kuka cikin zakuwa Halifa yace ci gaba ina jinki. Ta bashi labarin abinda ta sani duka.
Halifa ya girgiza kuma ya kasa yarda da abinda Asya ta fada, kamar yadda ya kasa yarda da abinda Anty ta fada, sai dai Anty ta fi Asiya hujja tunda ga yadda ya sameta, to da labarin wa zai yarda a cikin su. Iya sanin shi da Anty mutuniyar kirkice ya zata kai amaryar sa ayi lalata da ita, ko dan ta tona mata asiri shine zata kirkiri labarin karya ta ce anyi?.

Ya zauna ya tausasa murya Asiya ki fahimta bana zargin ki domin ni a budurwa na same ki, ko kin taba zuwa dakin wani ya yaudare ki amma bai samu nasara ba shine ya ke son ya fallasaki a gaban Anty, shine ke kuma yanzu ki ka kirkiri labarin da kika bani dan ki kare kan ki.?
Asiya Ta yi shiru tana kallon shi. Yace haka ne ko? Tace " Hasashe ka yi ko tabbaci ka samu? Dan Allah inyi maka wata tambaya? Yace ina jin ki. Menene alakar labarin da ta bayar da kuma wanda na ba yar ta ina suka yi kama?" Ya danyi shiru sanan yace duka labaran suna magana ne akan ki da kuma yin amfani da ke. Ta ce "Ka wai ka dauki labarin da kake ganin shine na gaskiya a cikin guda biyun ka yarda wanda ka ke ganin shine ba na gaskiya ba.

Allah shine mafi sanin gamshashshen labari,ina ganin zaifi kyau mubar zancen a haka. Ya yi shiru cike da damuwa. Dole ya goge shakku ta hanyar bincike...

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*

*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[6/14, 21:18] Ummi Tandama😇: Gaba daya Asiya ta gama gane cewa Anty har yanzu bata sonta kuma ta shirya mata gadar zare ne domin ta hau ta fada. Sai dai shi Halifa ba zai fahimci haka ba, da alama ma bai san wacece ainihin Antyn ta shi ba. Sannan ba zai gane ta da wuri ba, domin kuwa ya yarda da ita sosai. Dole ta dage da adduo'i akan Allah ya kare ta daga sharri da kuma makircin ta.

Bros Adamu ya ɗakko maman Nihal daga Asibiti sunje awo,danja dai dai kofar famfo ta tsaida su kamar ance waiga Hafsi ta hangi motar Bros da wata mace a ciki tana shan mangwaro, kamar Maman Nihal take gani amma bata san ta da kayan jikin ta ba, suna hira suna dariya. Tana tunanin ta fita daga Dan sahun taje dan ta tabbatar da abinda idonta yake zargi sai aka basu hanya.

Da ita kadai ce ba wasu fasinjan sai ta bisu. Har tsuma take yi ta isa gida ta bawa Anty labari.

Wani abu taji tun daga yatsanta har tsakiyar kanta. Adamu tare da Matar sa wannan wane irin sabon bala'i ne!! Ta mike jiri ya debeta ta koma da sauri yaraf ta fada kan kujera. Hafsi tace "Anty kiyi a hankali fa,ba zai kashe mana ke ba." Anty ta sadda kai tana tunanin ta ina zata fara, da wancan aikin na gurin matar Halifa ya yiwu da ko shakka babu zata samu iko mai karfi wallahi da sai ta lalata rayuwar matar nan,.
Chapter 18 · 0% Book details