← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 68

Sashe 9

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****
hafeez bayan yayi sallar laasar yana kokarin canja kaya ya fito jikinsa yayi masa sauki ummah ta shigo ta sameshi fuskarta a daure tace"ina kake shirin futa hafeez?yanzun ma can wajen husnar zaka?matar abokin naka"hafeez yayi murmushi ya dafa kafadarta yace "ummah inaso kibani goyon baya ki kwantar da hankalinki yaseer ya saketa baya sonta saboda yayi aure sana Aljanu ne suka saceta"ummah ta zaro ido hafeez yace "karkiji tsoro ummah Dan Allah kibani goyon baya"ummahnsa taja da baya cike da tsoro tace "ban yarda ba bazan taba Amincewa da kafada halaka ba hafeez kasan me kake fada kuwa to bari kaji bazaka daukomin masifa ina zaune lafiya ba zan fadawa mahaifinka yau zai dawo nasan kibazakaji maganata ba sanan bari kaji yanzun ma bazan barka ka fita ba"wani miyau mai daci hafeez ya hadiye yanawa ummah magiya bata sauraresa ba ta fice tana mita tsaye yayi yana tunanin furucun Abraham dana ummah kwarin gwiwa yasamu daga zuciyarsa dake karfafa masa gwiwa ya leko kanwarsa ce ke kallo a parlor ya waiga yaga ba kowa yayi mata alamu da ina ummah da hannunsa,da hannunta ta nuna masa daki can kasa tace "sallah takeyi kaje zance mata kana daki ka kulle kanka"ya jinjina mata da hannunsa ya fice tayi murmushi tabisa da kallo.....

******
karfe biyar na yamma Abraham ya dira a gate din gidan cikin kamannin yaseer sak har kayan jikinsa yana rike da makullin mota ya nufi shiga gidan su momy ne suka fito tare dasu innah zasu tafi ya tsugunna ya gaishesu innah ta kauda kai Abraham yace "momy husnah ta shirya?naga yamma tayi banaso inyi dare wajen kaita"momy tace "tana ciki a shirye take"tabishi da kallo innah tace "dan kwal uba da iskanci sai wani cin magani yakeyi ba wanda ya isa ya raba auren nan koya saketa saiya maidata"momy cikin takaici take komi ta kasaci sakamakon gabanta dake faduwa tunda aka dauro auren daddy da hajiya rabi.....

Abraham na Shiga tana zaune tayi shiru jiransa takeyi taji takun mutum tana daga ido sukai ido hudu dashi farin ciki ya lullubeta tace "kazo?"ya jinjina mata kai tace "bari in dauko gyale"tayi saurin mikewa ta shige ciki ta bude wardrobe din momy gyalen abaya tayi tozali dashi ta dauka ta fito cike da farin ciki zasu fita da Abraham suka jero suka fito giftawarsu muneeba ta gani ta jinjina kai tayi kwafa tace "kinyi bye bye da gidan nan".....

yaseer tsaki yayi yana daki ya kalli agogo ya kamata ya fita ya dauki yarinyar nan ya fita da ita kafin daddy yayi fushi dashi mikewa yayi ya fada toilet dan yayi wanka.....

******
dukkansu jugum jugim suke a harabarsu sakamakon babu narjisu babu Abraham yaki zuwa inda suke balle ya saki narjisu kamar daga sama sukaga narjisu ta fita hayyacinta tsoro da furgici ya kamasu mahaifiyar Abraham tace "waye ya sakoki narjisu"narjisu ta kalleta fuskarta bakinkirin gashin kanta a hargitse har kasa fatar jikinta dik ta sale tace "nadawo....babu wanda ya sakoni da kaina nayi kokarin kwance kaina maamah"wani miyau mamah ta hadiye mahaifiyar narjisu cike da farin ciki ta rungumeta narjisu tace "ina Abraham "zuhraliyya kallon yadda narjisu idanuwanta ke canjawa tayi hakan ya tabbatar mata ta dawo da mugunta narjisu ta cugaba da magana tace "badai ni Abraham yayiwa haka ba?ya gama soyayya da husnah bazan zuba ido bil'adama tana soyayya da mijina ba"mamah tace narjis....kafin tayi magana narjisu ta bace.....

hafeez giftawar motarsu husnah yagani ta gabansa mamakine ya kashesa ganin yaseer na tukin mota husnah gefensa suna farin ciki da faraa hafeex ya cije lebe yace "wato kishina kakeyi yasa bakaso in rabeta"sai kawai hafeex ya karya mota yabi bayansu husnah.......

*WANAN LITTAFIN NA DUHU NA KUDI NE KI BIYA 300 KI KARANTA IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANRAMUM BAN YAFEBA*

*KI BIYA 300 TA WANAN ACCOUNT DIN KI MALLAKI NAKI*

3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK

SHAIDAR BIYA TA WANAN NUMBER 08036953516 KO KATIN MTN

*IDAN BAKI BIYABA KIKA KARATAMUN ALLAH YA ISA!!!*

*SLIMZY*✍🏻07042277401

15
Daddy bayan fitar Abraham da husnah Wanda ya gansu sun matukar dacewa da juna mikewa yayi ya tashi daga harabar gidan ya nufi sashensa dake ta gefe da wayarsa a hannu yana danno numbobin hajiya rabi,

yaseer rike da wayarsa ya fito ya kalli agogo karfe biyar da minti sha biyar tsaki yayi idan bata fitoba Shi bazai shiga ya kirawota ba dan ko ganinta baya sonyi wanan da rabi mutum ce rabi aljana ya rasa dalilin dayasa tunda tazo gidan nan ko kwanciya yayi ya rufe idanuwansa ita yake gani baccin kirki jiya beyi ba daya rufe idonsa ita yake gani,minti goma sha biyar ya kwashe a tsaye bega husnah ta fito ba ya fito da wayarsa yayi dialing number momy bata shiga ba shikam bayaso ya shiga gidan,juyawa yayi yaja tsaki tunda bata fitoba nasan abinda zanfadawa daddy,ya kamata yaje gidan ummahnsa ya sanar mata halin da yake ciki a wanan gidan,fita yayi motarsa a kofar gida yayi parking ya buga mota yabar kofar gidan yana kokarin kiran muneeba,

muneeba manne da mahaifiyarta a kuryar gado hajiya rabi ta zubo rushin wuta a kasko sun rufe kofa ta zuba turare tana turare jikinta da hayakin da boka ya bata muneeba ta toshe hanci tace "ummah turaren nan fa wari gareshi"hajiya rabi daga cikin zani data lullube tace "kece kikejin warin ni banaji wanan warin a wajen Alhaji kamshi zaiji infada miki yau saidai in bamu hadu ba"murmushi muneeba tayi hangen wayarta tayi tana haske tayi saurin dubawa kiran har ya tsinke tace "yaseer ke kirana nasan sun fita da shida makirar yarinyar nan ta tafi kenan bari in tashi ma inje in duba sashen momy"cikin zumudi take maganat hajiya rabi ta fito ta kakkabe zani ta fito da wani turare tayi inserting ta shafe jikinta dashi jinjina kai muneeba tayi ta fice,

karo sukai da momy a hanya tace "barka da yamma momy "momy ta kalli muneeba yadda take faraa taji bata yarda da itaba tace "idonki kenan sai yanzun nake ganinki?"sosa keya tayi tana leken dakin momy,"lafiya dai muneeba"

"lafiya lau momy nadauka yaseer na nan ne dan nabaroshi gida yace zaizo ya dauki husnah su fita"momy ta kauda kai tana kokarin wucewa tace "tun dazun ya dauki husnah suka fita ai sun dade da fita"farin ciki ya lullube muneeba kamar ta kira yaseer amma ta fasa Dan bataso ya ganota jikinta na rawa ta wuce bata sake magana ba momy ta bita da kallo tana girgiza kai cike da takaici....

******
hannun Abraham cikin na husnah yana tukin mota ta kwantar da kanta jikinsa a kafadarsa tace "kasan me wani nishadi nakeji wallahi kamar kada mu koma gidan nan"Abraham ya shafa gefen fuskarta da hannu daya yace"Ah ah zamu koma mana me zai dameki bayan ina tarw dake husnah"zumbura baki tayi tace "tafiya fa kakeyi saidaib inka dawo ni nan da can banason katafi ka barni"dariya yayi cikin shaukin soyayya yacev"husnah kenan kin manta ni Aljani ne?"ta dago kai gabanta yadan fadi yadda ya kira kalmar aljanin ya girgiza ta dikda har yanzun bata gasgata menene aljaniba menene mutum ba yaga tana kallonsa ya jinjina mata kai yace "Aljani idan yaso zai shiga jikin mutum ya zauna, kasantuwar ni aljanine yasa ko bana tare dake kikejin alamuna a tattare dake koda baki ganina sau da yawa nakan zo baki ganniba musamman idan naga su momy"tayi ajiyar zucuya tace "amma meyasa ni Bana iya shiga jikin mutum"dariya ta bashi ya gimtse dariyarsa bayaso ta fahimci cewar aljani abun tsoro ne yace "saboda keba aljana bace ke mutum ce shine banbancin mutum da aljani"tadan tsorata saidai ta karajin sonsa tinda har yana shiga jikinta?murmushi tayi tace "nakara sonka tunda har jikina kana shiga"ya girgiza kai yayi mata trowing kiss yace cab'e ta sheke da dariya hafeez na biye dasu ya karya kwana ya shiga katuwar wata plaza yayi parking mota hafeez a gefen titi ya parker yadda suka ruke hannu da yaseer yasa shi hadiyar wani mugun miyau take yaji kishi ya baibayesa wato yaseer dama yaidararsa yakeyi?dama yanason husnah? dariya husnah keyi hannunta cikin na Abraham wadda kamanninsa a idon mutane yake sak yaseer a idon husnah kuwa mijinta take gani gwanin shaawa suke jerawa sai kallonsu akeyi faraa husnah keyi fararen hakoranta da suka jeru suka bayyana gumi ne ya gama karyowa hafeez ya koma mota,ta jikin glass din shiga plaza husnah taga wani mutum gefenta mai mummunar kama fuskarsa bakinkirin hakoransa na tsakiya kanana na gefe da gefe masu tsawo ta saki razananniyar kara ta runtse ido Abraham ya kalli kansa a madubi yasan shi ta gani ta madubi sakamakon aljanu basa rikida a madubi ta jikin madubin ya hangi hafeez a cikin mota wato yana biye dasu yayi saurin tallabota idanuwanta a rufe mutanen dake cikin wajen sukai cirko cirko tana nuna madubin idonta rufe tace "dodo ...... Abraham dodo nagani a kusa dani bakai nagani ba"hankalin Abraham ya tashi ya tallabota yana kallom fuskarta yadda ta runtse ido cike da tsoro yace "ba dodo bane ki bude idanuwanki bude kigani bawani dodo kinji matata karki sake kallon madubin tunda dodo kike gani"ta bude ido a hankaki tana kallonsa ya zura mata ido da weni irin kallo mai narkar da zuciya tace "kaima ka gani ko?"yace "nagani tashi ammmm mike to"ya tallabota da kyau ta mike ya gyara mata takalmin idanuwanta ta runtse bata kalli glass dinba suka shige ciki bin wajen da kallo tayi yace "to ki zabi kayan dik da kikeso zan siya miki kinji?"tsalle tayi ya ruko hannunta yace "kiyi murna ina tare dake a koda yaushe ki zaba zan fita zan amsa wayar maamah"ta jinjina masa kai ta shiga bin ko ina da kallo ya fice tsaye yayi a kofar plazar yadda wajen ke kokarin yin DUHU a idanuwansa ya tabbatar da narjisu tana wajen yanaji a jikinsa bin ko ina da kallo yakeyi be gantaba amma he can feel her presence a wajen jikinsa ya kama rawa yace "wato sun kwanceta Kenan"yayi kwafa ya koma ciki hafeez kuwa kallon yaseer yakeyi cikin mamaki,

kwando take turawa taji an rike kwankwasonta kamshin turarensa ya bugi hancinta ta kallesa da wani irin kallo da saida yaji yarrrr tayi masa kyau sosai yacev"munzagaya in tayaki"ta jinjina masa kaim....
Chapter 9 · 0% Book details