Sashe 2
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[5/24, 10:05] Ummi Tandama😇: *🧳 HASASHE🧳*
*Sabon littafin*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
*Page 2*
*Zaɓi biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*
Anty ta kalli Baba cike da tashin hankali tace, "Baba wai garin yaya kuka bar Halifa ya yi son zuciyar sa
Ya zai kai kaya gidan wata wadda ba a san ko wacece ba? Menene asali da tushenta shi kanshi na tabbata bai sani ba."
Baba ta numfasa tace " Habiba ni fa iyakacina kai kaya duk yadda ake ciki da yadda akayi gidan su Bilkisu munyi waya da ke, shi ya zo ya sa abokinshi da Hafsatu sune suka fito da kayan, mu muna waje ma. Anty ta kwalawa Hafsa kira, ta shigo tana cin cincin din da su ka ta ho da shi daga gidan su Bilkisu tana fadin ya yi dadi kyanshi da shayi.
Anty tace Wai Hafsa ya akayi ba ku dawo da kayan nan ba in ma bai amince da sharaɗin da akayi da gidan su Bilkisu ba? Hafsa tace "Anty kinsan Uncle Halifa babu wanda zai saurara in ya yi fushi. Wayata mutuwa ta yi shiyasa ban kira ki ba, ita kuma Baba katinta ya kare. Anty tace Ya Salam! Ta kai ta kawo a tsakar falon ta ce Baba zo kiga kayan da aka shirya tun farko za a kai gidan su Bilkisu.
Baba ta bi bayan Anty zuwa wani daki, akwatuna guda sha biyu blue da pink ga wasu adudu shake da kayan al ada an daure su da madaurin ado irin na zamani.
Cike da mamaki Baba tace Amma me ya hana a kai wadan nan? Hasashe na yi Baba.(, Anty ta cafke tambayar) . yadda suke nuna wa Halifa Kauna yarinyar nan kamar ta kawo kanta, sai na kalubalanci Halifa cewar yarinyar nan da bata kula yana samu ba da ba zata yi masa irin wannan son ba, sai yace sam ko bashi da ko sisi zata zauna da shi. Dan haka sai nace masa kar a kai kayanta wancan da aka kai na iyayenta ne da sun karba sun yi godiya sai a ba su mamaki da wannan.
Baba tace "Kash kinga rashin rabo amma kuma fa Habiba ba ku kyauta ba, ai wannan gwajin ba kowa zai cinye ba a wannan zamanin,domin 'ya' ya da iyayen su yanzu sun daura buri akan lefen nan."
Anty ta tabe baki ta ce, nifa dama yarinyar nan bata min ba idanunta sun bude da yawa wayo zata zo ta yi ta wa Halifa to shi bakar zuciya ce da shi, ga kafiya ko me zaki fada masa ba zai yarda ba sai ya gani da idanunsa shine na harba shi a haka bukata ta biya amma ya sake yin wani shashancin.
Baba tace "Su wadannan ai sai dai a kira musu babu, bashakka ba su da shi amma suna da mutunci kuma sunyi murna sosai." Anty ta zuba ido tana kallon Baba kamar wadda ta ji wata sabuwar kalmar da bata taba ji ba. Ta maimaita kalmar Babu!! Wai Baba kina nufin talakawa ne?!! Baba tace 'Yan uwana ne talakawa tilis kuwa amma ai wannan ba zai hana aure ba, domin baya cikin dalilan da suka hana a auri mace saboda shi."
Anty tace Baba muje in raka ki, Baba ku na da ne bazaki gane ina lamarin ya sa gaba ba, yanzu ba duniyar ku bace irin ta da, yanzu sai dan yanzu, wake harka da talauci,ai ko a tafiyar kan hanya bana fatan haduwa da malam talaka bare aure wannan maganar babu ita ko me zai yi, ashe gara ma su Bilki su da dan abin karyar rayuwa ce tai musu yawa, karyar tafi arzikin na su yawa, wannan babu fa ake kira tab.
Baba ta cika da mamaki, tace"Habiba yau she ki ka zama haka? " Anty ta yi yar dariya dama fa Baba baki sanni ba ganina ka wai kike yi. muje a kai ki ki hau adaidaita sahu ki koma gida ko menene kwa ji daga baya.
Hafsi ce ta tafi saka Baba a Napep Anty kuwa kamar ta yi hauka domin ta kira Halifa ta gaji amma bai daga ba. Daidai lokacin yana gaban wanda ya buga musu kati suna magana kan cewa ya sake buga musu wani amma ya canza sunan. Sulaiman ya kira ya mikawa mai buga katin wayar tare da fadin fada masa sunan yarinyar nan. Bayan ya fada masa sai Halifa ya amsa yace yawwa ka sanar da mahaifin yarinyar nan goben zan zo da magabatana a ko wane lokacin daga goman safe zuwa azahar, ita kuma ka fada mata zan zo da dare ya kamata ko sunan ta in rike.
Sulaiman ya sa dariya tare da fadin Halifa sai a barka. Insha Allah zan isar da duk sakunanka.
Kiran Anty ya sake shigowa yana kokari kiran masu Hall da za ayi fati. Ya daga bai bari ta yi magana ba, yace Anty kiyi hakuri gidan fa zan kwana komai dare dole zan dawo bari na gama da kacaniyar waje, bai yarda ta furta komai ba ya katse domin yasan duk damuwarta ya yanke shawara kai tsaye bai tuntube ta ba.
Ya fadawa wa masu Hall an fasa party su ba wani date din ya maida musu kudin su.
Anty ta rasa inda zata sa kanta ta danno number aminiyarta Hajiya Talatu domin neman dauki na shawarar abinyi cikin gaggawa.
Hajiya Talatu ta kalli sunan dake kan screen din wayar Sahiba ta furta tare da kallon yarta Ma u, tace "Ga matsiyaciyar nan tana kirana duk yadda aka yi neman fatawa ta zo, ai Habiba in har ta ci gaba da nuna min cewar bata gane wai ke nake son Halifa ya aura ba sai na koya mata yadda ake duniya."
Ma u ta taɓe baki Mama tace" Bar yar hau sai jininta ya yi sama zan daga in ta kira kamar sau biyar." Ma u ta sheke da dariya, tace Mama da Sahibarta. Hajiya Talatu tace yar Hassada ce tuntuni ta ke aiki akan Halifa wai kar ya yi aure sai wadda ta zaba masa tun ina shuna mata ke cikin Hikima har na furta mata cewa a hadaku kai tsaye ta ce bazakiyi masa ba, abin yamin ciwo amma na danne kuma abinda bata sani ba, wannan auren da Halifan zai yi tuni na saka Malam na shuri ya tarwatsa komai na san ma yanzun kiran nan labarin fasa auren zata bani da neman yaya zata yi. "
Ma u tace Wai shi Halifan ba kaninta bane me ya sa ta ke masa haka?
Hajiya Talatu tace, ' Dalilin da yasa na ke son ya aure ki ya kamata ki tambaya, kuma shine dai dalilin ta na hanashi auren sai ta nemo wadda ta ke so, dafa zai yiwu Hafsi zata bashi, dan dai muharraman juna ne. Ma u tace Wai duk menene dalilin ku?
Hajiya Talatu ta dauki wayar ina zuwa bari in daga yanzu na san tana wuya.
Cike da barkwanci tace Sahibata yi hakuri kin kira ina salla banyi la asar ba ga magariba ta doso kai. Anty ta ja tsaki "Wai yau she zaki tsaida sallah ne Sahiba. Ni ba wannan ba, kinsan auren Halifa ya wargaje?" Hajiya Talatu ta dau salati tare da danna Hansfree domin yarta Ma u taji. Anty ta ci gaba da fadin "Menene a bin yin salati ni ai gaba ta kaini dama ni na saita hakan kuma hakan nake son ya faru. Sai dai wata masifar yanzu haka ya kai kayan gidan su wata wadda ban santa ba, ya kuma ki sauraro bare. ma in fahimci komai dan insan ta ina zan bullo masa in ya shigo gidan."
Hajiya Talatu cikin mamaki tace Wai shi wannan yaron wane irin raini ne a tsakanin ku haka, na rasa sam bai maidake a bakin komai ba wallahi, banda haka ya Isa ya yanke irin wannan hukuncin kuma cikin gaggawa. Wai in tambaye ki Sahiba, kin yi masa aikin gurin Malam na daji kuwa?
Anty ta ja tsaki "Shin wai kin manta Halifan ne gurin Malamai nawa muka kai shi da ke, amma kamar ana shuka dusa. furar da Malam na kauye ya bani in dama masa, da yake gwanin fura ne a gabana ya shanye ta amma dan nan ko gezau."
Hajiya Talatu tace kira Malam na kusfa ya yi miki binciken gaggawa yanzu ki samu bayani, kinsan shi maza maza ne. Nima bari in kira na Shuri yanzu. Anty tace." To kirashi kin dai ki hada ni da shi. " Talatu tace Zan hada ku bari a gama wannan badakalar. Suna kashe waya Anty tace Matsiyaciya muguwa sai na gano shi in ma baki hada mu ba, kuma sai na gano dalilin ki na kin hadani da shi.
Itama Talatu a nata gefen cewa ta yi Bazan hada din ba mai mugun hali cinnaka baka San na gida ba, ni ce maganin ki.
Anty ta danna kiran Malam na kusfa a rude take fada masa cewa ya yi mata istihara yanzu a kan kaninta Halifa ta karanta masa komai yace bani mintuna, ta sake kiran wani malamin ta sanar da shi. Malamai ukun duk sun bukaci sunan yarinyar ko na Mahaifiyarta. rashin sanin sunan ya kawo tsaiko game da binciken dole sai zuwa gobe in Halifa ya shigo ya fada mata sunan domin kowa ya ce mata ya ga auren Halifa Amma baiga matar ba.