Sashe 46
Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"nace tabar gidan tace bazata bariba saida shaida zataga yadda zanyi da ita kuwa saita gwammace zaman makabarta da zaman gidan nan"yasa kai ya wuce murmushin mugunta hajiya rabi tayi ta sauke ajiyar zuciya cike da nishadi tabi bayansa zuwa sashensa tana lallaminsa da makirci da kissa.....
*****
husnah suna zaune a parlor da yusrah sun saka sunna tv suna kallo momy da nusrah suka shigo a tare nusrah ta zubo musu abinci a tray ta ajiye momy tace "a canja Tasha akai ta karatun alkurani mana"
"momy nan ma ai waaazi akeyi shiyasa muka kai"momy ta zauna tadan kalli husnah tace "yadai husnah ya kikejin jikin naki?"murmushin karfin hali husnah tayi hankalinta baya jikinta gangar jikinta ce a wajen hankalinta na wajen yaseeer,ta cije tacev"da sauki momy jikina kamar ba nawa ba banajin komi"
"da kyau husnah ki dage kinji karji kuskura ki rinka zama ke kadai kinji?sanan ki rinka zama nan munasa karatun alkurani munayin hira tare dikda zaman naki yau ne zuwa gobe jibi zaki koma gidanki gobe zaayi komi a gyara tunda babanki ya sai miki kaya dazun yake fadamun da mukai waya"husnah ta sunkuyar dakai idanuwanta suka kawo ruwa yanzun da Abraham zata tare?aljani?ta cije lebenta tabbas sai tasan yadda tayi momy ta gamsu da cewar yaseer din da yake zuwa ba yaseer bane Abraham ne kuma aljani ne amma kuma bataso hankalin momy ya tashi d'anta kwaya d'aya tilo,"ya kikai shiru husnah?"girgixa kai husnah tayi cike da kunya ta sunkuyar da kanta kasa tace "bakomi momy"
"gobe ki shirya da wuri idan yaseer yazo sai kuje dasu nusrah a siyo kayan sawa ko?"husnah wasu hawaye ne suka cicciko idanuwanta ta tabbatar da momy na tsananin kaunarta dikda kasancewar tana tare da aljani bai hanata sonta ba besa ta kyamaceta ba nusrah ta ajiye ruwa tacev"bismillah kumuci abincin"
"yan ubanci zakuyimun ko kun kama yar uwarku zakuci ni baku samin nawa ba"sukai dariya a tare yusrah tadan kalli momy cikin sigar wasa tacev"kishi kikeyi?"momy tayi dariya ja'ira kawai"jujjuya cokali kaeai husnah keyi ta kasa cin abincin momy na lura da ita sosai "husnah meyasa kika kasa cin abincun?"kuka husnah ta fashe dashi kamar tana jira momy ta zamo daga kujera ta karaso ta rungumota jikinta tana fad'in "lafiya meyafaru husnah kodai bake bace fadamun"
"momy ki yarda dani yaya yaseer dake zuwa gidan nan bashi bane Abraham ne, Abraham ne ya sauya kamanninsa zuwa yaseer shine yakeso ya tare dani ya batar da yaya yaseer "momy ji tayi kamar husnah ta buga mata guduma gabanta ya yanke ya Fadi tayi shiru tana nazari cike da rudu take girgiza kai "yanaso ya haukataki ne kawai husnah amma yaseeer ne kila yana sauya miki fuskar yaseer din ne kawai babu siddabarun da aljanu basu iyaba kinji kiyi hakuri kidaina kuka yaseer ne yana nan babu inda yaje"husnah kasa magana tayi cike da tausayi take kallon momy share mata hawaye momy tayi "maza ci abincunki kinji ki koshi sanan kije ki kwanta kin shiga ruwan zafin danace ki gasa kanki?"ta jinjinawa momy kai ta dibo abincun ta kai bakinta tamkar tana cin mad'aci haka takecin abincin....
*******
turare mai kamshin gaske muneeba ta shasshafa a jikinta lungu da sak'o cikin tsananin farin ciki take yau kalaman da yaseer ya fad'a mata ke yawo a kanta tana daure da towel taji motsin mutum da sauri ta waiga Abraham ne tsaye ya jingina da jikin kofa bashida karfi ko kadan a tare dashi sakamakon abinda ya shaka kamar zai mutu yakejin jikinsa kamar ana tsira masa allura,shiru muneeba tayi tana kallonsa "lafiya yaya yaseer naganka cikin wanan yanayin kamar kana cikin damuwa"idanuwa jajir Abraham ke kallonta yadda idanuwansa suka rine saida tad'an tsorata ta hadiyi miyau ta mike tana kusantosa ya d'aga mata hannu da sauri ta dakata kallon tsana yakeyi mata ji yakeyi tamkar ya shaketa ya mutu dan tsananin haushin da yakeji yaso ya rabu husnah yau burinsa bai wuce ya kusancetaba ya rabata da yaseer amma hakan ya faskara bazai taba iya zaman gidan ba zai iya hallaka,"karki matso kusa dani jikina bashida kyau mtswww naje gidan momy ne wanan sarkin aljanun husnah itace suka motsa shine na tabata jikina warin maganinsu yakeyi"ajiyar zuciya muneeba tayi dan cikinta gaba daya ya d'uri ruwa ganinsa cikin wanan yanayin ta dauka ya dawo hayyacinsa ne tayi murmushi "shine kake fushi?to kayi hakuri bari na taimaka maka kayi wanka ko?"cije lebe Abraham yayi sam bayaso ta gano shidun ba mijinta bane gashi kokarin shiga gonarsa takeyi idan ta kuresa tsaf zai bayyana mata koshi waye dan ya huce takaicin abinda hajiya saude tayi masa tabbas wanan matar sai ya dau mataki akanta,gyara tsayuwa yayi kafin yace wani abu ta ruko hannunsa tana kokarin cire masa riga badan yaso ba haka ya cire gabaki daya bayason motsi kuna ce a jikinsa ta maganinda karatun alk'urani....narjisu ce ta shigo dakin ta jikin bango wani kallo yayiwa bangon ya juya ya kalli muneeba yaga ta tsaresa da ido mamakin yaseer takeyi kardai shima aljanun sun shafesa,
"Abraham meyasa ka zabi rayuwa da bil'adama a duniyarsu kabaro duniyarmu kazo nan dan cikar burinka?"tambayar da narjisu tayi masa kenan yasa kai ya jufi toilet Tasha gabansa,"Baka amsamun tambayata ba,idan har kai ba mugu bane to me kakeyi a nan?dubi yadda jikinka dik yayi kuna kuna dik sakamakon husnah ne shin wanan husnah bazaka iya rayuwa ba saida ita?tace masa cike da tsiwa da takaici kallonta yakeyi tsaye a gabansa ya kalli yadda gashin kanta ya tsaitsaya takaici biyu ya hadun masa cikin fushi yace batare da bakinsa na motsi ba "ki kaucemun kafin na illataki na halakaki nafada miki kibar shiga gonata da rayuwata ninaga inaso zan iya ko dolene?so kikeyi wanan dake tsaye ta gane ni waye?"ya kalli muneeba da tsoro ya gama cikata kardai yaseer aljanu sun shigesa yadda taga yana kallon gefe daya bakinsa na motsi batasan me yake fada ba,ganin kallon da takeyi masa yasa ya wayance ya janyota ya rungumeta take ta fama masa kunar dake kirjinsa a manne yacev"ashhhg
"yadai menene yaya yaseer?"ya girgiza mata kai "gajiya ce ga tunani dayake cunkushe a zucuyata muneeba"ya shafa kanta "bari nayi wanka na fito ko?"ta gyada masa kai tayi farrr da ido "nayi missing din gwarzon mijina yau ina bukatarka inaso ayimun wanan sucking din"ta kashe masa ido ya girgiza kai ya shige toilet yana shiga ya rikida ya koma kamanninsa mai tsananin girma da ban tsoro juyi yayi yana kallon yadda fatar jikinsa tayi yayi wani huci ya kalli kofar bayin haushin wanan matar yaseer din yakeyi gashi narjisu ta bace yabarta tsaye yasan zataje neman Yaseer ne ya kumasan bazata taba ganinsa ba tunda yana tare da zuhraliyya.....
******
bakin kirin sararin samaniya tayi sakamakon dare da ya farayi kukan tsuntsaye yaseer yakeji ga tsananin kishin ruwa da yakeji dikda wacen aljanar ta kawo masa amma bazai taba iya shan ruwan aljanu ba,
kallom kasan bishiya yayi zuhraliyya ce da kayan saki a jikinta blue black ta kama gashinta gefe da gefe fuskarta fari tasss wasu ne sukazo wajen yana kallon yadda ta mike tana zagaye can kafin ya runtse ido ya bude wajen ya cika da aljanu yan mata da samari yaseer na kallonsu yanaji wani aljani yace "zuhraliyya inaji kamar akwai mutum a wajen nan bil'adama ko?"ta jinjina masa kai ta daga manyan idanuwanta sama ya kalla idanuwansa ya hasko masa yaseer ta tabe baki "yaya Abraham ya Bani ajiyarsa a nan yasa kukaji nace muzo muyi gad'ar a nan banaso nabar wajen"ya jinjina mata kai tayi wani tsalle ta soma rawa tana bada waka nan da nan suka soma yaseer dik abinda sukeyi a idanuwansa sukeyi yana kallom wasu kanana sunatayo itace suna kaiwa manyansu dake bayan bishiyar sunata girke girken abinci hakan ya tabbatar masa da yanzun dare ne dan idan da rana ne bacci sukeyi.....
wata isa ce mai karfin gaske take yawo a sama buuuuu kamar tashin mota zuhraliyya ta d'aga kai sama tayi ido hudu da narjisu,
kawar zuhraliyya tace "ke zuhrali kamar narjisu matar Abraham dama bata nan ance iska taje nemowa da karfi wajen sarki"zuhraliyya ta had'iyi wani miyau a makoshinta tsoro ya kamata fatanta kada narjisu taga yaseer yadda take shawagi cikin duhu cikin bishiyoyi tana kiran sunan yaseer cikin muryar datasaba zuwa masa,
kalle kalle yaseer keyi sama baya ganin komi sai sautin wucewar iska yana cikin sark'ak'iya duhu mai ban tsoro kasa magana yayi tabbas aljana narjisu ce,jikinsa ya kama rawa cikin tsananin kosawa ya kasa amsawa Abraham ya rigada ya daure masa harshe baya ko iya magana inhar dan kansa ne sai in yanason abu,
kamar walkiya zuhraliyya ta bace Abraham ganinta yayi dib cikin dakin muneeba ya fito wanka tana numfarfashi "narjisu narjisu'daga mata ido yayi ta bace muneeba naganin ya fito ta gyara kwanciya tayi kwanciya mai cike da daukar hankali kallonta kawai yayi wani abu ya fito daga idanuwansa ya shiga jikinta,nan da nan ta soma hamma kafin minti daya bacci ya dauketa cikin sauri da zafin nama yabar dakin ya nufi duniyarsu cike da fargabar kada narjisu taga yaseer....
*****
hajiya zainab kwance kan gadonta takeji kamar motsi cikin dakinta takun sahun mutum taji,ta hadiyi wani miyau cike da tsananin tsoro tana kallom kofar daki taga inuwar mutum sanye da kayan bacci tsaye hajiya rabi tayi tana waige waige,momy cikin bakinta ta furta "hasbunallahu wa jiimal wakil,ta fara karanto falaqi da nasi cikin tsoro ta jikin window hasken farin wata ya haska mata fuskar hajiya rabi take ta ganta,sai kawai momy ta kalki hannunta cikin furgici kardai tazo kasheta,adduoi momy ta soma karantowa bataga wani makami a hannunta ba har ta karaso bakin gadon ta waiga babu mai kallonta ta hayo kan gadon tana laluben fuskar momy,runtse ido momy tayi cike da faduwar gaba taji bakin momy tana kokarin tura mata abu a baki momy ta dartse bakinta gamm cikin karfi suka soma kokawa momy taji nauyin hajiya rabi ga cikin,cikin saa da dabara ta cafki dan yatsan hajiya rabi da gurza mata cizo wata yar kara tayi momy ta hankadata ta mike tana fadin "waye wanene?kece wa?"tana kokarin karasawa ta kunna wutar dakin hajiya rabi tayi wuf ta fice daga dakin ta yarda layar a kasa cikin azabar cizon momy,