← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 68

Sashe 18

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Abraham ne yazo a suffar malamin da hafeez ya kira bai saniba yacev"ai kasan su aljanu musamman bakake mugunta garesu sai an mike anyi dagaske sanan"hafeez ya jinjina kai yace "muje ko?"ya bude motar daddynsa da ita zasu fita ya shiga Abraham ya shiga ya zauna a gaba hadeez yayiwa motar key yayi horn mai gadi ya bude gate suka fice..... tafe suke hafeez cike da mamaki yakeyi yana satar kallon malam ibrahim Wanda ke zaune a gefe Abraham ya rikida ya koma yadda yake hafeez na kokarin parking a kofar gidansu husnah yana juyawa sukayi ido hudu da Abraham ya furgita sosai yana kallonsa yana murmushi yace "kadai dage saika rabani da husnah ko?ka dage saika bakunci lahira ko?"hafeez ya girgiza kai cike da tsananin tsoro"Abraham yace "banso na fito maka a ni bane yanzun amma hakan be yuwuba saboda yadda zucuyata ke azalzalata niba mugu bane amma kun dage kaida iyayenku sai kun rabani da husnah ko? niba mugu bane amma kuna kokarin koyamun mugunta sakamakon dagewa da kukayi ganin kun rabani da masoyiyata abar kaunata ko?tou zamu kulla zamu saka kafar wando daya daku dukkanku zan batar dakai zan kasheka"yace cikin kakkausar murya cike da tsananin fushi addua sosai hafeez yakeyi a bakinsa suna kallon kallo shida Abraham ganin adduae da hafeez keyi yasa ya bace daga cikin motar shiru hafeez yayi ya kifa kansa da sitiyarin motar cikin furgici tsaf aljanin nan zai rabashi da ransa amma yaci alwashin ganin husnah tasamu lafiya koda zai rasa rayuwarsa, fitowa yayi daga cikin motar ya nufi gidan ya tura kofa tozali yayi da husnah zaune tayi tagumi tana ganinsa ta mike ta tsaya ta nufoshi da sauri "yaya meyasameka?"tambayar da tayo masa yasa gabansa ya fadi Yana kallonta cike da tsananin so da kauna ta kalli goshinsa cikin rawar murya tace "kaji ciwo"ya jinjina mata kai yace "zonan zo"ya yafitota tana kokarin zuwa Abraham ya shiga jikinta kallon dayaga husnah tayi masa yasan ba ita bace wucewa tayi ta canja hanya ta nufi bayan gida da ita ya fita a jikinta ya tsaya Yana mata wani kallo tsoro da furgici ya kamata metayi masa yadda taga yana canjawa yasa ta furgita zata gudu ya fuzgota ta fada jikinsa ya matseta cikin karfi tayi yar kara yace "kin isa da aurena ki rinka magana da wani?ba nace ki daina kulasa na bakijiba ko dama ba sona kikeyi ba karya kikeyi?"kishi ya rufewa Abraham ido sam bega hawayen dake zuba a idon husnah ba tsabar azabar dataji rukon da yayi mata ya cigaba da magana yace "babu wanda zai rabeki ya zauna lafiya koda uban daya haifeki ne"ta fuzge daga rukon da yayi mata tana hawaye jikinta na rawa iska ce ke kadawa buuuuuuu a wajen tace "mahaifina fa kace Abraham mahaifina kake zagi?"a Karo na farko da husnah taji zafin Abraham tace "karka sake mummunan furuci akan mahaifina dik son da nakeyi maka zan iya hakura dakai'yana kallonta idanuwansa sukayi fari soll hawaye ya wanke mata ido yace "tou shikenan ki gwada in bakisan wayeni ba zan nuna miki cikakken ni aljani ne bazan taba Bari kiyi rayuwa da kowa ba saini nafada miki kuma zan baki mamaki zam horar dake yadda bazaki kara mun kuskuren abinda kikai ba"ya bace ta durkushe a wajen tana kiran sunansa "Abraham..... Abraham kadawo kayi hakuri nayi kuskure kasan ina sonka"kuka takeyi kamar ranta zai fita tana waige waige tana nemansa cikin kuka ta taho ko ganin gabanta batayi sukai karo da yaseer wanda shima besan da ita ba ji yayi sunyi karo ta fada jikinsa tana kuka ta rungumesa kammm "nasan bazaka nisancemiba Abraham kar kayimun haka kadawo ko nasan bazaka tafi kabarnina"yaseer ya tureta yana kallonta kamar zararriya take kallonsa idanuwanta sunyi jajir sum tattashi yana kallonta tana canja masa cikin wani irin yanayi yake kallonta lokaci Daya idanuwansa ke haska masa wata yarinya mai suffarta wadda yayi rayuwa da ita a Baya saidai besan wacece ita ba...

****
muneeba cikin zumudi take labe a cikin bedroom dinta ta kita ummahnta tana dauka tace"albishirinki ummah"cikin kosawa da son jim mai yar zatace tace "goro meyafaru muneeba"
muneenba tayi murmumushin takaici tace"yaseer ya taho cikin gida da takardar sakin husnah saki uku ya taho ya kaiwa momy takardar yanzun haka"tsalle hajiya rabi tayi cikin tsananin farin ciki tace "Alhamdulillah"suka sheke da dariya hajiya rabi tace ",ina nam inata tunanin abinda yaseer yasha zaisa ya dawo hayyacinsa idan ya dawo hayyacinsa ma a banza tunda saki uku yayiwa husnaj kinga babu aure tsakaninsa da ita harabada"muneeba farin ciki tayi tsalle tana rawa ta kashe wayar

Abraham ne ya shige jikin husnah ya sauya mata kamanni yaseeer gani yayi tana rikidewa ta koma wani gabjejen mutum mai ban tsoro lokacin da take kara nufosa aguje ya nufi cikin gida cikin kidimewa ita kuma husnah tsoro yasa ta zube a kasa tana kiran "momy momy ki gudu ga zaki nan zai kasheku ku gudu"ihunta yasa su momy da hafeez fitowa jin abinda take ambata ita a zaki take ganin yaseeer mai mummunan kama ita kuma ganin yadda take rikida yasa yaji tsoro yayi cikin gida yana sassarfa

gidan ke juya mata iska ta ko ina take kad'awa a hankali takebin ko ina da kallo yana sauyawa bakin kirin duhu ya garwaye ko ina bata ganin gabanta bata ganin bayanta ta kara tsandara ihu ta fadi ta zube.....

*WANAN LITTAFIN NA DUHU NA KUDI NE WANDA YA KARANTA BAI BIYANI BA ALLAH YA ISA!!!*

KI BIYA 300 TA WANAN ACCOUNT NUMBER DAKE KASA KI KARANTA CIKINSALAMA

3126584401
FIDDAUSI MUSA
FIRST BANK

SHAIDAR BIYA TA WABAN NUMBER 08036953516 KO KATIN MTN TA NUMBER

21
Chapter 18 · 0% Book details