← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 62

Sashe 16

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan zaki zama mai shahara a Duniya ta yadda ko ina za a sa ki, gwamnati sai ta so ta yi hulda da ke ko da kuwa ba wani Abu da zaki amfana mata." Anty ta mike cike da jin dadi Malam ka tabbatar hakan da ka fada za su faru? Yace "Kar ki yi wata shakka hakan zai bata mana aiki. Abinda kawai nake son ji zaki kawota?" Anty tace to ina zaka samu sauran Matan? Yace " Duk na samu, domin matar ɗana ta haihu zan yi amfani da ita kuma ina da Uwa ina da kanwar ta samu daya cikin su ba zai min wahala ba, samun sabuwar Amarya ma ba zai min wahala ba mai irin taurarin ta ne wahala dan baifi kamar a watsa biyar a cikin dubu ba, haka ta ke, yanzu dan ba a bude taurarinta ba ne shiyasa bazan gane ba, yana kwanciya da ita kuwa shikenan ya bude mata taurari kuma tauraron sa da nata tamkar bawa ne da ubangidan shi.kuna kallo zaku hakura dashi. Dan haka ni zan bude su taurarin na ta." Anty tace na gane zan San yarda zanyi tun yau ba sai goben ba in kawo ta. Sai dai ina tsoron karta zo ta fada masa. Ya saki dariya mai karfi. Zan mantar da ita komai, banda wannan tauraron nata ai kasheta zan yi kuma ba wanda zai tambayi ina take har abada.

Anty tace to Malam ina godiya in mun samu zuwa yau in kuma sai goben to ba matsala? Yace "Ba damuwa kar a wuce gobe dai.

*Zaɓi ɗaya cikin biyu ne ga duk me son karanta littafin HASASHE,Na farko zaka shiga wannan link ɗin 👉🏼https://www.facebook.com/share/p/1Bevu6CRwK/ zai kai ka/ki facebook zaka yi following channel ɗina na FASIHIYA ka/ki turomin screenshot ta wannan number👉🏼0814 000 4302 ko wannan 09068032427 zan sakaki group ɗin da zaki samu littafin ƙyauta, za'a cire alfarmar following ɗin a 10-june 2025 saboda haka duk wacce takai lokacin batayi following ba sai dai tabi hanya ta biyu,sai hanya ta biyu waɗanda basu buƙatar yin following zaku turo ₦1k ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank*

*✍🏻HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
[6/9, 10:43] Ummi Tandama😇: Anty ta yi sallama a kofar dakin Asiya, Halifa ne ya amsa, gabanta ya dan fadi amma saita dake, yace ki shigo Anty mana. Ta shiga tana waige waige," Ina yarinyar nan ta ke?" Yace tana bandaki bari na kira ta. Tace Dama so nake anjima idan rana ta kara sanyi zan kai ta gidan Baaba harda Baffanku Dan 'yan uwanta ba su kai ta ba, sun bada sallahu cewa a kaita, to bana son abin ya ja lokaci ya zama shiri ririta." Halifa yace Anty ki barshi kawai ni sai muje tare in kaita na hutar da ke. Da sauri tace, " Wa ya fada maka ana haka? Ai wannan al adace mai girman sai a dorawa iyayenta laifi ace sun rai na danginka , kuma bayan sun bar sallahu. Dan haka ni zan kaita. " Halifa yace to ba matsala ni sai in kai ku. Da sauri tace. "Sai kuma ya zama abin magana, ba a zuwa da Ango." Halifa yace a musulinci ne zai zama abin maganar ko a me? Anty wani abin ma ku mata kuke ruruta shi, to yanzu sai a kira Bros ya kai ku ko? Tace Dan Allah ka samin ido kawai bazan jera da shi ba, dan shima ina cike da shi na tura mishi lambar yarinyar da na samo mishi yaki kiranta, sai yana ce min wai wayar bata shiga kuma karya ne. Halifa ya ce Anty Dan Allah ki kyale Bros da batun auren nan, kawai ki bari ya zaba da kansa, ko zamanin ku fa ba ayi muku haka ba.

Karo na farko da Halifa ya kware mata baya akan maganar Bros. Ta dan yi dim Dan tana samun kwarin gwiwa daga gunsa da kuma tirsasa Bros din ta gurin shi. Tace "Bar maganar shi kawai ka fada mata in ta fito sai ta shirya. Yace to ba damuwa.

Asiya tana toilet ta gama ta kasa Floshing tana ta tarar ruwa tana makawa amma yaki wucewa duka, bata san Halifa ya shigo ba. Sai taji maganar shi a dakin yana fadin lafiya kuwa fin minti arba in. Ta leko ta bata rai ni kam in da wani ban daki a tsakar gida can zan na shiga. Ta fada tana tura baki cike da shagwaba. Yace to wannan menene matsalar shi?" Tace ina ta zuba ruwa amma yaki wanke wa. Halifa ya gane fuloshin ne matsalar, yace" Kuma kin danna gurin zubowar ruwa?" Tace ina ne gurin? Ya nufo ban ɗakin ta kulle da sauri tace ka fada min yace to ki danna wani guri a sama tukunyar nan ta makale. Allah ya ba Asiya sa"'a ta danna sai taji ruwa da gudu ya wuce da bayan gidan nata. Ta sauke ajiyan zuciya tare da fadin Allah ya kyauta rashin sani.

Ta fito ban ɗakin domin ta fesa turare duk da ba wari amma sai tana jin kunyar fita. Daga can cikin falo ta jiyo ana magana kamar muryar Maman Annur da sauri ta leko, su ne kuwa da yan layin su wasu yan mata. Murna Asiya kamar ta cinye su. Halifa ya gaisa da su ya koma daki, suka zauna ta bude firji ta dakko musu ruwan roba da lemo, suna ta Kallon ta cike da shi awa. Ta nufi dakin tana ce musu ina zuwa. Yana zaune bakin gado yana danna waya, tana shiga kamar ya dan razana ya aje wayar ta share kamar bata kula ba, tace zan dafa musu abinci. Yace "To ai kinga ban kawo kayan abinci ba, kawai ki kawo masu kayan tea da baredi kajin da baki ci ba suna firji sai ki kunna gas ki sa su a oven su yi zafi." Tace Ban iya. ba fa ko kunna gas ban taba yi ba, kuma bansan ina ne ma oven din ba. Yace muje in nuna miki ya koya mata komai sannan yace yar kauye, cike da tsokana. Tace naji Dan birni na samu karin ilmi yanzu ko ina naje na san oven da yadda zan sarrafa shi, kuma na iya kunna gas. Ya fito yana dariya ya shiga daya ɗakin ya sake daga kiran da Bilkusu take masa ta Vedio call.

Kuka sosai take tana tambayar shi cewa "Dan Allah ya fada mata ya kwanta da Asiya ajiya? Yace Bilkisu ina rokonki ki daina wannan maganar sirrin gida na ne, bana cikin masu irin wannan shirme, ki yi magana akan abinda ya shafe ki ya shafe ni kawai.

Ta sake fashe wa da kuka "Wai tafi ni kyau ne ko ta fini dirin jiki ne har da zaka kwanta da ita bayan ka jima kana fada min cewa tun da kake baka taba sanin wacece mace ba a kaina zaka fara, me yasa ka kasa sadaukar min da kyautar da ka jima da bani. Halifa ya yi shiru ya kasa magana, abinda bata sani ba, zantukan ta suna motsa shi suna tada masa hankali yana jin bukatar sanin macen. Ya jure yace, "Ki yarda da kaddara mana.

Asiya ce ta sake murda kofar ta shigo ya sake kife wayar da sauri yace ya aka yi na barki na gudo nan kin biyo ni?" Tace dama zance maka in kai su su gaida Anty ko? Ya kalli sashen kirjin ta, sai ya ji wani abu tundaga tsakiyar kan sa ya dira babban dan yatsan sa. Da gira ya amsa mata tace Kamar kana jin bacci yace" Sosai ma zan kwanta Dan Allah ki saurari bakin ki ko? Tace to, ta Juya yabi dan kugunta da kallo "Shine halas dinka wata zuciyar ta sake rada masa ya yi mika ya kwanta sannan ya daga wayar shi da ya kifa ta ganin ta kashe, ko data kira ya ki daga wa.

Asiya ta raka su Maman Annur gurin Anty sun gaisa ta yi musu fara a ta sa aka aiko musu da abinci. Suna gidan har bayan magariba haka ya yi wa Anty cikas, dan ta kira Halifa yafi sau shida yana cewa bakin ba su tafi ba, ya kara da cewa Anty a bari sai gobe mana tunda yanzu magariba ta yi ba iya gaisuwa zataje ta musu bane ki daina daga hankalin ki akan karamin abu mana. Tace so nake in wuce gurin kawai in huta ba wai dan wani abu bane.

Yace ki bari sai gobe, tace to Allah ya kaimu, sannan ina sake roka mata alfarma ka barta ta warware kaga yadda take a jeme. " Cike da kosawa yace to Anty ya kashe wayar.
Asiya ta idar da sallar ta dakko maganin da maman Annur ta kawo mata a jarka ta daga tana sha, duk da bata fada mata ko na menene ba ta san dai na mata ne tana karantawa a litattafai. Ya shi go ta yi sauri ta boye dan tace mata karta bari ya gani. Ya tako a hankali zuwa kusa da ita ya kai hannu ya dakko robar, yace menene wannan ki ke sha ki ka boye dan kar ki sammin? Yar rowa ce tsakanin mu.

Ta ji kunya ta turo baki cike da shagwaba tace Haka aka ce kar in Bari ka gani, nima bansan ko na meye ba wai ance maganin sanyi. Ya yi dariya ya dan kurba tare da fadin "Wai nan ke harda maganin mata ki ke sha ko? Ta zaro ido tace me yasa ka sha ance fa banda maza. Ya aje robar" Ta shi muyi sallar jiya da ake ta min korafi. Suna idar wa ya kawo kaza mai dumi daya ciro a oven da madara mai sanyi ya aje gefen Sallaya yace, wannan ake fara ci idan aka idar da sallar. Ranar kam ta ci, suka gama yace sai kuma ibada ta gaba nace miki a hade suke. Tace gashi bani da carbi ko zaka bani naka. Ya yi dariya yace kiyi wanka ki shafa turare ki sa kayan bacci ki same ni a wancan dakin tace to. Duk da gabanta yana faduwa kuma sarai tasan nufin shi, amma ta yi alwashin zata jure komai dan ta same shi.
Chapter 16 · 0% Book details