Sashe 27
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani abu ne ya taso tun daga yatsa har tsakiyar kan Anty, take ta Mike tsaye cike da tashin hankali." Halifa ciki matar ka ke gare ta? " Yace Wallahi Anty ashe ma shine yake sata duk Wannan firgicin gamu nan zuwa gidan nace dai bari in fara sanar da ke ne kuma sai kina ta waya. Ta sauke numfashi. "Lallai wannan babban albishir ne Halifa Allah ya kawo ku gida cikin aminci ka yi tuki a hankali. Jifa ta yi da wayar a kan gado tana fadin ya Allah ka kawo min dauki ciki kuma Halifa zai yi ɗa to me zan samu kenan? In yi wahala da shi wata banza ta zo ta haifi Magaji. Ta sake zabura ba zai yiwu ba, gashi Na tura kudin aikin.
Ta dauki wayar ta kira Malamin yana dagawa tace Aiki fa ya jika, yarinyar nan dai ta samu ciki. " Malam yace to menene abin daga hankali? Sai a zub da shi kuma a daure mahaifar ni fa in kina so sai in kwantar da cikin." Anty ta zabura kamar tana gabanshi, tace "A a Malam karka kwantar da shi zai iya tashi, inda za'a iya cire ma haifar cak,sai a aika aljanu su cire su yi taushen su su cinye." Malam ya saki dariya Sannan yace, Kai kina da mugunta sosai wallahi. To ba matsala yanzu dai za a cire cikii a kulle mahaifar kowa ya huta.
Halifa ya tsai da mota bayan ya shigo gidan Asiya zata fito sai Halifa ya ce tsaya, ya kai hannu ya bude motar yace fito. Asiya ta fito suka nufi daki. Kan doguwar kujera ta kwanta ya yace Bari na fadawa Anty mun dawo. Da murna Anty ta tari Halifa tana addu'a sai kuma ta fashe da kuka. Inama Hajiyarmu tana raye. Halifa wanda bai san mahaifiyar ta su ba saidai kaunar ta da yake ji a ransa yace "Allah ya yi mata Rahma amma Anty ni ai kece Uwata, ina jin ki a zuciyata fiye da ita tunda ban shaku da ita ba. Anty cike da jin dadi tace Allah ya yi maka albarka Halifa yadda kake min biyayya Allah ya sa wannan dan da za a haifa maka Shima ya yi maka biyayya. Ameen Halifa ya amsa da sauri domin ji yake kamar daga makogwaron mahaifiyar shi addu'ar ta fito. Anty cike da makirci tace muje in ga jikin nata.
Ido cikin ido suka kalli juna da Asiya a hankali ta furta Allahumma kafini him bina shi"ita. Addu"a ce da malamin su ya basu yace in sun ji tsoron cutarwa daga wani mutum to su karanta masa. Anty ta Iso tana fadin sannu da jiki Asiya Allah Sarki baiwar Allah matar firauna. " Halifa yace Anty ni ne Fir'aunan? Cikin dariya tace" A a kawai dai na tuna da mai sunan nata ne. Asiya ta yi guntun murmushi, tuni ta gane cewa rashin abin fada ya sa Anty fadin haka.
Aka shiga rainon ciki,
Haka dai Asiya ta shiga laulayi komai taci sai ya dawo dole aka kwantar da ita a Asibitin ana ta karin ruwa Halifa kuwa ko kasuwa daina zuwa ya yi duk ya fita hayyacinsa kamar shine mai cikin. Asiya har tausayin sa ta ke ji. Sadiya ce a gurinta Innar su ma tana kai kawo a gurin. Anty kam kullum tana hanya da girki, sai dai Asiya ta kasa yarda cewa Anty tana murna da cikin dan haka ta Kaurace wa duk wani abu da Anty zata kawo da sunan ta ci ko ta sha.
Wannan matakin ya kona ran Anty domin ta lura Asiya ta fake da amai ne dan kar ta ci abubuwan da take kawo mata wanda da ta ci da tuni cikin sai labarin sa. Shi kan shi Malamin ya ji haushi Dan haka yace ta barshi da ita ai dama Wai yaga karamin aiki ne amma zai mata abin da zata yi mafarki kuma da ta farka cikin zai fita. Duk wanda ya yi imani cewa Allah ishashshene babu shakka sai ya isar masa. Abinda Asiya ta dogara da shi kenan.
Kwanci tashi a sarar mai rai inji yan magana ciki har ya shiga wata hudu, duk da irin abubuwan da Anty ke yi Amma ko gezau kuma ta kasa ganewa bare ta daina narka kudinta a bokaye.
Karshe dai Malamin da yaga Anty ta saka masa kuka wiwi tana fadin har yanzu bai biya mata bukatar ta ba, gashi ya amshe mata kudi. Shine ya ce gobe ta dawo.
Wani Apple ya bata yace matsawar ta ci shi to saidai buzunta. Anty ta rasa yadda zata ba wa Asiya Apple. Sai ka wai ta dakko ta Bawa Nur da Nihal tace ga shi maza ku ruga ku kaiwa Antyn ku, kuce Babanku ne ya kawo.
Har ga Allah Asiya ta dauka Babansu ne ya kawo dan haka tuni yawunta ya tsine, ta gatsa hakori tana fadin gashi da zaki ta sake gatsa tana ci gaba da fadin shi Babanku din ya tafi ko yana ciki? Nur tace ya tafi. Nihal tace "Ke Nur sannu da karya, Dady bai zoba yau dinnan." Da sauri Asiya ta furzar da Apple din tare da kokarin kakaro na bakinta.
Su Nihal suka shiga yi mata sannu. Ta soma karanto addu'o'i domin ta gama gano gadar zare Anty ta ƙulla mata kuma ta fada. Da sauri ta dafa cikin ta ta ce Allah ka tsare min wannan kyautar da ka bani, Allah kar ka bar wani ya cutar da abinda ke cikina.
Ta soma jin yanayi Na tashin zuciya da jiri tana daga zaune ta dauki wayar ta da sauri ta danna kiran Halifa, sai a kira na biyu sannan ya daga lokacin muryarta ta fara sarkewa, tace ka zo maza ka kaini Asibiti na ci wani abu ahhh...maganar ta sarke Wayar ta fadi. Ya firgita ainun ya baro kasuwa afujajan tun a hanya ya kira Anty wadda su Nihal suka zo suna fada mata cewa Antyn Uncle ta fadi. Sai taje dakin ta dauke Apple din ta kutsiri mai kyau daidai yadda Asiya ta gutsira ta aje shi inda ta dauki wancan. Ta fice ta bar gidan dan haka Halifa yana kiran ta yace Anty ki duba Asiya bata da lafiya ki yi mata wani Abu kafin in dawo.
Tace "Subhanallah bana gida naje Ƴankaba amma yanzu zan nufi gidan.
Halifa ya samu Asiya tayi amai ga kumfa kuma ta suma ya sunkuceta zuwa Asibiti da gaggawa. likitoci suka hau kanta. Anyi nasarar shawo kan gubar bata gauraye jikin ta ba, sun gano guba taci mai tsananin haɗari wai dan ma bata ci da yawa ba, kuma tayi amai bayan taci din. Halifa ya girgiza kwarai da jin cewa Asiya ta ci guba to waye kenan ya bata guba, a sukwane ya koma gida ya ga Apple din da aka gatsa da kuma wani karami wanda ta balla ta to far da shi ya koma Asibitin ya kaiwa likitan kamar yadda likitan ya bukaci abinda taci a lokacin dan su gwada su gane wace guba ce a cikin nau in gubar da ake da su Dan su san maganin da za su bata ga ciki.
Anty ta shigo tana ganin Halifa agigice tace ina Asiya. Ta so ace cewa zai yi ta cika, sai taji yace tana ciki. Ya tsare Anty da ido Anty waye ya ba Asiya guba.? Ta zabura "Guba kuma Halifa ina za asamu guba?"
To waye ya bata Apple? Tace "Wai kana nufin Apple din dana raba musu aka kai mata nata shine aka samu mai guba? Ya sunkuyar da kai, yana jin zargin Anty a zuciyar sa. Amma wani sashen na zuciyar yana hanashi da cewa Sam Anty bazata yi haka ba.
Ya dago ya dube ta. Ina aka samo Apple? Ji tayi kamar yana tuhumarta kamar yana zarginta. Ta fashe da kuka "Halifa kar dai zargina ka ke yi? Na siyo ne a Unguwa na zo na raba musu. Yace ba shakka sai ya fito wanda duk ya yi yunkurin kashe min mata da yata. Anty tace ni da kai zan kira masa hukuma zo muje in kai ka gurin da na siya. Likitan ya katse su da cewa zaka iya shiga ta farka.
Anty ta ruga tana fadin Allah ka shiga lamarin wannan yarinya. Halifa ya tsaya gaban gado yana kallo Asiya wadda ta kara ware ido tana Kallon Halifa take ta tuna ashe fa ta ci Apple nan take komai ya dawo mata a kai, ta kalli Anty wadda take fadin Allah mun gode maka sannu Asiya. Sai kawai ta ji murmushi ya sauka akan fuskar ta tare da fadin Allah na gode maka da ka sake bani dama ta rayuwa ina me jaddadq imani na agareka ya Ubangijin Musa da Isa ya Ubangijin Sayyadina Muhammad Sallah akai wasallam. Halifa ya matsa kusa ya kara kunne da baya jin me Asiya take fada, ya dai ga ta kafe Anty da ido, zuciyar shi ta darsa cewa kodai Anty tana da hannu a cikin lamarin. Yace me kike fada Asiya? Ta kalli fuskar Anty wadda ta gama tsorata tana fadin me take cewa ne Halifa.
A zuciyar Asiya tace, Anty karki damu ba wanda zan fadawa abinda ki ke yi, bazan hada ki da Halifa ba, amma zai ci gaba da kai wa Allah kara, shine zai tsaya mana.
Muryar Halifa ta katse ta. "Asiya me kike fada? Naga kina murmushi." Can kasa muryarta tace ina son in karfafawa Anty zuciya ne naga ta tashi hankalin ta. Ka fada mata karta da mu in Allah ya yarda tunda Allah yasa na farka to zan tashi. Yace "Sannu Asiya zan fada mata amma waye wanda ya baki Apple mai guba?. Ka bari in samu kwarin jiki sai a yi magana. Yace shike nan. Anty wadda ke a firgice ta tsaya a gefe gaba daya ta sadakar Asiya tana zayya ne mishi abinda ya faru ne, tunda ta kasa kunne amma ta kasa jin abinda suke tattaunawa kasancewar muryar ta ta yi kasa.