Sashe 54
Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"tou Tashi maza kije kiyo alwala kizo kiyi sallah kema kin zauna kin tasata a gaba tana sallah ke kinyi tagumi ko kinada wata damuwa ne?"girgiza kai kawai tayi idonta cike da hawaye sam tarasa meke damunta wani irin kunci takeji a cikin ranta wanda batasam dalilinsa ba dakyar take taka kafarta ta shiga bedroom dinta ta jikin windown glass taga kamar mutum tsaye ta kurawa glass din ido taga yana budewa yana rufewa wata murya taji ana mata magana wani haske kamar walkiya daga jikin glass din ya taho ya nufo jikinta kafin tayi wani abu ya Shiga jikinta kasa shiga toilet din tayi ji tayi kawai bazatayi sallahr ba bataso ta nemi waje ta zauna "ina miki magana?bazaki kulani ba?"ta juya bataga kowa ba cike da damuwa tace "wai waye keson takurani ne?waye kemun magana"cikin kosawa tayi maganar tana waige waige ajiyar zuciya taji anyi hade da fad'in a sanyaye "husnah mijinki ne ina sonki husnah husnah ina sonki karki rabu dani gashi baki ganina yanzun nayi kokarin ki koma ganina abun ya faskara,amma inaso in kasamce dake karkiyi alwalar nan kinji?"wani abu taji yarrr yadda yayi maganar ya matukar bata tausayi dikda takasa tuno muryar da akeyi mata magana,ummah hadiza ce ta shigo hade da turo kofar ta zabura ganinta "husnah me kikeyi zaune gefen gado ke kadai?inace an hanaki zama ke daya anzo ana miki magana ko?"ta kalli window gani tayi ana hura window yana gaba yana baya yana fadin "karki fada"ta girgiza kai ummah hadiza ta cije lebe "baki sallahr ba kenan?"ta dago kai ta kalli ummah hadiza taga ta tsareta da wani kallo na tuhuma tsoro ya kamata ta girgiza kai "banyi ba ummah nashigo dakin kawai naji banaso inyi ummah kibarni Dam Allah"ruko hannunta ummah hadiza tayi batace komiba ta nufi toilet da Ita ta shigar da ita ta dauko buta ta mika mata "maza yi alwala kiyi ina kallonki ki fito zan jiraki kiyi sallah wato an fito da tsurfar hanaki kiyi sallah ko?"babu musu husnah ke alwala tiryan tiryan suna fitowa sukaji anja wani mugun tsaki hade da kwafa husnah taja da baya tana kallom ummah hadiza cike da tsoro tace "kinjifa kinji ummah?"tsaki tayi kawai ta shimfida mata dadduma "oya maza tada sallah kafin raina ya baci idan kin idar kizo kiyi hayaki kafin mijinki ya dawo nina rasa ina yaseer ya shiga ma mtswww"husnah ta tada sallah ummah hadiza na zaune gefen gado harta idar ta kama kanta tayi mata addua tace"tashi muje bazan barki ba nasani ko zai shigo tayaki fira munafukin"ta fuzgo hannunta husnah naso taji meyakeson fada mata tana jin tausayinsa sosai suka fito nusrah tasa tv zatayi kallo ummah hadiza ta sauya tashar zuwa ta karatun alkurani suna nan zaune gaba daya husnah hankalinta ya rabu biyu ta rasa meke mata dadi dan zaman da sukeyi da yaseer a dakin momy tana masa shagwaba yana biye mata ta fara sabawa dashi ko ina yaje oho,take wata zucuyat tace Yana tare da matarsa kin manta ku biyu ne?"wani abu ne yazo mata wuya ya tsaya mata,
"ummah akwai komi a gidan nan ko?me zaa dafa ne?"Ummah ta jinjinawa nusrah kai tace"komi akwai dik abinda kikeso ki Shiga ki dafa mana ni yanzun inata jiran wanan ja'irin yaron ne....
******
momy ta fito da hijabinta ta nufi sashen daddy inda take jiyo muryarsu ta shiga da sallamarta ta zauna yadan kalleta sau daya ya kauda kai hajiya rabi ta watsa mata wata uwar harara "yadai kika shigo me kikazoyi"daddy yace yadda yayi maganar kamar ya sauko momy ta karanto adduoi kafin tace "nazo yi maka sannu da zuwa ne dama naji shigowarka"tabe baki hajiya rabi tayi ta turo dankwalinta gaba tana kad'a kafa suka hada ido batare da daddy ya ganiba tace"yau din nan zaki gaba yau zakibar gidan nan"tayi mata nuni da hannu tana dariya hade da harara dariya taba momy murmushi kawai tayi mata,daddy nacin abinci yadan saci kallon momy suka hada ido wani kallo tayi masa irin kallon da take masa ya gigitasa gani tayi ya ajiye cokalin ya juyo gareta mamaki ne ya cika hajiya rabi ta kalli kular abincin data zuba masa magani ya cinye tasss befi cokali daya ba boka ya sanar matada cewar dayaci bazai gamaciba batareda ya saki momy ba amma gani tayi kamar yanaso ya sakewa momy ta gyara zama cike da kissa ta kalli momy tace "masu ciki kenan nikam zainab yaushene watan haihuwanki?"wani kallo momy tayi mata ta dauke kai daddy yace "badake take magana ba ki amsa mana zainab banason bakin hali kibar ganin na sake dake harna barki kim zauna mun a daki"momy tace "nima bansaniba dan bana zuwa asibiti"daddy ya kalleta ya kalli cikin kyau sosai cikin yayi mata gata nan da kurucuyarta kamar ko yaushe bata canjawa yarasa dalilin dayasa inhar zai ganta zai rinka ganinta tamkar bakin kumurci ko bakar karya sam bayason hada ido da ita zucuyarsa nayi masa zafi ,amma yau yana kallom cikinta tabashi tausayi,ta mike tana daga kafa dakyar tace "saida safe"ya dan bita da kallo hajiya rabi ta kafesa da ido,
momy tsaye tayi a jikin kofar dakin daddy wasu hawayen farin ciki suka zubo mata yau Alhaji badamasine ya kulata?tana kallon yadda yake satar kallonta lallai tayi bacci tayi sake irin saken datayi aljani ya saace mata ya gashi dataje canja abincin bayan ta zuba ta tofa addua cikin abincin yaci gashi har ya kulata?ta girgiza kai tsakaninta da rabi Allah ya isa....
******
muneeba na kwance kirjin yaseer tana shafa gashin kirjinsa dake kwance luff bacci sosai yakeyo dik yadda taso ta juyashi tasamu kansa ya kusanceta ya kasa sakamakon bashida karfi kara rungumota yayi cikin bacci da magagi yace "husnah....husnah ya jikin naki?yadai?"yace kamar bugagge tsaki muneeba tayi yana bacci yana kiran sunan husnah saboda tsabar jaraba?husnah da momy bokansu na aiki amma zatayi maganinsu yau zataga yadda zaayi ya kwana dakin amarya,wata harara tayi masa kamar yana ganinta ta turesa ta zame jikinta Daga nasa,
bugun kofa taji da sauri ta zuro kafarta kasa ta kalli agogo karfe goma na dare to waye zai buga mata kofa yanzun?ummah?ta tambayi kanta badai ummah ba tasan tanacan makale da daddy ta muskuta wani nauyi kafafuwanta keyi bugun da akayi na biyu ne yasa yaserr mikewa furgigit kamar a mafarki yaji bugun yana fadin "husnah ina rigata?"muneeba tayi tsaki cikin kasa da murya tasan ya dauka a dakin husnah yake tace "ka kwanta bari naje na duba waye ke buga kofar"girgiza kai yayi "ah ah bazaki fitaba darene karkije aljanin nan ya daukemun ke ya zuro kafarsa yana lalube cikin saa yaji rigarsa a gefe ya zura cikin duhu yake kallonta mamakin ganinta da katon ciki yakeyi idonsa har rufewa yakeyi tsabar bacci bugu na uku ne yasa yayi saurin kunna fitila muneeba ya gani yana bim dakin da kallo "muneeba?a dakin nan nake dama?"tambayarta yakeyi cikin wata irin murya yace "magana nake miki"sosa keyarta tayi cikin murya mai ban tausayi a sanyaye tace "bacci ne fa ya daukeka shine nakyaleka ganin ka gaji"tsawa ya daka mata "karya kikeyi "cikin sauri ya fice ya nufi bugun kofar yana budewa yaga ummah hadiza tsaye tace "au Yaseer dama dakin matarka kazo ka kwanta?dik kiran da ake maka bakajiba kenan?"ta kalli muneeba dake bayansa ta zumburo baro ummah hadiza ta jinjina kai tace "ehh lallai to Alhamdulillah tunda kana nan Bari intafi na lallashi husnah data shiga damuwa take kuka akanka"cikin wani irin yanayi jikinsa na sassarfa yace "ummah wallahi bacci ne ya daukeni shine bugun kofarki ne ma ya tasheni kila da sai safiya tukunna zanga anan na kwana Dan Allah kiyi hakuri"yasa kai ya fito ummah hadiza tayi gaba tana jinjina kai tqbbas tasan shiri ne tini hakan yasa tazo ta wargaza shirin tasani yana nan ta tabbatar da hakan tun ganin da tayi musu da sadiya da kiran da akai masa tasan shiri ne tabbas zata zaunar da husnah akan kishiyarta dole tana tafe yaseer na biye da ita ana yayyafi sama sama,
muneeba wani ihu tayi cikin dakin tsananin bakin ciki ko gani batayi tayi jifa da kofin dake centre table cikin wani yanayi ta barke da kuka tana fadin "wallahi karyane baki isaba yaseer nawa ne ni kadai yaseer be isa ya kusanci wata maceba saini"ta kwanta a doguwar kujera tana kuka harda bubbuga kafa.....