← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 62

Sashe 11

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kalli Anty wai ina makullan gidan nan ne? me hada sola nan ya same ni a kasuwa dazu, yana son kara sa aikin shi. Tace "Wa zaka sa a gidan? " Ya kalle ta cike da mamaki. Yace Wai Anty meyasa ki ke min Haka fisabilillahi bakwa wani shirin biki kamar yadda kuka fara a farko kin daina tattaunawa komai na shirye shirye ko da yake ni bani da matsala in aka daura aure an gama min komai.
Anty ta ce "Kai ashe yarinyar tana da aljanu hauka tuburan take yi in sun. tashi shine iyayenta basu fada mana ba. Halifa yace wace yarinya ke nan? Tace wadda zaka aura yanzu.
Halifa ya danne mamakin sa yace ni sun sanar dani tun a ranar da nace zan aure ta kuma na musu Alkawarin, zan rabata da su. Anty ta tsaya tana Kallon shi cike da mamakin yadda ta zabga karya kuma ya kare hakan duk da ya sa mata kokwanton ko dai da gaske tana da aljanun ne?. Shi kuma mamaki yake tana da aljanu aka boye masa, ya dai sha alwashin in Allah ya yarda sai ya auri Asiya ko ma wane aibu gareta. Anty ta katse shi to gaskiya tunda tana da larura, ba zai yiwa ka kaifa wannan katon gidan ba, ka kawo ta nan gidan ku zauna a sashen ka har muga kamun ludayin jikin,kada wata rana ta fita ba a sani ba suje su halakata. " Shiru Halifa ya yi can kuma ya ce kawai ki bani makullan zan ga ya za ayi. Magana kamar wasa sai gashi ta watsu a dangin Halifa cewa mai ciwon hauka zai aura

*** *** ***

Asiya ta saka hijabin ya mata ƙato har kasa kasancewar ba dai dai girman ta bane na cikin lefen ne Halifa ne ya kira ta a waya yace ta fito yana gurin shagon Sulaiman zasu unguwar da ya faɗi mata duk da be ce mata ga wajen da zasu ba ya ce ta shirya ne kawai,ta rasa wane hijabin zata saka Inna tace saka na lefenki sai gashi ya mata ƙato tunda Bilki tana da tsawo da kuma kiba, ita kuma yar tsuntsuwa.

Halifa ya fashe da dariya lokacin da ya kalli Asiya, Kingan ki kuwa kamar wata tattabara a cikin leda? Asiya ta yi takwa takwa da fuska, cike da shagwaba tace yaya harda kai a yi min ba 'a ko? " Kamar ya zube damun daɗi, yana son shagwaba sosai abinda Bilkisu bata iya ba ita sai izza. Yace. " Yi hakura kanwata, ni nafi son ki a haka, yadda zan jefaki sama in cafke kayana." Ta sunne kai a tafukan hannayen ta cike da kunya da nauyin abinda ya fada. Yace zo muje tabishi ya nufi wata mota yana yi wa Sulaiman alamar sai ya dawo da yatsan sa. Ta Kalle shi kasa kasa yana cikin motar kwayar idanunta dauke da alamar tambaya. Yace" Shigowa za ki yi mu tafi. " Tace Ina Kenan? Ta tambaya cikin salo. Yace" Saida ke zanyi. Ta kama murfin motar ta bude tare da fadin lahiya lau, inji katsinawa. Ya tintsire da dariya, "Ina matukar samun nishadi in muna tare, da alamu na yi sa ar mace wadda ta iya hira." Ya kai karshen maganar tare da juya motarsa dan fuskantar inda za su bi. Nishadin na ka ai ba zai yi tsawo. ba" Saboda me? " Ya fada yana kokarin tattara hankalinsa gareta. Saboda ga shi zamuje ka sayar da ni. Ya girgiza kai," Ba saida ke zan yi ba, gurin mai magani zamu je." Ya fada cike da son bugun cikin ta. Ta Kalle shi da sauri Wani ne ba lafiya? Ta jefa masa tambaya cikin sauri. Ya Dan yi shiru domin kamo bakin zaren, tana da wayo fiye da shekarunta. Ya yi gyaran murya sannan ya soma magana a hankali, Asiya zan kai ki gurin mai rukkhya ne kinsan in mace zata yi aure ana bukatar ta zama komai lafiya a yi gwajin jini da sauran su," . Ta ce rukiyya ai sai masu Aljanu Yaya ni kuwa tunda Allah bai dora min ba ai sai mu gode masa. Jinin dai muje a gwada dama Innarmu ta yi wannan Hasashen cewa jini zamuje gwaji lokacin da kace in zo. Kuma kasan abin mamakin shine ni A A ce, kasan yadda aka yi na sani wata rashin lafiya na yi, kowa ya ganni sai ya ce sikila ce shine aka yi min gwaji ashe ma nidin AA ce.

Ya kalleta da mamaki " Allah na zaci ke As ce, kuma duk da cewa ni A S ne wallahi ban damu ba ko ke din AS ce na fi damuwa da ace kina da Aljanu amma kin taba yin su?" Tayi dariya nifa ko mugayen mafarkai bancika yi ba domin bana manta adduo'in idan zanyi bacci Allah ya tsare ni da sharrin su. Yace"Alhamdulilah yanzu bari muje gwajin jini." Ta kasa danne Hasashen ta tace. Labari ka samu cewar ina da Aljanu kenan. Ya yi yar dariya." Ina zan samu wani labari kawai dai kinsan anayin gwaji." Tace nasan ana gwaji amma ban taba jin na Aljanu ba, Yayata ta yi aure amma ba ayi mata rukiyya ba, bana son ni da kai mu samu shakkar wani abu tsakanin mu, ko me kake son sani game da ni kar ka damu ka tambaye ni kai tsaye zanyi maka bayanin shi. Haka nan nima zan yarda da duk abinda zaka fada min. Dan Allah kar ka yi min karya a duk irin rayuwar da zamu yi bana so ta sam.
Kunya tana son kama shi lallai wannan yarinyar itace matar da ta dace da rayuwarshi, dole ya yi taka tsatsan ta sake kashe shi da cewa. Ka dai yi min Alkawarin zan rayu cikin aminci ko? Bai amsa mata ba sai da ya yi fakin a cikin asibitin Malam Aminu Kano sannan ya dauki waya ya kira wani likita ya sa a sanar da shi sun karaso yace to ya jira shi gashi nan zuwa. Ya kalleta na miki wannan Alkawarin matsawar ina numfashi. Ta sauke ajiyar zuciya tare da fadin na yarda.
Bayan angama dibar jini suka dawo mota tare da rakiyar abokin na shi tanaji su suna tattauna yadda akayi aka fasa da Bilkisu Abokin yace " Ka samu yar shila. Suka sa dariya yace ka fa yi dabara abokin a in namiji yana da jiki yar shila zai samu, Halifa yace au ni yanzu ina da jiki? Suka yi dariya suka tafa. Asiya dai ta kashe kunne tana jin su.

Wani shagon gyaran jiki na yan birni ya gani akan titin gidan su kawai ya ja birki suka shiga. Yace yana bukatar su yi mata gyaran jiki na amare nawa ne, suka fada mishi farashin daban daban yace mai tsadan nake so amma ta yi kyau sosai, suka ce to zata zo na kwana uku gobe zata fara zuwa, ya basu rabin kudin da suka caje shi, yace sauran sai ya ga yadda sukai mata.
Bayan ya yi mata siyyar kayan kwalama suka tsaya inda yake fakin ya taka mata sannan ya ce to zai kirata anjima. Asiya tun a ranar ta tabbatar rayuwarta ta canza Wai ita za abiya irin wadannan manyan kudin dan kawai a mata gyaran jiki. Gashi ashe Halifa yana da mota, sai taji ta kara aji kuma ya shiga ranta, dan gaskiya bata taɓa sa ran auren mai mota ba, amma ta na mugun son mota sosai.

Halifa ya kebe da Sulaiman ya tambaye shi akan dan Allah ya fada masa gaskiya ko Asiya tana tada Aljanu. Sulaiman yace gaskiya bata da su, ita tace maka tana da su? Yace a a, kasan sharrin mutane wani aka samu ya fadawa Baffa na da kuma Anty. Sulaiman yace shiyasa Anty da Hafsi suka zo gidan su Asiya jiya kenan.? Halifa ya zaro ido, Anty da Hafsi fa kace kai gaskiya ba su ka gani ba. Sulaiman ya ce ni fa na raka su har gidan. Mamaki ya cika Halifa daga Anty har Asiyan ba wanda ya fada mishi. Ko shine dalilin da Asiya ta dage cewa ya mata Alkawarin cewa za ta samu aminci a gurin sa.?"Dole dai akwai wani abu.. Ya yi sallama da Sulaiman ya tafi.

Yan mata ne kyawawa guda biyu suka amsa mishi sallama a Falon Anty, shi bai cika kallon mutane ba musamman mata, dan haka ya amsa sannun da suka hada baki suka yi masa ne ya nufi Dakin baccin Anty. Ya kwankwasa ta ce waye, yace "Anty ni ne, ta fito tana fadin dan Halas ka ki ambato irin albarka kai nake ta kiran wayar ka taki shiga. Ya katse ta Anty me kukaje yi a gidan su Asiya?" Tace zo muje zan amsa maka wanna tambayar daga baya. Kamar ƙaramin yaro taja hannun shi zuwa falo da kyawawan yan Matan ke zaune. Tace duba a cikin su ka zaba dukan su wayayyu ne in sun yi maka duk biyun ma baka da matsala. Suna Jami a ƴaƴan masu da shi ne, kuma'ya'yan kawaye na ne. Ta kalli dayar Amina mike ya ganki. Ta mike tsaye tana takun kasaita, ta zauna, dayar ta tashi ita ma tana rangaji. Anty tace wannan kuma Kamila sunan ta. Ya bita da kallo domin gaskiya tana da kira ta jan hankalin ɗa namiji, ya kasa dauke idanun sa daga kirjinta....

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*
[5/26, 09:17] Ummi Tandama😇: Cike da farin ciki Aunty ke kallon Halifa ganin yadda ya kasa magana, da alamun yarinyar ta dauki hankali sa daga ganin yanayin kallon da yake mata.

Ganin haka yasa ta katse shi da faɗin Amina zo mu basu guri su yi magana. Cikin sauri yace "a a," Gaskiya bana bukatar ko daya ciki su. Ki zo muyi magana ya koma dakinta.
Chapter 11 · 0% Book details