Sashe 30
Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
muneeba zubewa tayi a parlorn daddy yana tsaye da farar rigar jallabiya ta bacci ya harde hannuwansa yana kallon kasa muneeba cikin kuka tace"daddy indai yaseer bazaa rabashi da husnah ba to tabbas aljanunnta zasu dawo wajenmu yanzun gashi aljanin yazo yana furgitamu"cikin kuka take magana da tsoro sai gumi takeyi hajiya rabi kuka ta fashe dashi tace"kaga abinda nake fada maka ko? kaima ka kasa bacci sakamakon yadda ya shafi jikinka ka tozarta manyan mutane abun ya dameka sanan gashi yanzun yaje Yana razana muneeba gata da yaron ciki wayasani ko yajene ya rabata da cikin dake jikinta"muneeba cikin kuka tace"kuma daddy yaseer yana tare da husnah sai karfe sha biyun dare sanan ya sameni a sashena bansan meyakeyi ba har yana ikirarin Bazan shiga tsakaninsa da itaba nidai daddy a raba mana auren nan bazan iya rayuwa da mutum da aljani ba"ran daddy yayi mugun baci bugun kofar yaseer sumaji a gaggauce suka waiga duka cikin tsoro suke,.... momy dake kwance kan dadduma inda bacci ya dauketa ta zabura ta mike tana waige waige ta murtsuke idanuwanta to waye cikin daren nan?take tambayar kanta cikin sauri ta mike ta leka dakin husnah ta bude kofa a hankali tasa hannu ta kunna wutar dakin tana kunnawa husnah ta mike ta zauna dama ba bacci takeyi ba momy tace"ke kuma fa?meya hanaki bacci?"muryar yaseer sukaji sama sama Yana magana "a bude nine "momy ta juya da sauri husnah ta zuro kafa tana waige waige bata gansa ba babushi a kusa da ita ta taka a hankali ta fita tabi bayan momy tanayi tana waigen ko zata gansa a parlorn daddy taga daddy tsaye muneeba durkushe tana kuka wani kallo hajiya rabi tayi wa husnah tace "meya fito dake?ko kin taho da aljanin ne nan?"muneeba na jin haka ta mike cikin tsoro da kissa ta makalkale yaseer daya shigo tana kuka daddy ya dakawa husnah tsawa"ke kuma mai kikazoyi nan?kinzo ne da aljanin dodo?"husnah ta kalli momy take idanuwanta suka cicciko da hawaye ta kalli momy suka hada ido da yaseer yace"Daddy babu laifinta a ciki shine yake bibiyarta yake kaunarta amma ba laifinta hasalima husnah batasan menene aljani ba menene mutum ba"daddy ya dakatar da yaseer"ka dakatamun dik abinda kukeyi kaida zainab da husnah naji na kuma sani yanzun wanan yarinyar daka yasar da Ita sai tsakiyar dare ka koma fa?"yana kokarin ture muneeba yayi mata wani kallo daddy yace"tou bari kaji akan wanan lamarin kaga dai husnah yata ce ko to bazan bari ka wulakanta muneeba akanta ba nafada maka kuma dik kunbiya kunbiyar da kukeyi akan maida auren saina gadama tunda nine uban husnah "yaseer ransa ya baci husnah hawaye ke zubo mata kenan Abraham abin kyama ne abun gudu ne? kenan dodannin dik datake gani sune shine Abraham yake komawa mutun?ta fashe da kuka ra ruga da gudu ta wuce yaseer zaibi bayanta daddy ya dakatar dashi"kadawo nan kafin in sassaba maka shashasha dau matarka kutafi"yaseer huci kawai yakeyi muneeba ta shagwabe fuska"tsoro nakeji akwai aljani a cikin dakin daddy ni bazan iya komawa ba"daddy ya dafe kai kawai yasa kai ya barsu a wajen hajiya rabi ta rufa masa baya suka nufi daki yaseer yayi mata wani kallo dayasa ta natsu yana nunata da yatsa yace"ke idan kikace abinda zakiyi kenan bazaki tabajin dadin zama dani ba anfada miki ina sonki kamar yadda nakeson husnah ne?a rashin husnah nasameki har kikaga na saki jiki dake banmasan yadda akayi nafara sonki ba wallahi"yayi kwafa ya fice ya nufi sashin momy g dare shasshekar kukanta yajeji ji yayi kamar ana watsa masa wuta a jikinsa tsayawa yayi jikin madubi Abraham na gefensa Yana kallon madubin ya furgita fuskar Abraham ya gani cikin mummunan kama idanuwansa kyar akansa jajir fuskarsa baka kirin ga wasu kunnuwa Masu ban tsoro kayan saki ne jikinsa ya zabura yayi baya yace "A'uzubillahi"momy tace "lafiya?"ya girgiza kai ya gyara tsayuwa gefe yana waige waige bai gansa ba daya kalli madubi sai yaga wanan mummunar kamar husnah na kuka ta taso ta tsaya gefensa kamar ance ta waiga sukai ido hudu da Abraham ta kwalla kara zata zube yaseer ya rungomta jikinsa tsamm ya riketa ta runtse idanuwanta jikinta sai rawa yakeyi yace "husnah kinga abinda nagani"bakinta na karkarwa tace"nagani dama wanan dodon kagani"yaseer yayi murmushi yayi hamdala yace"tou shine kike ikirarin shine mijinki"Da sauri ta bude idonta ya jinjina mata kai yace "aljani baya rikida a jikin madubi shiyasa kikaga kamanninsa haka yana zuwa miki kyakkyawa kamar balarabe ko?tou babu mummunar halitta kamar aljani kinga yanzun sanadinsa gashinan ana kyamarki mahaifinki ya shafa sanadin haka yasa mutuncin daddy ya zube dikda dai ni ya taimaka hk kikeso kiyi rayuwa dashi ana kyamarki dagake saishi dik rungumekin dayakeyi bakisan dodo ke rungumeki ba?"zabura tayi ta zauna tace"dama dodo ne ke rungumenu?"tashin hankali yaseer ya hango karara a idon husnah ya kalli momy tayi murmushi alamu sunyi nasara akan husnah girgiza kai ta shigayi "shikenan ya cutar dani amma ya cuceni asheshi dodo ne mai mugun kama yake canjawa yana zuwa mun ya yaseer yanzun ya zanyi?"ajiyar zuciya yaseer ya sauke yace"karki sake barinsa ya rabi jikinki kinji?"ta jinjina masa kai ta turo baki tace"momy kawai ya sakeni kinga yanzun daddy ma guduna yakeyi"tausayinta ya kamasu momy ta share hawayenta tace"da izinin Allah "ta rungume husnah itama ra rungumeta yaseer ya mike tsaye yace"momy kiyi mata addua bari inje ta kwanta zuwa safiya zan fita zani gidan innah akan maganar momyna datace dole saita koma gidanta"murnushi momy tayi ta jinjina masa kai yasa kai ya fice parlor ya tarar da husnah inda ya barota ta rafka tagumi cikin damuwa da tashin hankali take tana ganinsa ta mike zatayi magana ya rigata"ni zan tafi ki zauna a nan tunda tsoron kikeji"yasa kai zai fita da sauri tabi bayansa tana waige waige ta ruko hannunsa ya kwace hannunsa yayi gaba tana biye dashi,
husnah kwanciya tayi tai lamo idanuwanta basu daina fidda hawayeba kamannin Abraham data gani ya girgizata kodai bashi bane?kai shine tasani yaya yaseer bazai mata karya ba to idan ma bashi bane meyasa ake gudunta sabodashi?ta tabbatar yau Abraham abun tsoro ne tunda mahaifinta ke korarta saboda aljanu momy tace "yadai husnah"cikin tausayawa husnah tayi maganar ta girgiza kai tace "kidaina kuka kinji?"momy ta mike ta fice batare da tayiwa husnah addua ba tana fita Abraham ya fito ta jikin bango ya harde hannuwansa a kirjinsa ta juya baya tana kallon gefe daya tana juyowa suka hada Ido ta zabura ta koma ta zauna tana waige waige cikin tsoro da furgici tace"mai kazoyi?bayan kai dodo ne bansaniba sai yau kake rayuwa dani?ashe ku aljanu abun tsoro ne?dik na dauka kemanninka haka suke tabbas na gasgata hakan tunda narjisu na zuwa mun cikin kamanninku"cikin tsiwa takeyi masa magana ta Kura masa ido cikin ido tana kallonsa"meyasa ka saceni ka kaini cikin danginku dodanni?"furucin husnah ya bugi zucuyarsa yana mata wani kallo itama shi takeyi dikda zuciyarta cike da tsoro take tana kallonsa,"ni ba dodo bace bana komawa dodo bana canja kamanni in koma wani abu daban amma kai kanayi dik mai yasa?"ya tsayar mata yace"dakata husnah butulci zakiyimun?"idanuwanta suna fidda hawaye tace"ba butulci zanyi maka ba nasan gaskiyar lamari yau dikda baa gama fayyacemum komi ba gashi nasan komi ashe dik tsoratanin da akeyi a danginku ina gidanka lokacin ashe aljanu ne mutanenku?baka taba fadamun ba?kadaukeni kaje kana rayuwa dani?bayan nida kai ba halittarmu daya ba?ka cuceni tunda kasa nakamu da sonka alhalin kai ba mutum bane kamata ba halittarmu daya ba"ta fashe da kuka zucuyarta nayi mata kuna Abraham matsowa yakeyi fuskarsa na canjawa tana rikida tana komawa abun tsoro fuskarsa ta koma kamar bayan kada jajir wasu kulali abubuwa ke fitowa daga fuskarsa ya daga hannuwansa take ya soma rikida jijiyoyi na bullowa da wasu kumbuna yana takowa "baki isa kiyimun butulci ba karya kikeyi kina nufin zaki rabu dani ne bayan nima ina sonki?"tsorata tayi ta manna jikinta da jikin bango jikinta sai rawa yakeyi kamar mazari ta shiga girgiza kai tana runtse ido yazo zai kawo mata cafka ta diro daga gado zata fice ta ganshi a gabanta "nima zaka kasheni ne?toka kasheni ka huta ka kasheni"take cewa cikin daga murya momy ta jiyota ta zaburo ta bude kofar tayi tozali da husnah kamar mahaukaciya "momy gashi nan yazo gashinan yazo na tabbatar da shi dodo ne gashinan yana canja kamanni"ya bude bakinsa hakoransa kamar na damusa tagani ta kwalla kara momy ta furgita ainun ta rungume husnah ta rufe kofa husnah na bude ido ta ganshi ya fito ta jikin kofa ta zabura ta dauki abu zata bugawa Abraham taga ya kalli abun ya dawo mata momy ta dojw cikin tashin hankali momy ke addua a bakinta tana tofawa husnah a jikinta ta rufe ido sai gunji takeyi tana gurnani bata iya magana can taga husnah ta lumshe ido bacci ya dauketa yana tsaye jikin bango yana hawaye husnah tasan wayeshi yau sai ya kashe yaseer sai ya illata masa rayuwa tunda ya shiga gonarsa yana tsananin son husnah kuka yakeyi cikin wani irin yanayi ya bace.......
*Y'AN BATI INA SANE DAKU INADA LABARINKU DIK WANDA YA KARANTAMUN LITTAFI ALLAH YA ISA BAN YAFE MAI BA*
*LITTAFIN DUHU 300 KACAL KI BIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA GA MAI BUKATAR SIYA KO BIYA YA TUNTUBI WANAN NUMBER*
08036953516
07042277401
*SLIMZY*