← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 68

Sashe 66

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kamshin turaren yaseer yasa muneeba saurin dagowa daga zurfin tunanin da ta shiga ta gansa tsaye rike da hannun husnah hannunta cikin nasa Yana murzawa kafeta da ido yayi wani kallo yakeyi mata mai cike da tsana da takaici idonta ya cicciko da kwalla ya kauda kansa yana kokarin fita hafeez ya ruko dayan hannunsa "ina zakaje kuma?ai babu inda zaka inma zaka fita kabari a baka damar haka"ya dawo ya tsaya yanajin husnah tayi wata ajiyar zucuya ta kallesa ta kashe masa ido yayi murmushin gefen fuska,

malam yayi adduoi sosai sanan yasa leda a hannunsa batare daya budeba ya nade abunda muneeba ta haifa sanan ya kawo wani magani yaba hajiya saude "wanan wanka da sha da tsarki zatayi saboda yadda zataji canji a jikinta inshaaa Allah babu komi ma"hajiya saude ta karba tayiwa malam godiya yasa hannu da bismillah ya dauka ya kalli yaseer yace "muje a birne ko?"yaseer ya cije bakinsa ya sake kallon muneeba idanuwanta na kansa ko kiftawa batayi ji takeyi kamar ta hadiyesa ya zama nata suka fice tare da malam husnah ta zauna gefen gado cike da tausayin muneeba take ta yaya muneeba zataji abinda yasamu mahaifiyarta da kanwarta?kwalla ta cicciko a idonta muneeba tace "yadai husnah nasan kina kuka ne saboda abinda ya sameni ko?"husnah ta jinjina kai ta kasa amsawa muneeba tayi ajiyar zuciya hade da murmushi mai ciwo sai hawaye tace "na tuna lokacin da nake fatan aljanu su cigaba da rayuwa dake,na tuna lokacin da nake miki fatan ciwo gashi ke yanzun fatan samun sauki kikeyi mun husnah rayuwa kenan idona ya rufe ban taba tunanin Allah zai juyamun da rayuwa haka ba yau ina mahaifiyata?ta tafi bansan inda take ba itadin da take bani gudun mawa wajen aikata mummunan aiki gashi yau wa gari ya waya"toshe mata baki husnah tayi ta share hawayenta"ki daina fadin wanan abun kinji jarabawa ce da kaddara kinji kidaina kuma yaya yaseer be tsanekiba"daga bakin kofa taji ance "waye yace miki ban tsaneta ba?nina fada miki haka?to na tsaneta tsana ta harabada banason ganinta a rayuwata ko kadan banida bukatar cigaba da rayuwa da ita husnah saboda haka karki yaudareta tasa ran ni zan cigaba da zama da ita a matsayin mata da miji dan haka kizo murafi zo muje banason shakuwarki da ita dan ke baiwar Allah ce bakisan komiba banaso ta koya miki munanan halayenta kazamai"cikin fushi yake maganar ganin yadda ya canja fuska ya tsorata husnah ta mike jiki babu kwari sumi sumi tabi bayansa tana waigen muneeba cike da tausayawa nan muneeba ta zauna kamar an dasata hawaye wani nabin wani.....

Akwai documents na books dina guda hudu mai bukatar duka 1k pc me

zainul abideen
izza ta
kukan zuci
ramin mugunta...

*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BANYAFEBA*

08036953516
07042277401

*SLIMZY*✍🏻

52
ummah hadiza ta shigo dakin dauke da plate din lafiyayyar jealouf din shinkafa sai kamshi take hannunta dauke da kunun gyada a kofi mai dan girma tayi sallama shiru muneeba bata amsa ba ta karayi kallonta tayi yadda hawaye ge gudu a fuskarta harta zauna batasan ta iso ba ta dafa kafadarta tayi saurin share hawayenta "umm ummah hadiza"tana kallonta da jajayen idonta ummah hadiza ta girgiza kai "muneeba meyasa kikeson saka kanki a damuwa ne?tunanin me kikeyi kankanuwarki dake har na iso bakisan nazo ba umm?wanan abun daya sameki rubutaccen alamari ne baki isa ki canja shiba don me zakisa damuwa"ta girgiza kai ta karbi kofin kunun gyadar kamar bazatayi magana ba bakinta nayi mata d'aci tace "ummah hadiza yaya yaseer ya tsaneni na tabbatar ganina bayason yi rabuwa dani zaiyi"ta karashe maganar da rushewa da kuka hajiya saude ta shigo tare da yusrah sunyi shirin tafiya gida tace "ah ah lafiya naganku jigum jigum zaune muneeba na kuka? kukan meye kuma kikeyi hakan?"ta girgiza kai hajiya saude ta hada rai tayi kicin kicin ta soma sababi tana fadan muneeba na cuccusa abinci tace"ni tafiya zanyi sai kuma an kwana biyu tunda zainab tace babu suna batason tara mutane gara in husnah ta haihu ayi ai ta hutar damu sai an kwana biyu zan leko ku"ummah hadiza ta mike "muje in taka muku Allah ya huta gajiya yabar zumunci"

"Ameen"ta amsa harta kai kofa ta juyo "to muneeba Allah ya kara lafiya"ta jinjina kai ta amsa mata muryarta na rawa suna fita ta kifa kai a pillow ta soma rera wani sabon kukan....

*****
yaseer na kwance yana rungume da husnah fuskarsa daidai gefen fuskarta yana shafa cikinta yace"ke yanzun fa baki sona yasa ko kishina bakiyi ko?"ta dan kallesa ta hararesa "injiwa waye yace maka bana kishinka ina sonka ina tsananin kishinka"tadan tura baki,..
"gashi kuwa kinason zama da kishiya inbake ba husnah waye keson zama da kishiya waye ke gayyato kishiya?kishiyarma irin muneeba wadda na tabbata tasamu dama akanki hawa kanki zatayi don ta fiki wayau mugun takaici kike bani bansan wace irin wawta ke damunki ba"shiru husnah tayi tana nazarin maganar yaseer tadan jiyo da kanta ta kara shigewa jikinsa yayi mata rumfa da hannuwansa gashinta ya bazu a kafadarsa tace "tsananin tausayinta nakeji yasa kaga ina rokar mata gafara wajenka amma ban kawo tunanin cewar zata iya samun dama akaina ba dikda nasan cewar mace babu abinda bazata iyaba yaya yaseer muneeba tana sonka dik abin nan da nakeyi dannewa nakeyi kawai duba da halin data tsinci kanta ciki"ya shafa gefen fuskarta yace "Tou bari kiji bazan taba zama da mazinaciyq ba akan hakan zan iya rabuwa da kowa in akace saina zauna da muneeba"tayi saurin kallonsa tana nuna kirjinta "har ni?"ya kashe mata ido "Banda ke dan nasan kina sona bazaki taba takuramun akanta ba bakyason fushina"ta shige jikinsa "waye zaiso fushin mijinsa"yayi yar dariya ya cire rigar jikinsa ya dago kanta ya nuna mata nipple dinsa ta hararesa "me kuma zanyi?da wanan kananun nipple's din"dariya yayi ya ware idanuwansa yace "au nidin to sucking zakiyimun inaso indan karawa yarona karfi ne"ya janyota yana kokatin cire mata riga cikin sigar shagwaba take tutturesa tana dariya haka yayi nasarar zare Matq rigarta yq zurawa boobs dinta ido yace "wad'anan suna kasheni suna tafiya dani suna matukar daukar mun hankali"cikin shauki ta girgizasu yayi wata yar kara ta sheke da dariya ta rukosa tace "kai ummah hadiza fa"ya kada kai "batanan tana sashensu momy wajen mai jegon Dodo"hararsa husnah tayi ya faki idonta ya cafki breast dinta ya lumasu cikin bakinsa tadan gabtsare tana shafa nasa kai tana lumshe ido dadi na ratsata wasu wasanni yaseer keyiwa husnah masu ratsa sassan jiki da dik wata jijiya dake kai sakwanni kwakwalwa da zucuya idanuwanta a rufe yake ya haye kanta cikin nishadi sun kwashi minti arbain a haka dakyar yaseer ya d'aga husnah ya rungumota jikinsa tana sauke numfashi yace "Allah yayi miki albarka hussy"yasa hannu ya janye gashinta daya rufo gefen fuskarta tayi murmushi ta motsa pink lips dinta tace "Allah ya saka maka da Alheri mijina ina tsananin kaunarka"ya lakuce mata hanci yace "muje muyi wanka"ta make kafada ya gane mai takeso ya dauketa yasata a kafadarsa suka shiga sun dauki lokaci suna wasanni sanan suka fito tare ya shirya tsaf ana kiraye kirayen sallahr magriba yasa jallabiya ya fice itama ta tada sallahr ta a gida tana fitowa nusrah na zaune a parlor tana daddana waya tace "yauwa Anty husnah zo in koya Miki wayar nam da yaya yaseer ya siyo miki"cikin mamaki husnah ta ware ido "waya kuma"

"au be fada miki bane"murmushi tayi take taji ta kara son mijinta a zucuyarta ta zauna nan nusrah ta shiga koya mata wayar iphone 13 ce sabuwa gal a kwali husnah murna kawai takeyi bakinta yaki rufuwa wajen minti talatin yaserr be shigoba ta kalli agogo tadan damu gashi gari ya soma duhu tace "nussy muje sashensu momy"nusrah kamar jira take ta mike "muje inyi wasa da shuraim da sudais din momy"

husnah ta ware ido "au har ansa musu suna ne?"nusrah ta jinjina kai ehh "daddu yace daya sunansa muhammad badamasi daya sunan daddynmu wato Ahmad shida Amininsa yasa"husnah dadi ya lullubeta suka fito a tare,

muneeba na zaune a sashenta ta mike kafafuwanta da safa a kafar tana kallom tv amma sam hankalinta baya kan tv kamar daga sama taga yaseer a gabanta ta zabura tana kallonsa bakinta ba rawa tace "ya yaya yaseer ka shigo mana"wani kallo ya jefeta dashi ya kauda kansa gefe "Allah ya tsareni in zauna kusa da mazinaciya mai shirkarka wadda ke had'a Allah da wani ke dan bakida kunya sai kice inzo in zauna inyi miki me?"ta sunkuyar da kanta gabanta ya tsananta faduwa tozali da tayi da farar takardar dake hannunsa jikinta ya soma karkarwa kamar ana watsa mata ruwan sanyi tace "ka kayi hakuri "dakatar da ita yayi ya tako cikin dakin yana taku cikin kasaita ya kara kyau sajensa sunyi bakin kirin fuskarsa sai sheki takeyi ta zuba masa Ido hade da shagala da kallonsa wani tsawa yayi mata "meye kike kallona kqmar wata mayya?karki sake kallona ke idan kika kara kallona Allah ya isa kuma saina Miki mugun duka"tayi saurin kauda kai jikinta sai rawa yakeyi yadda ya fusata ya hada rai yana karto mata rashin mutunci yace "karbi"tayi saurin kallon hannunsa ta kasa mika masa hannu yace "zaki karba ko saina mammareki?"da sauri tasa hannu ta karba kwalla ta cicciko a idonta yace "sakamakonki ne nasakeki saki uku kije ki samu kanin boka ki aura dan na tabbatar idan saki daya nayi miki to nasan kila tausayinki zai tankwara zucuyar wani cikin iyayena in maidake to babu aure a tsakanina dake dan nidin ba mazinaci bane irinki mazinaciya"muryarsa kamar zata fasa dodon kunnen muneena musamman yadda ya kaurara maganarsa ta kiranta mazzinaciya ji tayi tamkar mafarki takeyi rufe idonta tayi tana rokon Allah kada ya farkar da ita daga wanan mummunan mafarkin da takeyi ya tsirtar da miyau a tsakar dakin ya finciki kofar ya fice ya buga karar buga kofarsa yasa tayi furgigit ta kalli takardar dake hannunta cikin jikinta takejin wani zugi zafi radadi na ziyartarta hade da wani gumi da yake karyowa a dik wata kafa ta jikinta,
Chapter 66 · 0% Book details