Sashe 51
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Anty tana zaune ta zabga tagumi abin duniya ya ishe ta,wai yau duk takamar ta isarta da ikonta da juya Dady da take yi ita ya yi wa kishiya da wata mara aji. Matar da bata fi ta yi mata wanke wanke ba.
Halifa da take hankoron yadda zata mallaki abinda ya mallaka ta juya ta yi sabuwar rayuwa, abinda ta gina a zuciyarta tsawon shekarun da ta rike Halifa Dady ya rusa komai ya hada ta dashi hatta danta da ta Haifa ya tsane ta. Ta farajin Duniyar ta isheta gara ma ta mutu ta huta.
Katsam sai ga kiran Hajiya Talatu, bata ji wani daɗi ba,domin zuwa yanzu tana jin kunyar faɗin wai an mata kishiya. Talatu tace Sahiba me yake faruwa ne haka ba kya ɗaga waya ta. Anty tace Talatu ina cikin masifa ba karama ba, Me kuma ya faru? Ki bari kawai Me gidan nan ne ya munafurce ni ya yi aure, ta fada mata halin da ta ke ciki. Talatu ta ce "Ba ki makara ba kawata, kishiya dai dama ki saka mata date na barin gidan ki dan haka kar ma ki sata a gabanki, shi kuwa Halifa har yanzu ba shi da mata bare ɗa, kuma duk a ciki ƙoƙarin ki ne haka ta faru,aikin ki ya sa ta haukace ta bi Duniya kin ga ko hakan ma ai nasara ce, ki koma ga malamai ki ki sa a haɗa Halifa da Aljana ta aure shi bazata taɓa bari ya yi aure ba bare ya haihu, sannan ki dage ki mallake shi, farraƙa Dady da matar nan ba wani dogon aiki bane, abin kunya ne su Hajiya Gaji su ji wannan yadda suke gulmarki cewa kin tare gaba kin tare baya."
Anty ta ja tsaki Bana son wannan mafitar.domin sabga ce ta cin kudi kuma bani da su.
"Habiba kina da hanyar samun kudi tun kwanaki na fada miki, kin ki ne da yanzu ba wannan magnar ake yi ba. Tsaki Anty ta ja dan ta tuna abinda Hajiya Talatu ta yi ta bata shawara a kai. Tace dan Allah ki bar wannan maganar domin yanzu ko da mun hada baki yan bundiga sun dauke ni ba wanda zai damu sai su Hafsy ƙilama Dady murna zai yi ya rabu dani. "Ga Halifa? "Hajiya Talatu ta katseta. Anty tace tab ai Halifa yanzu ya fi kowa tsanata. Kwabon shi ba zai bayar ba dan fansa ta, ni dai kawai zan taho wajen ki in dan huta, dan naji Halifa yana fadin zai kira zama ina tsoron ma ko ya gano wani abu ne. Hajiya Talatu tace "Dan wannan ba damuwa zan turo miki kudi sai ki zo mana da shinkafa,kinsan Kano tafi sauki. " Anty ta fusa ta, tace Au kina fada min inzo da abincin da zanci ke nan ko? Ni da kike zuwa gidana ko sanar dani zuwanki ba kya yi sai dai ki diro min fa?" Hajiya Talatu tace "Wallahi Sahiba ba haka bane maida wukas Allah ya kawo ki lafiya." Anty tace na fasa zuwa ma ta kashe wayar.
Hajiya Talatu ta sa dariya ta ce shegiya dadina da ita saurin gano inda mutum ya dosa,kar ta zo da shinkafar aikuwa ta kwashi faten tsaki.
Asiya ta kula da yadda Halifa sam baya son ta kusanci wayar sa, ba kamar da ba in ankira zai ce miko min watarana ma har in yaga wani abu a tiktor zai ce zo ki gani, hatta lambobin sirrin shi ta sani, amma yanzu sai taka tsantsan. Alamu sun gama nunawa akwai abinda yake boyewa dan haka sai ta fara tunanin abinda ya kamata ta yi, dan ta dakile abin da take zargi.Abu dai mai muhimmanci shine ta hadu da Innar ta kafin komai dan haka bari ya dawo.
Abinda ya daure mata kai shine yadda Halifa yau shine har karfe shabiyun dare bai dawo gida ba, mutumin da sai ya dawo gida ma sannan ya fita sallar magriba, ta kira wayar shi yafi sau hamsin amma bai daga ba, kuma ta mai text tana tambayar ko lafiya, amma babu amsa,dan haka ta sawa zuciyarta cewa tabbas Halifa ko dai ya fara neman matan da yace, ko kuma yaje gidan su Fati.
Ta yi kuka har ta godewa Allah abinda ya bata mamaki da ya shigo ya ganta zaune a falo. Wai sai yace "Lafiya ba ki yi bacci ba har yanzu? Ta danne komai ta tausasa murya, ina fa lafiya baka dawo ba,yaushe zan iya kwanciya Yaya ta nufe shi da nufin rungumewa. Sai ya dakatar da ita tare da faɗin muje ciki bari inyi wanka. Kuma sai ya yi gaba ya barta turus a tsaye.
A sanyaye ta bishi ciki tini har ya shige ban daki, ta kalli wayar shi akan madubi zuciyar ta tace kul karki taba masa waya baki san me zaki gano a ciki ba.Wata zuciyar tace ki duba kila ta haka zaki gano matsalar har ki san ta yadda zaki dauki mataki.
Abin mamaki Halifa ya canza lambobin sa na sirri. Ko iya haka hujja ce,ta fada cike da tashin hankali.
Tana canza kaya zuwa na bacci ya fito ta sani yanzu kam in komai bai kawo shi ba jarabar shi zata kawo shi tunda wani sa in ko kwaurin kafar ta ya gani ko ya yi shirin fita zai iya sake wanka.
Amma abin alajabi ko kula hakan bai yi ba ya tada salla ya yi magariba da Isha 'I. Asiya tana zaune bakin gado tana kallon shi har ya idar ya isa gadon Jariri ya sunbace shi sannan ya yi masa addu'a. Asiya jiki ba kwari tace abinci fa? Ya zauna kusa da ita ya dafo kafadarta, shayi kawai zan iya sha.Ta mike zuciyar ta tana fada mata cewa tabbas Halifa ya tara da wata domin ga hujjoji, ya zo da janaba, ya yi wanka hatta sallama hadawa ya yi ke nan tun kafin magariba suke tare, wata zuciyar tace in haka ne me zai hana ya yi wanka acan inda ya yi abin? Halifa yana da kyankyami ba zai iya wanka a kowane irin bandaki ba. Daya zuciyar ta fada mata.