← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 62

Sashe 39

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Talatu ta ja tsaki karya ki ke ashe ba tsoron haduwa da shi ki ke ba,in kuma ya fito fa. Cike da kuri Anty tace sai me? Ta tsaya inda ta saba yi masa labe, waya yake yi da alamu da lauyan shi yake yi.
Taji yace Barrister mu bar Zaman zuwa ranar litinin. Halifa ya fada yana tari. Ya dan jima yana tarin kafin daga bisani yace Barrister zai fi kyau haka zan kira jimawa mu karasa. Bai saurari amsa ba ya kashe wayar. Cike da tashin hankali ta isa dakin ta. Ta samu Talatu har ta cire riga zata shiga wanka, Anty ta shigo tana fadin "Wata sabuwa na shiga uku Talatu cike da tashin hankali. Hajiya Talatu cike da fargaba tace 'Me aka yi ne Sahiba Anty tace Naji Halifa ya na waya wai za su zauna da lauyoyin sa ko dai zai amshe duk dukiyar shi ne ya koma yana sarrafa su, in kuwa haka ne yanzun ne daidai lokacin da zan mallake shi. Hajiya Talatu tace baki yi tunani akan ko zai kwace wannan gidan yace ku tashi ba? Ya amshe dukiyar sa ta hannun mijinki danki Adamu ?"Anty ta zabura tana kai komo. Ta gaigiza kai,ko a mafarki Halifa ba zai aikata haka ba. Yanzu kin kara jin maganar akwatunan...... maganar ta katse lokacin da idanunta suka sauka akan gurin da akwatunan suke, shakku ya dar su a zuciyarta. Ina akwatunan ta furta a fili Hajiya Talatu ta kalli gurin da sauri,tace "Lallai kam hankali shi ke gani,Talatu ta furta ta mike ta nufi gurin tana fadin Sam ban kula da ba wani abu a dakin nan ba. A gigice Anty ta fita ta nufi falo tana kira Hafsa. Hafsa ta fito a gigice tana fadin "Lafiya Anty? Tace Halifa yaushe ya kwashi akwatunan shi?Hafsi ta taɓe baki wallah har kin tsorata ni. Da rana ya kira su Anty Umma da su Maman Nana suka raba suka tafi."

Anty ta kara zaro ido bai taba ba kannenta wani abu ba shawarar ta ba,bare abunda yake dakin ta. Anty tace "Lallai sabon abu to ba matsala nima na kwashi rabo na ,gara ma ace su ya ba da ya ba waccan shegiyar matar tashi ko da dai na gama da babinta fatana su fusata su kai shi kotu kafin ya motsa na saka lauyoyin da za su ji min da shari ar, ta dubi Talatu Ina alfahari da lamari da ke.

Hajiya Talatu ta ce 'Ni kuma fargaba ne ya cika ni, barin in hada kayana asubahin fari zan dauki hanya in tafi gidana sauran bayani zamu yi a waya tunda na miki me wuyar.Hafsi ta ce "Gara kam ki tafi domin wani huci na ga yana yi yau din nan yana cewa Anty Umma ku raba kuma yan uwana ne,kuma daga yau kowa babbane a cikin ku duk mai son wani abu ya kirani kai tsaye duk daya ku ke da kowa." Anty ta zauna ragwaf a bakin gado, lalacewar tawa har ta kai haka a gurin Halifa? Tabbas sako ya bada kuma ya iso,zan kuma same shi har dakin sa. Ta mike fuuu ta nufi dakin Halifa amma sai ta hange su tsaye da Dady suna tattauna wasu zan tuka da zata so jin abinda suke cewa. Kai tsaye ta nufi gurin su,abinda ta iya ji shine insha Allahu Dady ranar litinin a office din Barrister Sani makoda. Sai Dady yace Ina fatan dai lafiya in kuma maganar kudi ne in taho da listening abinda ke guri na.Halifa yace ka yi hakan ma,domin maganar ta shafi hakan. Shima Bros na sanar da shi. Halifa Anty ta kwada masa kira cikin tashin hankali .Ya kalle ta duk da duhun magariba tana iya kallon yadda ya daure fuska yana kallon ta ba tare da yace kala ba.

Tace "Gidan uban wa ka kai Akwatunan nan? Sannan mitin din uban me ka ke hadawa!!!
Ya Kalli Dady sai kuma ya nufi motar sa ba tare da ya yi magana ba. Hakan ya bata kwarin gwaiwar karasawa kusa dashi cike da gadara ta ce Ni sa ar ka ce harda zaka wuce ina yi maka magana? Ya daga Murya "Kama kan ki Anty!! Karfa ki kure ni!! Dady ka fada mata karta fusata ni ba danta bane ni, bata da wani karfi na hani ko Umarni a kaina fa!!!!Ya bude motar ya shiga ya tashe ta ya fita da mugun gudu gudu. Anty ta yi tsaye cike da mamakin irin daga muryar da Halifa ya yi mata, har su Hafsi da Talatu sai da suka leko ta window. Dady ya sa kanshi ya wuce ya bar ta tsaye cike da mamaki da tsoro.

Ta koma ta zauna bakin gado suka yi shiru dukkan su. Hajiya Talatu ta mike ta janyo jakarta, ta shiga linke kayanta dake bakin gado. Hafsi Tace "Anty shawarar da zan baki ki rage matsawa Uncle Halifa akwai matsala sosai. Hajiya Talatu ta ce "Kodai ya samu labarin...Anty ta daga mata hannu ba wannan bane, Halifa ne ya dawo asalin Halifansa, fatana malaman nan su dukufa aiki,domin akwai katuwar matsala. Abinda ya daure min kai nake son sani yanzu wane shiri ya ke yi da lauyoyin ? Zaman me zasu yi harda Dady da Adamu? Dukiyar sa yake shirin karbewa ? Ina son sanin wannan amsar.

Hafsi tace to Anty kije ki tambayi Dady mana bazai rasa sanin wani abu ba. Zaraf ta mike kamar mai jiran madafa ta nufi dakin Dady.
Yana waya daidai lokacin yana fadin To da zaki barsu a gidan ko zaki rufe su ta baya ne? Ya danyi jim sannan yace, ok tunda Shafa tana nan shike nan kuje sai ki min message zan tura miki kudin Allah ya bashi lafiya da safe in na fito masallaci zan zo inga jikin nashi. Yana kashe wayar ya dago kai suka yi ido hudu da Anty.

Duk da faduwar gaban da Dady ya ji amma sai ya dake, maimakon ta tambayi a binda ya kawo ta sai ta bige da tambayar Da wa kake yin waya? " Baki sansu ba. Ya bata amsa a
takaice .Ta danyi tsam kamar me nazari . Sannan ta taɓa baki tace Halifa ya ke nufi da yace Me Halifa yake nufi da yace ku hadu ku yi mitin? Me yasa baki tambaye shi ba? Ya fada cike da daure fuska. Tace Au me kake nufi wai kaima kulle ni zaka yi? Dady ya zauna bakin gado "Dan Allah kije bacci nake ji."
Ta fita tana huci ta zauna bakin gado inda Hajiya Talatu da Hafsi ke jiran ta. Hafsi tace Anty karfa ki saka wa ranki damuwa ki zo ki kwanta ciwo. Amma me Dady yace?

Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce wai ni kuwa Hafsi Babanku na da yan uwa ne a nan Unguwar? Hajiya Talatu tace kaji wata maganar kuma an tambayi wani abu kema kuma wai kina tambaya..
Anty tace Talatu Alhaji na samu yana wata waya wadda ta daura min kai,shine nake tambayar ko yana da wata yar uwa na manta.

Hafsi ta kalle ta "Me yake cewa,da wata yake waya wai Bintu. Hafsi ta sa dariya Anty kin manta ne da matar Abokin shi marigayi Bintu matar Alhaji b
Baita.? Anty ta taba baki. "Wallahi shaf na manta, yana taimaka musu, ni kinsa ko a matan abokai in har baza a kira ki ki amsa ba to hanyar jirgi daban da ta mota. Ta sauke ajiyar zuciya dan jin hasashenta bai tabbata ba. Tace Dadyn ma yaki fada.

Halifa tafe yake ko ta kan shagon Sulaiman bai bi ba ya nufi gidan su Asiya yana son zuwa ranar litinin ta tare a sabon gidan shi insha Allah.

Gidan nasu a rufe da wani dan karamin kwada hakan yana nufin basa nan. Ya kira wayar ta kamar kullum a kashe sai yaji zuciyar shi tana hasala dan haka sai ya juya ya dauki motarsa ya tafi.
Kasuwa ya wuce rai babu dadi, saidai yana zuwa yaran shagon suka bashi wata takarda inji wani mutum yace daga Kotu. "Kotu! Ya furta cike da mamaki bashi da abokin rigima ko daya waye zai yi karar shi.

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*

*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[10/1, 10:07] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w

Halifa ya sha mamaki ganin wai Asiya ce ke karar shi, ya shiga shago ya zauna duk da sanyin A C hakan bai hanashi zufa ba.

To me ya yi mata har da zafi haka zata yi kararsa?
Bayan shi da ta yi wa laifi yace kar ta fita ta fita,kuma taki yarda su hadu,ta tafi wani gari duk bada izninsa ba, sannan ya nemeta a waya duk abin ya gagara yaje gidan ma basa nan,shine yanzu kuma zata tsaya da shi a gaban kotu, gaskiya shi kam ba zai tsaya da ita a kotu ba,sai dai ta fadi duk abinda take so alkali ya yi mata kawai ya hakura, dan kila saki take nema,sannan zai dauki nauyin cikinta amma a sani da ta haihu zai amshi dansa.
Ko da ba su yi soyayya ba,tana da wani mahimmaci a gare shi,tana bai taba sanin mace ba sai a kanta,kuma ita ce kadai ta ganshi a wani yanayi da ba zai iya fassara shi ba.

Ya mike ya fita a shagon yaje mota ya zauna sannan ya kira Bros a waya, ya sanar dashi abinda ya faru da kuma abinda ya yanke. Bros ya cika da mamaki, yace "Ka kira waliyinta mana babu mutunci fa kuje gaban Kotu ku tsaya,kuma dole ne fa in alkali ya kira ka kaje,amma in kun samu masalaha a gida sai ta janye batun Kotu.
Chapter 39 · 0% Book details