← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 68

Sashe 51

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ku mutafi abar kayan in zamu dawo zamu biya mutaho da malam nida yusrah sai yayi saukar alkurani a daga kayan"momy tayi gaba tana gyaran gyale yusrah a tsorace take har yabzun komi sanyi sanyi takeyi suka fita a tare suka rufo kofar shiga sashen tare suka dunguma a dayar motar yaseer dake gidan suka fice....

*****
innah ce da sauran kannen daddy suka sauka a gidan cikin farin ciki momy ta karbesu ba zata sukai mata dan batayi tunanin biki zayi karamin biki don tarewar husnah da yaseer ba,
"wai nikam har yanzun angon nawa bezo bane? inaso yazo ya zaba koni ko husnah ko mai waccen cikin kamar kwallo"ummah hadiza ta sheke da dariya tace "innah kenan so kike ki daukar mana magana ko kinsam cin mutuncin da rabi tasa mai gida yayi mun kuwa?"innah tadan ja da baya tana kallon ummah hadiza shekeke cike da son karin bayani ganin haka ummah hadiza ta gyara zama momy ta tabata ta girgiza mata kai alamar kada ta fada ta kauda kai "kyaleni zainab nafada gara tasan cewa danta ya kusan kwarkwancewa"nan ummah hadiza ta kwashe komi ta fadawa innah salati kawai innah keyi muniba ce ta fito daga sashen mahaifiyarta da Anty sadiya ganin taron jamaa yasa tayi turus tana kallonsu daidai innah tayi dariya cike da tsokana tace "au bazaki gaisheniba muneeba?ko har yanzun kishin kikeyi dani?dama kin gaisheni mun hadewa husnah kai dayafi dan na tabbatar idan ta tare yau kema da akayimun kishiya dake dena yayinki zaiyi"hajiya rabi ta fito tana fad'in "me kukeyi baku tafi ba inace tace batajin dadi ne?"muniba idonta ya cicciko ta kalli hajiya rabi tace "ummah Ashe bikin tariyar husnah akeyi?"gaban hajiya rabi ya fadi dik dauka wasa akeyi tayi ta kalli cikin parlorn momy ta hangi mutane zazzaune anaya ciye ciye,

"au bakisan yau kishiyarki ke tariya ba ina mijin naku?ko be fada miki ba?"ana haka su yaseer sukai sallama a tare suka shigo da husnah suna gaba momy da yan biyunta na baya wani kallo muneeba tayi musu lokaci daya taji wani abu ya caki zuciyarta kamar mashi DUHU ta soma gani kafin daga bisani ta saita natsuwarta innah kuwa cikin rawan jiki tq tashi tana kokarin gyara daurin zani tace "yauwa Alhamdulillah gashi nan ma mijin namu yazo kai yanzun haka akeyi ashe muniba batasan yau ake tariyar amaryarta ba?"rasss gaban yaseer ya fadi ya kalli muniba ya kalli cikin dake gabanta take yaji wani yarrrr idonta cike da hawaye hajiya rabi tace "kayi magana mana?inace ko dazun ka kwana gidan nan ka fita ashe fitar dakayi zuwa kayi dauko matarka"momy dake gefe tsaye lokacin tace "au bakusan fa da aljani kuketa rayuwa kwana da kwanaki ba,to ba Yaser bane wanan shedanim aljanin ne yake zuwa a matsayin yaseer"wani jiri muneeba taji yana kokarin kadata ta dafe kirji dama aljani take runguma tayi baya zata fadi da sauri yaserr ya rukota tare da Anty sadiya ta kara narkewa kawai ta fashe da kuka kamar jira takeyi,

hajiya zainab ce ta fito daga daki tana fadin "Aljani hajiya saude wallahi jikina ya bani ba yaseer bane nadai kasa gasgata cewar bashi bane din innahlillahi wa innah ilaihi rajiun ashe mun auna arziki sace yaseer din yayi kenan?"momy tace "mu Shiga daga ciki"ta kalli Yaseer ta watsa masa harara tace "ah sh a cikin mutane take shigewa jikinka kamar wata mage?ko akanta aka somayin ciki ne?ka kaita daki ka dawo yanzun yanzun banson rashin kunya"jikin yaserr na rawa ya rike muneeba tare da Anty sadiya suka wuce sashenta hajiya rabi kuwa ta cika famm kamar zata fashe tsananin bakin ciki yasa ko ganin gabanta batayi haka ta nufi sashenta,

suna shiga sashensu yayi bedroom da ita narkewa tayi a jikinsa ta soma rera kuka shafa kanta yakeyi cikin sigar lallashi "kukan me kikeyi?baganiba nadawo inda bandawoba ina duniyar aljanun fa?"ta girgiza kai ta share hawayenta "Alhamdulillah tunda ka dawo amma yanzun yaseer haka zamuyi rayuwa tare da aljanu?tarewa da husnah yanzun ba karamin masifa bane"Hade rai yayi yace "karki sake kiran husnah masifa kinji nafada miki idan ba haka ba zan sassaba miki akan me?don kawai kaddara tasameta"kuka ta fashe masa dashi "aini nasan baka sona tuntuni dama ita kakeso nasan zan fuskanci bakin ciki nasani"shiru yayi jiki a sanyaye ya shafa sumar kanta gumi ne kawai yake karyo mata kishi yake hangowa karara a kwayar idanuwanta yace "ki kwantar da hankalinki kinga ga abinda kike tare dashi yanzun idan kika tada hankalinki kinga wani abu zai sameki da abinda kw cikinki"cike da shagwaba ta tura baki tace "to ba kai bane yanzun shikenan bani kadai gareka ba bansan yadda zanyi da kishinkaba mijina ina tsananin kishi akanka"fuskarta ce yake gani tamkar husnah irin wanan shagwabar takeyi masa wanda ya fahimci cewar nature dinta ne shagwaba yayi nisa cikin tunani ta bugi kafadarsa tace "kayi shiru"

"yi hakuri husnah"ta kallesa da sauri ya dinke bakinsa wani kallo tayi masa ta juya masa baya yana kokarin janyota yaji wayarsa ma ringing ya duba momy ce be dauka ba ya barta ya fita,

yana fita ta mike ta zauna tayi wata ashar davsauri sadiya ta shiga dakin tana jijjiga kai "tabbas sai kin shirya muneeba sai kuma kin iya kissa dan naga an juyawa yaseer kwakwalwa"muneeba ta kasa magana tsananin tashin hankalin da take ciki....

*****
tsaye suke a zagaye da Abraham tunda ya dawo duniyarsu baya magana dik maganar da baba da mama sukeyi masa fuskarsa ce take fidda wani abu kamar mai bakinkiirin dik shedar wuta a jikinsa musamman wuyansa ya dago kai ya kalli mahaifiyarsa da nad'in mayafin dake kanta dakyar ya bude baki cikin wata irin murya mai ban tsoro yace "HUSNAH..... yau husnah da kanta ta zubamun abinda zai cutar dani?"wasu hawayene na jini ke zubowa daga idonsa dake fidda wani mai mai har har yanzun hayaki ne ke fita akansa,
daga gefensu wata dattijuwa ce baba kande tace "Abraham ka kasa hakura da husnah ko?husnah ba jinsin ka bace dikda na tausaya maka nasan irin yadda ka nuna mata soyayya amma ka duba kaga yadda wadanan biladama suka kona ka"ya kalleta tana tsaye da sanda a hannunta jikinta na kyarma saboda tsufa yaceb"husnah ina sonta ina tsananin kaunarta nina reni husnah nine na tseratar da ita daga shedanum aljanu lokacin da mahaifiyarta ke kwantar da ita a daki ita kadai lokacin nake zuwa nake wasa da ita harta shiga raina husnah tana sona"

"bata sonka Abraham inda tana sonka bazata taba konaka ba amma kuma wanan karon bazan hanaka daukar fansa akan wanan bil'adamar ba"jinjina kai Abraham yayi tare da wata kuwwa mai karfi saida iska ta tashi cikin dajin bishiyoyi ke kadawa da ganyayyaki yace"saina koma gareta bazan barta haka ba zan dau fansa akanta sanan wanan abun dake cikinta sai ya zama nawa"jinjina kai mamah tayi cikin tausayawa suke kallon yadda fuskarsa tayi kwanciya yayi a kasa saida kasar wajen ta girgiza iska ce kawai take tashi yana dafe da kirjinsa idanuwansa a rufe rufff wanan hawayen na jini nabin gefen fuskarsa cikin tunani yake ita yake gani lokacin da take watsa masa ruwan magani akansa jikinsa na salubewa....tunowa da yadda take tarairayarsa da tsananin kauna da soyayya lokacin da take duniyarsu tunowa da yadda suke kwanciya suna farantawa juna rai yayi yadda take shagwabewa idan tanason abu.....kuka yakeyi jikinsa na karkarwa zuhraliyya ce a gabansa besaniba kallonsa takeyi cikin tausayawa ya bude idonsa yana kallonta tana kallonsa yace "ki kwasarmun kayana dake gidan da nayi rayuwa da husnah ki kai gidan husnah Sabo"cikin damaucewa take kallon yadda jikinsa yayi amma hankakinsa na kanta?tayaya zata dumfari gidansu husnah bayan ga kunar dake jikinsa?bacewa yaui bata gansa ba tana waige waige ina yaje?"

dakin hajiya saude ta dira kayan na inda suka ajiye kallon kayan kawai yayi suka bace ya zarce gidansu husnah da yaseer inda zasu zauna yana shiga gate din yana bin ko ina da kallo yana jinjina kai a hankaki rayuwarsa da ita yake tunawa yana kokarin Shiga ta bango ya kasa dik yadda yayi sakamakom karatun alkurani da yakeji yana tashi a gidan,

momyn husnah ce ta dibo maganin da hafeez ya kawo bayan yaseer ya shigo su hajiya hafsat suna masa fada tace "yauwa ga wani magani nan sa hafeez ya kawo ya tabbatar mun inhar Tasha sun rabu da aljanin nan"

"hafeez kuma momy?"Yaseer yace yana maida hankalinsa kanta cikin kishi yace "ban amince tashaba ai nine mijinta yanzun idan tasha ta warke shikenan fa ya zama shine sanadin rabuwarta da aljanin can bayan nine nayi alkawarin kashesa"cikin takaici yake maganar hajiya saude ta karbo kofin dake hanmun momy ta mikawa husnah dake zaune gefe ta tankwashe kafa ta lula tayi nisa cikin tunanin Abraham,

ummah hadiza ta ciro turaaren da hajiya saude ta bata shigowarsu tace"karbi wanan maza nasa akai rushi gidan kaje kasa turare"ya karba yana kallon sashen da husnah ke rike da kofin magani ya fuce cikin takaici.....

*****
muneeba kuwa tsaye tayi rike da kwankwaso tace "nasha alwashin Bazan taba bari yaseer yayi rayuwat jin dadi da husnah ba ke yau din nan ma bazan bari ya kwana tarw da ita ba"sadiya ta jinjina kai tace "dakyau haka nakeso".....

*WANAN LITTAFIN NA DUHU 300 KACAL ZAKI BIYA KI MALLAKI NAKI IDAN BAKI BIYABA KIKA KARANTAMUN BAN YAFEBA*

07042277401
08036953516

*SLIMZY*✍🏻

42
Chapter 51 · 0% Book details