← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 62

Sashe 38

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*

*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[9/20, 15:40] Ummi Tandama😇: Asiya da Sadiya suna tafe fitina irin ta masu ciki ta sa Asiya ta nemi Sadiya da ta yi mata rakiya zuwa gidan wata tsohuwa da suke siyan magarya lokacin suna zuwa primary suna tafe Sadiya tana mitar nisan gidan tana fadin "Allah da ace ke daya ce ba domin cikin nan ba wallahi bazan kama doguwar tafiyar nan ba kila ma muje bamu samu ba. Asiya tace sai mu wuce bakin Asibiti muje rimi can kam zamu samu har a duwa.

Sadiya tace saidai ki biya mana mu hau dan sahu kuma yanzu .ma dare ne bazamu samu ba.

Cak Asiya ta tsaya tana waige waige.

'Lafiya?" Sadiya ta fada tare da dafa Asiya. Tace "Ina jin kamshin Turaren Yaya Halifa, duk yadda aka yi yana nan gurin. Sadiya ta saki baki tana bin Asiya da kallo. Sannan ta taba baki tare da fadin "Waye kuma Halifa?" Mijina Asiya ta fada tare da nufar shagon Sulaiman ta leka shi kanshi Sulaiman baya ciki,ta juya da sauri ta nufi gidan su ta ma manta da Sadiya. Sai biyo ta ta yi tana kwada mata kira.

Ta duba ko ina a kofar gidan tana kalle kalle, bata ganshi ba ta shiga gidan Inna tana tsaye rike da wata farar takarda da sauri suka karasa Asiya tace Inna la.. Lafiya? Bata san me yasa ta faduwar gaba ba. Inna tace Takardar sakin ki ce Mijinki ya kawo. Maganar ta daki kirjin Asiya har ma da Sadiyar duk da ba ita aka saka ba.

Da sauri Sadiya ta amshi takardar ta soma karantawa a fili.

"Ni Halifa na saki Asiya saki uku kuma cikin jikinta ba nawa bane ta nemi ubansa,in kuma bata yarda ba zan shigar da kara kotu. Tun kafin ta kai karshe Asiya take fadin Amma kuwa Inna waye wanda ya kawo wannan takardar? Ta kai karshen tambayar cikin rawar jiki da rawar murya. Inna cike da bacin rai tace koma waye ya kawo ke dai ba ya sake ki ba,ni gara haka da a sabarta min ke,batun ciki kuwa dole ya amsa koda kuwa hakan zata kaimu har gaban alkali ne. Amma zamu fara ta kan waliyyan shi tukunna da safe zan yi magana da Abban su Sulaiman. Sadiya ta sauke gwauron numfashi sannan tace, "wannan zalunci ne aka yi wa Asiya gaba daya tun daga auren zuwa yanzu."

Asiya tace Inna gaskiya ba zan taba yarda cewa Halifa ne ya kawo min ba, domin kalaman da ke rubuce a jikin takardar ba kalaman da Halifa zai yi amfani da su ba ne koda kuwa saki na zai yi, sannan in har Halifa zai sake ni ba zai min saki uku ba.

Kuka ya kwace mata ta fada daki da gudu ta fada kan yar yaloluwar katifarta tana furta Innalillahi wa Inna ilaihirraji un.

Sadiya ta zo ta zauna kusa da ita ta dafa ta cikin sigar lallahi tana cewa, kiyi hakuri Asiya Allah ubangiji shine mai sakayya zai bi miki hakkin ki.
Asiya cikin kuka wiwi take fadin 'Ba zan iya tsayuwa gaban alkali muna shari'a da Halifa ba,ya fi karfin haka a gurina koda kuwa zai karyata cewa cikin ba nashi bane.
Sadiya tace kaji Haukan ba,to wazai yarda da hakan? Inna daga tsakar gida take fadin cewa "Sam bata san illar da hakan zai ja mata ba, ni kuma matukar Ina raye ba zan bari karya ta hau kan gaskiya kuma ta zauna ba."
Asiya ta sake fashewa da kuka tace, Inna , zuciyata har yanzu bata amince da cewa Halifa ne ya sake ni ba,Halifa wallahi ya yi min alkawura da dama yana sona Inna.

Sadiya ta ja tsaki ta fita a dakin da ta shigo dan lallashin Asiya. Inna ma cike da jin haushi tace "To sai ki hada kayan ki ki koma gidan sa ki zauna tunda kin ce ba,zai iya sakin ki ba. Kuma ki rufe min bakin ki kafin ki tunzurani in hau kanki har ke har cikin dake jikin ki,bana son in sake jin muryar ki a gurin nan har ke har cikin naki.

Asiya ta kwanta tana hadiyar zuciya nan take zazzabi da ciwon kai suka diro mata,bata taba sanin tsawon dare da ake fada ba sai a ranar, tufka take tana warwara zuciyarta tana fada mata cewa ba gaskiya bane akwai alkawura masu dama a tsakanin su.To amma ba shakka ta ji kamshin turaren shi a wannan lokacin . Sai taji wata sabuwar kauna da son Halifa a zuciyarta ita kam zataje ta yi idda a dakinta.
Ta tashi ta kalli sadiya tana ta baccinta da yaranta.Da a ce mutuwa Halifa ya yi zai fiye mata akan ace yana raye ita ma tana raye amma basa tare, ina ma ace ta mutu, ta ayyana hakan

Ta mike ta je gurin akwatin kayanta ta dinga daga su a hankali har ta ciro wayar ta. Bata yi mamakin ganinta babu chaji ba,domin iya tsawon lokacin da aka kawo mata bata sa a chaji ba, kuma bata zaton ta kashe kafin ta fita sabgar ta.

Bazata tuna tsawon lokacin da gidan su ya dauka babu wutar lantarki ba tun farkon ciwon Babansu. Kenan ita da chaji sai dai gobe idan ta kai gurin chaji. A fili ta furta Innalillahi wa Inna ilaihirraji un. Hannu ta ji an dafa ta ta baya. Ko bata juya ba,ta san Sadiya ce. Tace "Haba mana Asiya ke da a ka yiwa shedar hakuri da kawaici ya kamata ko bakiji dadin abinda ya faru ba,ki daure ko dan Inna musamman ma da yake bata da ishashiyar lafiya. Asiya ta juyo ta kalli Sadiya. "Maman Annur dan Allah ke kunyi soyayya da Baban Annur kafin ya rasu?" Sadiya tace kin dai san ba auren dole aka yi min ba ko?" Asiya ta lumshe idanun ta, taci gaba da fadin Baki san soyayya ba domin da kin santa ba zaki yi min wannan maganar ba, in da soyayya kuke yi dashi na tabbata da daya mutu da sai kin bishi." Sadiya tace Kina nufin in kashe kaina duk da lokacin mutuwata bai zo ba?
Asiya ta mike tana tangadi ta koma kan katifar bata taɓa zaton Sadiya zata fahimci abinda take nufi.

Sadiya ta ci gaba da fadin ki sani bawai banji mutuwar mijina ba ne ko kuma bana son shi ko kusa, kawai dai tawakkali gare ni. "Baza ki gane ba.' Asiya ta fada tare da kwanciya rigingine ta ci gaba da fadin, ki kwanta kawai. A zuciyarta ita dai kawai zata koma gidan mijinta ta yi idda ko Allah ya sa ya maida ita.

"Ya kamata ki nutsu sosai saki uku ya yi miki,ki kauda kanki daga gare shi karma ki nuna masa kin damu ko da mu kin nuna mana."
Sadiya ta sake katsewa Asiya tunani, da magana kuma kamar ta san tunanin da take yi.

Kan Asiya ya kuma sarawa ashe fa saki uku ne. A fili tace astagfurullah ba shakka akwai wani laifin da na aikata wa Ubangiji.

Kafin gari ya waye Asiya bata iya gane banbancin 7 da 17 . Hankalin Inna da Sadiya ya tashi suka dauketa zuwa Asibiti, likitan ya yi fada sosai akan yadda suka bari jininta ya hau irin haka, ya bukaci ganin mijinta bayan ya ba su gado Inna ta ce shine sillar ciwon saki uku ya yi mata kuma yake da a war cikin ba nashi bane. Likitan ya fusata yace zai hada su da wani lauya mai rajin kare hakkin dan Adam kuma zai taimaka musu dan su kai shi kotu.
Duk da halin da Asiya take ciki bata iya magana amma ta daga yatsa tana girgigizawa alamun baza ta iya tsayawa da Halifa a gaban kotu ba.

Inna tace "Ai ba ta ita zamu yi ba in zamu bi mata hakkinta,makauniyar soyayya ta rufe mata ido.
Likitan yace a kwai yarinta a kanta dan haka baza ku tsaya jin ta ba. Amma yanzu a bari a samu kanta tukunna.

Anty suna tafe bayan sun sauka daga kan dan sahu, gida suka nufa, tun farar safiya suka fita sunje gidan malami ya kusa goma,duk damuwarta akan batun Halifa ne, tana cike da tsoron abinda ya aikata jiya,ta san shi da zuciya ta masifa kuma ta kashe kudi a shekarun baya gurin malamai da dama kafin ta samu aka karya masa zuciya sannan ta samu sassauci,domin in da ne ta yi masa wannan rainin hankalin da kaya samu zai yi ya cinnawa sauran wuta. Kuma ta sa a rufe mata bakin mutumin nan mai kudin da ta karba dan tijara. Hajiya Talatu tace karki damu gashi rabin kudin ma duk sun tafi a malamai, nasan tun yau zamu soma ganin karfin aiki domin mun saka malamai masu zafin hannu.........

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*

*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[9/21, 18:35] Ummi Tandama😇: Ta kalli motar Halifa da ke aje a gurin da yake aje ta, tace yana gida ma wallahi Sahiba har wata faduwar gaba naji kinsan bamu hadu ba tun jiya, bari inje gurin dakin sa inga me yake ciki.
Chapter 38 · 0% Book details