← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 68

Sashe 34

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
parlorn daddy aka ajiyewa yaseer pillow ya kwanta hajiya rabi na zaune gefensa da mafici tanayi masa fifita innah tace"yanzun a ina muka kwana badamasi?"ta kalli daddy wanda gaba daya ransa yake a hade yace"banida abinda zance tunda kum rigada kun yanke hukunci ammafa kusani yanzun zaa soma artabu da wanan aljanin tunda kuka maida auren husnah da yaseer"innah tace"babu abinda zai faru aibefi karfin Allah ba"hajiya saude ta jinjina kai ta dubi momy tace "ina husnah?"momy tace "tana daki"hajiya saude tace"da ita zantafi can inyaso yaseer idan yanason ganinta sai ya rinka zuwa kafin agama shirye shiryen komawa dakinta"hajiya rabi taji wani abu ya soki kirjinta tabi hajiya saude da kallo tayi jifa da maficin hannunta daddy yace"ban yarda ta koma ba gaskiya ta zauna a nan na tabbatar idan ta koma cen zaa rinka cutar da muneeba ne"hajiya rabi cikin kissa tace"ashe kasani shikenan yanzun muneeba zata zama yar kallo kenan tunda anyi kutun kutun an hada auren husnah da yaseer ni fatana kartaje wadanan aljanun su cutar da ita da abinda kw cikinta"hajiya saude tace"dole zan tafi da husnah kamar yadda baba kabiru yace"daddy ransa ya baci yace"shikenan tunda an nunamin husnah ba y'ata bace amma kusani ku dauketa dik abinda ya faru kar wanda ya nemeni"ya fice daga dakin innah tace"jeki hado kayan husnah"momy ta mike jiki ba kwari ta Shiga dakin husnah tana kwance lamo akan gado tayi nisa cikin duniyar tunanin Abraham gashi tana tsananin sonsa amma bazata iya rayuwa dashiba a matsayinsa na dodo jinnu mai cutar da mutane momy tace"tashi husnah zaki koma gidan hajiya saude da zama"husnah ta mike tana kallon momy jinjina mata kai tayi tace"ki kwantar da hankalinki kinji?zaki dawo nan din idan angama komi na aurenki da yaseer "husnah ta zabura tace "momy aurena da yaseer kuma?"sai kuma tayi shiru tanajin bugun zuciyarta na karuwa momy ta dauko kayanta tace "momy banasom wadanan kayan "momy na kallonta tace "don me?"ta girgiza kai tace "Abraham ne ya siyamun su"momy ta jinjina kai kenan ranan da suka fita da yaseer ashebada yaseer bane da aljani ne?"dire kayan momy tayi yana juyawa ta waigo taga kayan sun bace husnah tana kallonsa ya dauka ya rungume momy ta kalli wajen ta kalli husnah,"ina kayan?"husnah ta muskuta ta sauko tace"maishi ya dauka"momy ta waiga bataga kowa ba ta ruko hannunta suka fice....

yaseer mikewa yayi yace "muje momy in rakaku gate"hajiya saude tace"kamata yayi kaje can ka kwanta a sashen muneeba kayi wanka ka sauya kayan jikinka kaga jikinka dik jini"ya gyada mata kai muneeba tayi saurin rukosa tace"muje"ya kalleta ta gefen ido momy na tafe husnah na biye da ita tana satar kallon yaseer shima satar kallonta yayi ta Shiga mota momy ta shiga su innah nan aka barsu suka wuce....

muneeba ta taimakawa yaseer ya tube ringarsa ta shige kirjinsa ta kwantar da kai tace"yanzun nasan shi kenan munkoma mu biyu muke da kai ko?'ya shafa kanta kawai bayason magana ya janyeta ya shige toilet ta fita ta nufi kitchen cikin takaici take da tsananin kishi tabbas zata nunawa husnah ita rainon mutane ce dan tasan husnah batasan komiba kuma husnah zuciyarta na wajen aljanin mijinta zata kwace yaseer ta rabata dashi kota wani haliz

daure da towel ya fito yana goge jikinsa yayi tozali da Abraham a tsaye cikin dakin yayi wani juyi ya kallesa ya gifta ta gefensa yana zagayesa yacw"kayi nasarar mallakar husnah amma kasani mu biyu zamuyi zaman aure da ita dan bazan taba barinka da ita ba bazaku taba zaman lafiya ba"yaseer ya kallesa ya kauda kai tsoro ya basa yadda fuskarsa ke juyawa yana canja kamanni. daga fari ya koma baki idanuwansa kuwa jujjiyawa sukeyi idan ka kallesa idanuwansa guda shida suka koma zaiyi magana Abraham ya bace....yaseee ya jujjuya bai gansa ba muneeba ta turo kofar da tray a hannunta ta doro flask tana kokarin zubawa ta mika masa taji an fuzge daga hannunsa an watsawa yaseer a jikinsa tafadasshen ruwa ta ware idanuwa tana kallom. yaseer shima ita yake kallo jikinta na rawa tace"bani bace wallahi naji kamar an kwance an karba daga hannuna ne kaji?"ya jinjina mata kai yace"nasani"ta mike ta dauki tray din ya dauki magungunansa ya wetsa ya zura jallabiya ya shimfida dadduma ya tada sallah.....

******
husnah na zaune kan carpet din dakin taji tanajin fitsari ta kalli kofar dake manne jikin bango jikinta ya bata toilet ne ta shiga,

Abraham ne ya fito ta jikin bango ya sauya kamanninsa zuwa yusrah kanwar yaseer ya kalli carpet din take tray na abinci lafiyayye da madarar hollandia ya bayyana ya zauna ta fito sukai ido hudu da yusrah tayi murmushi dikda tasanta tunda sunzo gida sau biyu tace"ga abinci nan nakawo miki kici ki koshi idan ma bazakiciba ni zan zauna muci tare inbaki aike matar yayana ce"Abraham yace cikin suffar yusrah tayi murmushi tace"zauna mucu"a sanyaye yusrah ta zauna husnah nata kallonta sam jikinta ya kasa natsuwa tace"mucu"Abraham ya dibo yakai bakinsa husnah bata ganin tauna bakin yusrah take cinyewa tare sukaci yusrah tace"umm Bari kiga yanzun zan fita yaya yaseer ya kasa sukuni yace zaizo yanzun ya ganki"husnah tayi murmushi tace"nima inaso ingansa kodan insan ya jikinsa"Abraham ya kada kai yadau tray din ya fice yana fita ya bace....

bayan fitar yusrah da minti talatin taji an turo kofar da sauri ta zabura cikin tsoro tana ganin yaseer taji hankalinta ya kwanta cikin shagwabarta data zame mata nature tace"saida kazo ko?ya jikin naka?"zama yayi gefen gado yace"da sauki tayaya zan iya zama can bayan kina nan?"husnah tayi murmushi sam batajin sonsa ko kadan a zuciyarta saidai idan suna tare tanajin faduwar gaba miko hannu Abraham yayi yace"taho nan muyi wata magana"wani yarrr taji ta yaya yaseer zaice ta kawo hannunta?daga zuwansa dikda ance an maida aurensu?"ya tsareta da ido wani abu ne ya fito daga idonsa ya shiga jikinta ji tayi ta gagara yi masa musu ta tako ta taho a hankali ya dorata a cinyarsa ya rungumeta yana sauke numfashi yana shakar kamshin jikinta yace "ummm inason kamshin jikinki koba turare"take maganar Abraham ta fado mata yana yawan cewa yanason kamshin jikinta koba turare,yawo ya somayi da hannunsa a jikinta tace"yaya yaseer kadaina"Abraham yayi murmushi yana jifanta da wani kallo mai cike da shaawah

momy ce ta shiga dakinsu yusrah suna zaune suna kallo nusrah na danna waya tace"ku dauko radiom dakin bakin can kusa memory card din nan kusa karatu cikin gidan nan yanzun nan shima ayi connecting dinsa da Bluetooth akai dakin husnah kuma karku rinka barinta ita kadai" nusrah tayi narai narai da ido tace"nidai tsoronta nakeji ina tsoron aljanu"momy tayi tsaki tace"tunda dodo ce ko dallah kutashi kuyi abinda nasaku yanzun zan kira malam muyi magana a soma karbar magani,

husnah nagani yasa bakinsa a nononta yana tsotsa yana liliya dayan tace"yaya yaseer ka bari "Abraham ya kasa magana yayi missing dinta sosai hawaye suka ciko a idon husnah tace"kabari yaya yasee"kenan dama yaya yaseer dan iska ne?tace a ranta nusrah data nufo dakin taji husnah cikin wata murya tana fad'in "yaya yaseee ya bari"dafe kirji tayi yaushe yayansu yazo gidan nan?

*LITTAFIN DUHU NA KUDI NE 300 MAI BUKATAR SIYA YA TURA KUDI TA WANAN ACCOUNT DIN*

3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK

*SHAIDAR BIYA TA WANAN NUMBER KO KATIN MTN 08036953516*

*SLIMZY*✍🏻
31
Abraham na rike da kwankwason husnah yana kara mannata da kirjinsa yana in fanta da wani kallo mai cike da so da kauna itama kallonsa takeyi mamakin yaya yaseer takeyi kici kicin kwacewa takeyi ya shafa kanta ya rad'a mata a kunne"kin manta an maida aurena dake?"yace tace cikin wani irin yanayi mai cike da kasala"idan an maida aurenmu yaya sai kazo kana tabani kuma a gidan momy?"shhhhhhh yace"momy ai tasan ni mijinki ne?"jikin nusrah ne yayi sanyi ta tabe baki ta juya ganin gilmawar mutum yasa husnah saurin turesa tace"gashi nan ai yanzun kaja momy ta ganmu"Abraham ya waiga ya kalleta yace"ba momy bace saidai su nusrah bari inje insamesu inci mutuncinsu"tura baki tayi ta hararesa ta zauna gefen gado bugun zucuyarta ya tsananta Abraham na fitowa yayi murmushi ya rikid'a daga kamannin yaseer ya koma kamanninsa yayi mik'a ya kalli kofar dakin yana hangenta zaune gefen gado ya girgiza kai yana tsananin sonta dikda yasan tana sonsa wanan shegen bil'adaman ne ya shiga tsakaninsa da ita amma yanzun aka fara wasan,ya bace,

daga kitchen nusrah ta fito da tray na abinci sukai kicibis da nusra tace"yadai naganki kindawo ina abinda momy tasaki kiyi?"kallon kofar dakin husnah tayi tace"naje na tarar da yaya yaseer ciki yazo"zaro ido nusrah tayi cikin mamaki tace"yaya yaseer kuma shida momy tace tabarosa can gidansu ya kwanta dakin Anty muneeba yayi accident fa?tayaya zai kamo hanya yazo"ta wuceta tace"ni matsamun in kai abincin zanyi sallama idan ma yana ciki zan shiga abuna"tabe baki yusrah tayi ta wuce,

dakin momy yusrah ta shiga ta tarar da ita tana sallah ta zauna gefen gadon ta jira momy ta idar kallonta momy tayi tana kallon hannunta tana jiran karin bayani yusrah tace"naje zansaka karatu na tarar yaya yaseer yazo yana dakin shine nadawo"

"yaseer kuma?au da yace zai biyomu naki yarda shine daya shigo gidan bai fad'amun ba?"momy ta yunkura ta karbi radiom "muje inci masa dan tselen uwa"yusrah ta rufawa momy baya,

husnah na zaune gefen gado nusrah cikin tsoro tace "Assalamu alaikum"da sauri husnah ta juya ta amsa tana murmushi ganin nusrah da tray din abinci ya bata mamaki tace "ah ah yusrah ta kawomin abinci har munci tare fa yanzun"daidai nan momy ta shigo tana fad'in "ina yaseer din?"husnah ta sadda kanta kasa tace"ya fita momy nadauka ma ya taho wajenki ne"

"ta ina zai taho wajena bayan yasan yadda mukayi dashi?nace ya kwanta ya huta shine ya kamo hanya yazo batare da nasaniba ya shigo zanyi maganinsa"momy ta kalli nusrah dake rike da tray a tsaye tace"ki ajiye mata tray din mana"
Chapter 34 · 0% Book details