Sashe 43
Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"nice nusrah yaya dama nace munyi kokarin mu saka karatun kurani kamar yadda momy tace mun gagara shine nace ko zaka taimaka mana yayi'kallonsa husnah kawai takeyi yace"tasamu bacci kubari kawai kuyi kokarin yin abinci kafin momy tadawo"nusrah tace "toh yaya"ta juya ta jikin kofar yake kallon nusrah ya jinnina kai,
wani fitsari husnah taji ganin yadda yayi juyo ya sauya kamanninsa zuwa mummunan halitta mai ban tsoro gajere mai kibar gaske bakinkirin take kallonsa ta tsorata haka ya tako ya hayo kan gadon tanason sakkowa ya fuzgota jikinsa ta tsandara ihu tana hawaye "haba Abraham idan kana sona kuma saika cutar dani?meyasa ka zabi ka azabtar dani da rayuwata?meyasa tun fatko kasan kai waye ka boyemun halittarka yasa na shagala da zanyi rayuwa dakai har karshen rayuwata"yadda take hawaye yasa tausayinta ya kamasa gumi ne ke karyo mata tace "ina yaya yaseer?"tambayar da tayi masa kenan yayi mata wani kallo cike da tsananin kishi wato tambayar yaseer ma takeyi?bazata bashi hakurin amanarsa dataci ba?"husnah meyasa kike tambayar yaseer?kinaso in kashesa ne?"da sauri ta girgiza kai tana fad'in "ah ah ah ah kada ka kashesa dan Allah kadawo dashi naji zanyi rayuwa dakai amma karka tabashi"haushinta yakeji yasan idan ya cigaba da zama zuciya zata iyasashi ya illatata kawai gani tayi ya bace ta durkushe a kan gado ta makalkale pillow tana kuka cike da takaici da tausayin kanta da tsananin haushin momynta Wanda itace dama silar jefata cikin wanan masifar?
*****
shiru cikin gidan babu kowa hajiya saude ke kwada sallama momyn husnah tana sallah tayi gyaran murya "au Ashe sallah kikeyi inata kwad'a sallama baa amsaba kamar ke kadaice ma a cikin gidan"momyn husnah ta sallame ta amsa "nikadai ce hajiya rabi da sadiya da muneeba sun fita babu dadewa sun koma asibiti muneeba babu lafiya"hajiya saude ta tabe baki tace"halan ciki ko?"momy tayi murmushi tace "barka da zuwa kece da rana tsakar nan?"momy ta gyara zama tace "washhh nice wallahi na fita tinda safe ina yaseer?"hajiya saude ta tambaya momy tace "ni ai yau banga yaseer ba ke zan tambaya keda ya kwana gidanki daddynsa na nan ya cika fam yana nemansa muneeba kwana akai da ita babu lafiya,hajiya saude kikabarsa ya kwana da husnah can bayan ga matarsa nan gashi batada lafiya"
"itama husnah ba matarsa bace kenan? dikda yamun laifi hakan yasa ma naje gidansu innah daga can nake mun yanke shawarar zaa fara gyaran sashen husnah zata tare cikin satin nan kafin ayi ciki a gidana dan danki dai sab'ab'awa yayi infada miki yajiwa yata ciwo"kunya ce da farin ciki suka lullube momy sai kuma tace "to hajiya saude ya akai hakan?aljanin yabarsa kenan har ya iya kusantarta?"nan momy ta kwashe yadda sukayi da malam da maganin da ya bayar ta fadawa momy farin ciki ya lullube momy harda hawayen farin ciki tayi tai shiru tana kallon hajiya saude baki bude,
nusrah ce ta sake kiran momy "kai wad'anan yara dake faman kirana tun fitata bansan me sukesoba bari dai in dauka karsu kashemun carji"momynyaseer tayi murmushi idonta ya sauka akan cikin hajiya zainab,ta jinjina kai ta dau wayar "hello"
"momy tin dazun muke kiranki baki dauka kina fita Anty Husnah ta rikice mutanen nata sukazo wai gidanmu daji take gani"dafe kirji hajiya saude tayi momyn husnah dake sauraren nusrah ta firfito da ido waje,
"yanzun ina husnah?me kuke ciki? gani nan zuwa gidan"
"yaya yaseer yazo ai tun dazun saidai kitaho kawai yanzun dai tasamu bacci"ajiyar zuciya hajiya saude tayi ta kashe wayar tana kokarin jan mayafinta "banga ta zama ba gida zani saidai kafin inje gidan zani gidan malam ne insamesa akan husnah in zamuje tarene muje"momy ta rude sosai "ko zamuje tare?"girgiza kai hajiya saude tayi tace "kiyi zamanki kiji da kanki naga abin arziki gashinan saidai naso muyi magana amma hakan bazai yuwuba gara intafi inga halin da take ciki"momy ta jinjina kai cikin sanyin jiki ta zauna hajiya saude ta fice cikin sauri tabar driver waje....shiru momyn husnah tayi take taji wani haushi da tsanar kanta ya darsu a zucuyarta ta furta "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"hawaye suka Shiga zubowa a idanuwanta tambayar kanta takeyi meke damun kanta?shin waye silar batar husnah?take tabawa kanta amsa komi yasami husnah itace sila sakamakon sakacinta....
*****
"boka yanzun fa matar nan ciki gareta na tabbatar da ciki ne boka bana bukatar ya kasance tanada ciki saidai ni insamu"tace cikin tsananin damuwa wata dariya boka yayi yace "dik abinda kikeso shi zaayi da cikin nan idan kince a dauko cikin daga jikinta a dawo dashi jikinki ma zaa iya"ta kalli sadiya,gyara zama hajiya rabi tayi tace "boka da sai nafi kowa farin ciki idan hakan ta kasance inaso kafin inbar wajen nan a dauko cikin matsiyaciyar matar nan azo dashi a sakamun"sadiya tace "niko inaga gara a kashe abinda ke cikinta kisamu naki idan kuma kika haifi dan dake cikinta yazo yana kama da ita fa?"shiru hajiya rabi tayi tace "haka ne kuma kaga boka a halaka abinda ke cikin nata kawai"
"kawai shiyafi"boka ya d'aga wata kwarya sama yayi surkulle hade da Kiran sunan hajiya zainab so uku ya sauko da kwaryar kasa saiga hajiya zainab cikin kwaryar da cikinta "lek'a kigani"ta leka zaune take tana hawaye saidai cikin tsananin mamaki take yadda taga momy da alk'urani a hannunta ya daure mata kai kasa magana tayi ta kalli boka yayi dariya yace "wanan aikin tsafi bazai yuwuba saidai ke zakiyishi rabi"yace a kausashe wani miyau ta hadiye tace "kome zanyi zanyishi matukar abinda ke cikinta zai halaka"ya jinjina kai ya ciro wata laya yar karama da magani a kulle "ki tabbatar wanan layar ta shiga bakinta kota wani hali inhar layar nan bata shigaba to taci abu dauke da wanan maganin an gama amma tabbas sai kinyi dagaske kin jajirce idan ba haka ba abinda ke cikinta zaizo duniya kuma najimi ne"damm gaban hajiya rabi ya fadi zufa ce kawai take karyo mata ta ko ina,
muneeba kuwa cikin kosawa tace "ummah tunda an sallamemu ya kamata muzo mutafi dan yau din nan zan aiwatar da abinda zanyi saina tabbatar yaseer ya tsani husnah wanda zai mata saki uku bai saniba"sadiya tayi murmushi tace "kedai kishi zai kasheki"murgudawa sadiya baki tayi sukai sallama da boka dakyar muneeba ta iya tashi mararta ce tayi mata nauyin gaske kamar cikin ya tsufa....
******
momy na shirin rufe alk'urani taga ana shigowa da kaya cikin gidan Abraham ne ya shigo yana murmushi yace "momy barka da yamma"momy ta rufe tace "yaseer kaine haka?wad'anan kayan fa?"murmushin mugunta Abraham yayi yana kallo ya sadda kansa kasa yace "naje gidan innah ne daga gidan momy shine tacemun husnah zata tare wai shine fa to wasu kudi sun shigo asusun bankina nace bari in siyo mata kayayyaki"momy tayi murmushi tace "allah yayi albarka ,ya jiki. husnah?dazun hajiya saude ta tafi daga nan baa sukuni ba nusrah ta kirata akan ta burkice inaga ma ta biya gidan malam yanzun haka zasu tafi tare"wani miyau Abraham ya hadiye yaji dadin labarin nan dan tabbas idan yaje gidan malam na nan to asirinsa zai tonu zasu gane shi aljanine ba yaseer ba yayi shiru momy tace "yadai?"ya girgiza kai "ah ah bari in karasa sashen muneeba nad'an gaji ne"ta jinjina kai tabi kayan da kallo anata shigowa da hadaddun kayan set na gado wanda sun tasarwa million biyu da rabi momy tace "ikon Allah yaseer kenan"yana kwanar sashen muneeba ya bace daga cikin gidan hajiya rabi suka shigo da faraarta ta tsaida momy dake kokarin shiga daki "ah ah hajiya zainab yadai?wadanan kayan fa zaki canja kaya ne?"momy mamakin ganin hajiya rabi nayi mata faraa takeyi gabanta yadan fadi cikin zuciyarta a hankali bakinta ya furta "hasbunallahu wa niimal wakil"hajiya rabi ta sake washe baki ta jeho mata tambaya momy tace "na husnah ne wanda zata tare"
"tarewa?"suka hada baki harda muneeba ido waje suna kallon momy ta jinjina kai kawai ta wuce tabarsu nan tsaye muneeba wani ashar tayi ta nufi sashenta kamar mahaukaciya.....
*****
shiru malam yayi yana kallon husnah yana karanto addua a bakinsa shi take kallo bakinta nason ta fada musu ba yaseer bane aljanine ta kasa momy ta kallusu nusrah da sukai tsuru tsuru "ina yaseer din?"kallon juna sukai "Yana dakin Anty husnah"
"daga dakin nakefa shigowata bangansa ba"husnah zatayi magana kanta ya sara ta ta dafe kanta malam ya cafki kanta cikin saa ya soma tofa mata addua yana murza kanta da turare....
*WANAN LITTAFIN NA DUHU....300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN ALLAH YA ISA!!!!!*
08036953516
07042277401
*SLIMZY*✍🏻