Sashe 44
Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
37
bankad'a kofar dakinta tayi ta shiga ta yarda gyalenta ta zauna gefen gado ta dafe kanta sadiya tsaye tayi a jikin kofa tana kallon hajiya rabi cikin damuwa da rud'u "lallai matar nan wato manakisar da suke hadawa kenan batare da munsani ba?shirye shiryen tarewar husnah akeyi a cikin gidan nan?tabdijan inko inada rai bazan taba bari husnah kota tare ta zauna lafiya ba"ta mike tana numfarfashi,
"ki kwantar da hankalinki yarinyar nan da ake maganar tariyarta da yaseer ba son yaseer dim takeyiba zuciyarta na tare da Aljan mai zai d'aga miki hankali?abu daya zakiyi ki tada tarzoma idan Alhaji badamasi ya dawo Shi kadai ne zaki bullo ta wajensa ki wargaza komi sanan kisan yadda zaki kafin ki halaka cikin can na waccen bakar dagar kisa masa tsanar cikin yasa a ransa lallai ba cikinsa bane"sharce gumin da ke karyo mata tayi idanuwanta jajir tace cikin dimuwa "kunnamun fankar can ni gaba daya gumi nakeyi ma"sadiya dake tsaye ta daga kai ta kunna fanka ta sa hannu ta gefenta ta kunna makunnin AC ta jikin bango ta dawo ta gefen ummah ta zauna "haba yaya har wanan dan abun zai tada miki da hankali?kin tsaya cikin damuwa bayan ga babban gagarumin makami boka ya baki ai yanzun kwantar da kanki zakiyi ki tabbatar ta saki jiki kin bata wanan maganin taci kuma kisan yadda zaki cikin dare har layar kisa mata a bakinta kamar yadda yace kinga karama ce tsaf zata hadiyeta cikin bacci"murmushi hajiya rabi tayi hade da sauke ajiyar zuciya ta zuge jakarta ta ciro maganin tana jujjuyawa "zainab kenan saidai wata bake ba Baki isa kiyi ciki ki haifesa a cikin gidan nan ba da raina da lafiyata yadda nayi nasarar aure miki miji haka zanyi nasarar halaka abinda ke cikinki"jinjina kai sadiya tayi tace "har naji dadi banaso ki rinka karaya yaya bayan kedin macece mai kamar maza na tabbatar zaki iya"
"zan iya"tace hade da sauke nannauyar ajiyar zucuya ta mike tace "ina zuwa"ta fice sadiya tayi murmushi ta harde hannuwanta a kirjinta....
******
muneeba tsaye a gaban gas ta cika d'akin da kamshin abincu da takeyi saidai bata cikin hayyacinta surutai takeyi kamar wadda ta zare tsananin kishi da ya turnuke ta"ni yaseer zaiyiwa haka?ashe dik abinda suke kullawa Kenan shiyasa har yaje can ya kwana?wanan munafukar uwar tasa sai naga bayanta babu wanda zaisa inyi zaman kishi da matar aljan"tace a fili ta ciro maganin da boka ya bata tasa ma yaseer a abincu tana cikin kwashe abinci taji motsin shigowar mutum tad'an sak'e a gefenta ta juya baya "waye?waye nan wajen?"tayi shiru tana saurare turo kofar Abraham yayi ya shigo ajiyar zuciya tayi ganin yaseer ne Tayi masa wani kallo sanan tq d'auke kanta gefe daya ita a dole fushi,
Abraham ya tsaya daga bayanta ya zuro hannunsa kwankwasonta ya rungumeta sosai badan yaso hakan ba sam bayaso ta harbo jirgin shiba yaseer bane "yadai fushi kikeyi dani?"ta jinjina masa kai cike da takaici sai kuma hawaye ya fara zubowa a idonta yad'an joyota ya hadeta da kirjinsa ya rungumota "nasan kukan mai kikeyi ki kwantar da hankakinki husnah baxata taba kama kafarki a wajena ba kinsan yadda nake sonki ai badan nasoba zaa maida wanan auren saidan umarnin mahaifiyatq"da sauri ta kallesa tana hangi gaskiyar sa a kwayar idonsa ya lumshe idanuwansa Abraham yayi kissing goshinta ta sauke ajiyar zuciya ta kara shigewa jikinsa yayi mata rumfa "yaya yaseer banaso wata mace ta rab'eka tsananin kishin da nakeyi akanka zan iya hallaka kaina dik ranan da na wayi gari ka tare a d'akin wata bayan ni"ya jinjina kai Abraham ya cije lebe ya dan janye jikinsa "nafada miki wanan tariyar badan nasoba zaayita dik abinda zakiga nayi zanyine kawai dan farin cikin momy bawai dan inaso har cikin zuciyata ba kidaina tada hankalinki akan wadda batasan itadin waceceba ma"murnushi muneeba tayi cikin tsananin murna da farin ciki tabbas aikin boka da yayi kafin subaro ya soma aiki yau yaseer da kansa yake fad'a mata wad'anan kalaman?da wadanan kalaman zatayi amfani wajen yakar husnah ta kara tabbatarwa kenan mahaifiyar yaseer baa zaune take ba,ya tsareta da ido tad'an kallesa cikin shagwaba tace "kana kallona nayi kyau ne?"ta juya baya ta kada masa mazaunanta murmushi Abraham yayi yace "sosai kinyimun kyau matata wanan cikin kara miki kyau yayi"tasa hannu ta rufe fuskarta yace "bari in d'an watsa ruwa kafin kingama"ta jinjina masa kai ya wuce yana fita ya rufe kofa yayi mik'a ya kalli bango ya tsage ya shige ta ciki...
*******
tari sosai husnah keyi sakamakon hayakin daya turnuke parlorn cikin tausayawa hajiya saude ta girgiza kai tace"sannu husnah"ta jinjina mata kai idanuwanta sunyi jajir malam ya tsareta da Ido yace"ta wani suffa yake zuwa miki?"tayi shiru bakinta na karkarwa ta sunkuyar da kanta kasa tayi masa bayani "yana zuwa mun a mutum a siffar dana sanshi da ita watarana Dodo"ta fashe da kuka "la'anannen Allah shedani in Allah ya yarda saiya rabu dake husnah"cewar hajiya saude a fusace malam ya jinjina kai yace"ya taba kusantarki?"ta girgiza kai "Alhamdulillah tunda bai taba kusantarta ba inshaaa Allahu idan har kun dage zai iya rabuwa da ita wanan turaren da nayi mata bazai taba iya kusantar jikinta ba"momy ta jinjina kai cike da gamsuwa ya cigaba da magana "yadda kika jajirce akan ta hajiya indai kundage zai rabu da ita sanan kar mujinta ya nisanceta idan so samune kamar yadda kikace zata tare to ta tare a gidan nata sanan kar a rinka barinta ita kadai a daki tunda tana fama dasu shima zai bada gudun mawa wajen kara zamansu a tare da ita dik runtsi ya zamana tana tare da wani ko wata"ajiyar zuciya momy tayi tace "yanzun malam baka ganin zai cutar da mijinta?"ya girgiza kai yace "tunda har mijinta yayi nasarar kwanciya da ita kadarinsa ya karye akwai abinda zan baki kiba mijin nata shima ya rinka amfani dashi"momy a fusace tace "nusrah daukomin wayata in kira yaseer ja'irin yaro saboda yasan yana gudun fad'ana yasa ya gudu jin nadawo yazo kuyi magana kayi masa bayani"nusrah ta karasa dining table ta dauko jakar momy ta mika Mata ta ciro wayarta tayi dialing number yaseeer kawai sukaji ringing din wayar yaseer cikin daki,tsaki momy tayi "a d'aki yabar wayar"bakin husnah na rawa tanason tayi magana ta kasa kallon glass din window tayi fuskar Abraham ta gani ta kalli glass din dake gefe nanma shi tagani ta sunkuyar da kai "mai kikeso ki fad'a husnah?akwai abinda kikeso kice fadamun menene karki boye idan kika boye zai cigaba da cutar dake"kwalla ta cicciko a idanuwanta muryarsa takeji can nesa kamar a iska "idan kika fada musu niba yaseer bane zan kashe yaseer "damm gabanta ya Fadi "ki fada mana menene?"hajiya saude tace cikin kosawa ta girgiza kai kawai "hajiya akwai abinda takeson fad'a ina zargin akwai wani wanda yake tsoratar da ita musamman yadda take kallon gefe taki magana,yana kusa ko?"ta jinjina kai tana hawaye malam ya kada kai kawai ya ciro wani koren magani "hajiya kinada nono?"momy tayi shiru tace "banidashi amma akwai yoghourt "
"nusrah dauko yoghourt a fridge"nusrah ta tafi kitchen tana shiga tayi kicibis dashi tsaye taja da baya zatayi ihu ya bace jikinta na rawa ta dauko ta kawo yace "wanan maganin zan bata Tasha sakamakon kema kin taimakeni amma bakowa nake bamawa ba saboda wuyarsa"ya mika mata "juye a kopi"ta juye tasa yoghurt ta mikawa husnah hannunta na rawa ta karba ta soma sha tari ya turnuketa "karasa shanyewa kinji?"ta shanye yace "alhamdulillah wanan da kike gani,maganine bishiyar maganin inda take unguwar da akwaita aljanu basa zama wajen nabata ne kawai amma badan zaki iya biyana ba saboda yanada wahalah"momy ta daga hannu ta godewa Allah gumi ne ya karyowa husnah tadan jingina tana sauke numfashi ji tayi jikinta tamkar ba nata ba,"Mai kikeso ki fada dazun?"tace "dama yaya yaseer bashi bane Abraham ne"momy ta kalli malam ya kalleta "anya husnah"ta jinjina kai momy tace "malam kodai yana rikidar da fuskar yaseee ne a matsayin nasa yasa take ganin kamar shine ba yaseer ba?malam yace "zai iya yuwuwa,amma kisa ido zanbaki abinda zakiyi idan har ba yaseer bane to zaman gidan bazai yuwu masa ba"
"Tou shikenan"ta ja ajiyar zucuya,husnah ta mike yusrah ta rukota suka nufi daki malam ya bata komi yadda zatayi ta karba tayi masa godiya