← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 62

Sashe 36

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun gama gaisawa Baffa yace Ina son ka fada min abinda ke faruwa a gidanka da bakin ka. Domin na samu labarai marasa dadi daga bakuna daban daban. Nan dai Halifa ya zanyyane wa Baffa iya abinda ya faru na zuwan kwarto gidan sa abinda ya biyo baya na dorawa a waya. Baffa yace to kai ina matsayar ka da yarinyar domin kayi kuskuren rashin rike kwarton kuma kai baka shiga ba dan haka babu wani labari da zaka bada shara a ta karba. Sannan Antyn ka taje da ƴan sanda gidan su matar ka za a kama Uwar yarinyar yan Unguwa suka hana. Kasan da wannan?

Tsaye Halifa ya mike,. Anty ce ta kira wa Inna yansanda to akan me? Baffa yace zauna ka kwantar da hankalin ka. Kamar yadda na fada maka munyi magana da abokina Baban Abokin ka. Gaba daya suna zargin Antynka da yunkurin kashe auren ku, ta hanyar kulla abubuwa. Dan sunce har guba ta bata da sauran zantuka su na mata. Ina son ka kwantar da hankalin ka ka sanar dani kai me ke ranka game da matar ka? Halifa yace gaskiya Baffa bana zargin matata har zuwa yanzu kawai naji haushi tafiyar da ta yi gida ne bayan na hana ta, kuma tafiyar ta ta ce ta bawa masu yada maganar damar bin diddigi da kuma kaga wasu zantuka, da tana gidanta karya ne wani dan jarida ko dan tiktok koma waye ya tinkare ni ko ita tunda dai irin wannan abin ace ya faru da gaske kuma muna tare ai bazai yiwu ba. To da ta tafi ma daga gidan su sai ta kuma tafiya kauyen su duk ba yarda ta. Dan haka sai na barta ta gama yin yadda take so. Amma game da aurena ko cikin ta wannan duk baani da wata damuwa. Sannan ni kaina ina zargin Antyna da wasu abubuwan saidai bana fata zargin ya zama gaskiya shiyasa nake ta gocewa kuma ina ta bata uzri. Domin idan har Anty zata cutar da ni to kuwa Mahaifiya zata cutar da danta.

In Anty bata sona meyasa bata kashe ni tun ina tsumman goyo ba? In Anty tana son kashe ni me yasa ta tsaya ta bani tarbiyya da ilimi bata taba nuna min wani banbancin ba? Wace riba zata samu in ta hana ni zama da mata ta?
Wadannan sune tambayoyina Baffa kuma inka duba zaka ga haka ne. Amma Na fadawa Allah ya kawo min mafita ya bayyana shedanin da ke son hanani zama lafiya da matata da kuma Anty na.

Baffa yace to Allah ya bayyana gaskiya amma ka samu ka dawo da matar ka dakinta ita kuma Antyn taka ka bata hakuri matsalar iyali ba a sako jami an tsaro.
Halifa yace Insha Allah zan tashi in koma can gidana ne kawai maganin fitinar Baffa yace haka ya yi. Halifa ya nufi gida. Anty ta kira mai sayen akwatuna ta zube su a falo suna ta ciniki Hajiya Talatu ma tana son biyu a ciki amma fa Anty tace sai ta zube mata kudi ko kuma idan taga alat sannan zata bada. Halifa ya yi sallama a kofar falo sannan ya shigo kai tsaye....

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*

*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[9/7, 11:02] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w

Kallo ya bisu da shi fuskarshi cike da alamun tambayoyi Anty ta diririce tamike tana fadin oyoyo Halifa Oyoyo Uban masu gida oyoyo uban masu kudi kinsan fa duk yan gidan su masu kudi ne. Har lokacin idanun shi suna kan akwatunan Anty cike da in ina tace "Am dama wannan ne ya wannan irin akwatunan ka ya kawo za a siya kasan baka nan an saka ranar danka Baban su Nihal shine ka ga ina wayata ma ko ina ya jefa ta, wallahi sai kiranta nake yi bai daga ba. Halifa ya kai kallon shi kan Hajiya Talatu wadda ta ke ta kokarin rufe wasu jajayen kayan bacci wadan da yasiye su a wata tafiya da ya yi Chaina lokacin yana kan hada lefe. Nuna wasu ta kalma da aka tura kasan kujera yace, "Harda wadan can takalaman da kayan baccin can duk zai saida? Ba jira amsa ba ya ci gaba da fadin Ni zuwa anjima zan amshi nawa akwatunan da kayan ciki zan kai su sabon gida." To ai suna ciki ko zaka dauka yanzu? Anty ta fada da sauri tare da share zufar data keto mata a goshi. Ta ci gaba da fadin ka zauna mana bari a kawo maka abinci ka sha hanya. Zata yi hanyar kicin Halifa ya ce " A koshe nake Anty karki manta bayan magriba zan kwashi kayan". Ya Juya ba tare da ya jira amsa ba.

Kai kawo yake yi tunda ya shiga falon sa, ko kaffara ba zai yi ba wadannan kayan sa ne, kwanaki ta fada masa ta taba wani abu a kayan ransa ya baci amma ya nuna mata babu komai. Shine yanzu kuma zata sai da akwatu nan. A fili ya furta Allah ya sa dai ba duka kayan ta salwantar masa ba.
Anty ta kalli Hajiya Talatu tace "Na shiga uku kinga wata masifa to yanzu ina zan samo sauran kayan ni Habiba, ko kuwa dai in kira Malam ya rufe min bakin sa. Hajiya Talatu ta ja tsaki" Dan Allah dubi yadda duk ki ka burkuce kika fita hayyacin ki kamar wani ubanki, dan bai samu kayan ba sai ya dake ki? Anty tace "Baza ki gane irin zuciyar da Halifa yake da ita ba, a haka ma dan na saka Malamai sun min aikin karya zuciyar ta sa, ke da dane ya samu kayan nan wallahi sai ya daga mana hankali a gurin nan ko ya kwashi kayan ya cinna musu wuta."

Hajiya Talatu tace, to hakura zakiyi da wancan aikin kenan na Asibitin? Anty ta kalli mai sayen akwatunan tace Inaga kawai kaje. Yace To zan baki yadda kika ce da farko. Anty tace Kai kuma ana ga koshi kana ga kwanan yunwa, duk fa a gaban ka komai ya faru kuma da Hausa muke magana ba wai da wani yare ba. Me siya akwatuna yace Hajiya in kun canza shawara Dan Allah ku nemeni ta wannan lambar. Hajiya Talatu ta yi karaf tace ina ganin abinda za ayi kawai ka bamu kudi in kurar ta lafa kazo ka kwashi kaya. Anty tace "Tabbas domin na san ganin kayan ne ya sa yace zai dauka domin fa tabbas ya san kayan shi ne ba wai ya yarda da abinda na fada bane. Me Siyan kaya yace ina ce nan gidan ki ne? Anty tace. Ban gane ba, yace" "Ba dai nan ne gidan mijinki ba, ko kuwa zan ba ki kudi ne kawai dan tsoro?
Hajiya Talatu tace gidan ta ne ka bamu miliyan daya daga baya sai muyi magana. Yace ai ba kayan miliyan zan siya ba, akwati catai in bada dari uku nake neman ragi. Hajiya Talatu tace ai zamu baka wasu kayan kalli gidan nan fa, ji kayan da ke falon nan miliyan din banza kawai dai wata bukata ce ta gaggawa. Yabi ko Ina da kallo a zuciyar sa yace zai so ma su ki bashi kayan ko kudinsa domin in har abin ya zama rigima sai ya ci ribar da ta linka abinda zai samu in aka yi sabgar lafiya lafiya. Ya Numfasa
Yace to naji zan bada amma in na bada miliyan daya in kudin za a maido min miliyan da dari biyu da hamsin za a bani ko kuma a bani kayan kudi. Suka ce sun yarda nan take yace sai anyi rubutun yarjejeniya bayan sun gama yace Su bashi account number. Kamar wasa ya saka wa Anty miliyan daya kuma ya tafi.

Halifa bai jima a gidan ba ya dauki motarsa ya kaita gurin wanki yana can ya kira Bros ya sanar da shi ya dawo anan yaake fada masa Maman Nihal ta haihu da namiji. Ya yi masa murna ya kuma tambaye shi batun aure da ya ji Anty tana fada, yace tabbas akwai batun ya sanar da shi komai. Halifa yace Kasan kayan lefen mata ta da Anty tace a jinkirta bata sune na gani sun tasa tare da wannan kawar ta ta suna cinikin su? Bros ya saki salati Sannan yace "Amma ka Karbi kayan ka ko?" Halifa yace Tace ba su bane amma dai na san borin kunya ne da dare zanje in ce ta bani wallahi Bros Anty bata taba bata min rai irin na yau ba, yau ne na yi tunanin dama ace mahaifiyata tana raye domin Uwa ce kawai ta san darajar duk wani abu na danta. na ga iyayen da sune ke hadawa yaran su lefe dan su rufa Asiri. Bros yace "Ina tabbatar maka cewa Anty ko ni din ne hakan zata aikata min dubi yadda ta korar min mata." Halifa yace ta yi haka ne dan tana zargin tun da ka auri maman Nihal kasuwancin ka ya tsaya kaga tana fada ne akan son ci gaban ka.

Bros ya ce akan son ranta dai, ni mahaifiyata ce bani da yadda zanyi amma kai yar ka ce zaka iya neman hakkin ka ko nuna mata rashin jin dadin abinda ta yi maka. " Halifa ya sauke ajiyar zuciya yace. Na fada maka ne dan inji sanyi kar kaji haushin magana ta. Bros Yace ba wai bakar magana na fada maka ba Uncle wallahi haka shine gaskiya kaje ka ce mata ta baka kayan ka, bai dace abar mutum ya yi tafiya a cikin kuskure ba. Halifa yace zanga me zanyi.
Chapter 36 · 0% Book details