← Book details Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 68

Sashe 40

Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zumbur momy ta mike daga kan gadonta tana bin dakin da kallo ta dafe kirjinta jin karar bude dakinsu yusrah taji tasa hannu ta kunna wutar dakinta yusra da nusrah ne suka shigo aguje dakin "momy momy meke faruwa wata k'ara mukaji cikin gidan nan kodai Anty husnah ce?"momy tace "zai iya yuwuwa amma ba muryarta najiba kamar muryar yaseer Allah dai yasa wad'anan aljanun ba zuwa sukayi ba suka cutar da yaseer shiyasa da yacemun zai tafi gida shi kadai ban amince ba"momy ta kalli agogo biyu da minti goma sha biyar na dare,ta zuro kafarta tasa hijab ta fito cikin tsoro bakinta dauke da addua ta karasa jikin kofar dakin sautin nishim kukan husnah taji,
yaseer na kwance yashe a gefe yana sauke numfashi gumi ke karyo masa ta ko ina yaji sautin bugun kofa da sauri ya mike ya zauna yana kallom yadda husnah ke cije baki lokaci daya tausayinta ya kamasa yadda take gumi yace cikin sarkewar murya "wannene "momy daga waje tace "nice yaseer lafiya dai ko naji kamar ihu kuma ga kukan husnah inaji"gaban yaseer ya yanke ya fadi karar da yayi har dakin momy gumi ya karyo masa ya dafe kai ya kalli husnah da Sabom kuka ke taso mata yace "am momy bakomi fa husnah bacci ma takeyi nima yanzun bugun kofarki ya tasheni"momy najin yadda yayi magana tayi ajiyar zuciya tace "zo ka budemun dai insan menene ke faruwa kodai karya kakemum"yaseer ya karasa gefen husnah yayi saurin kwantar da ita yaja bargo ya rufeta cikin kasa da murya yace "husnah ki rufe idonki ki kwanta dan Allah kar momy tasan meyafaru"wani haushinsa taji ya darsu a zucuyarta wato yasan abinda yayi meyasa ta yarda dashi? rufe ido tayi take ta tuna lokacin da suke cikin bahom wanka itada Abraham lokacim da yake gwada mata tsananin soyayya yadda idanuwansa suka kankance da shaawarta tsananin kaunar da yake mata yasa ya hakura da bukatarsa da taji ciwo amma tanaji tana gani yaya yaseer ya shigeta ya ji mata ciwo....ta toshe bakinta kuka na kokarin kwace mata ya budewa momy ta shigo dakin ta kunna wuta gefe taga husnah kwance ta lullube da bargo ajiyar zuciya ta sauke "alhamdulillah babu dai wata matsala ko?"ta kalli yaseer da yayi zuru zuru babu alamar bacci a tare dashi momy tayi tsuru tana kallon yaseer ganin haka yasa yad'an tsargu ya kauda kai momy tayi tozaali da rigar nusrah ta bacci a kasa momy ta tsugunna tace"kaga nusrah wato rigarma a kasa ta saketa mtswww Allah ya shirya yaran nan"ta dauka tace "saida safe"ta juya zucuyarta cunkushe da tunani kodai wani abu ya faru ne yaseer ke boye mata?amma bataga alamar komi ba,ajiyar zuciya ya sauke ya kashe wutar dakin ya cire rigarsa ya karasa yana kokarin shiga cikin bargon ya janyota ta mike ta zauna tace "bana bukatarka a yanzun yaya yaseer ka duba kaga yadda kajimun ciwo"tace cikin kuka zucuyar yaseer ta karaya yacev"shekara da shekaru ina jiran wanan ranan husnah,nima banso hakan ta kasance yanzun ba naso sai kin tare a gidana husnah amma na kasa controlling kaina saboda kaunar da nakeyi miki"ta share hawayenta tana kokarin sakkowa daga gadon ya riketa jikinta yayi mugun zafi ta ture hannunsa ta zuro kafarta kasa tsayuwa tayi jim radadi mai tsananin a kasanta ta fashe da kuka ta Durkushe a kasa ya sauko cikin sigar lallashi yake bubbuga bayanta taki saurarensa sai kuka da takeyi a haka bacci yadan dauketa ya sungumeta ya maidata gado ya rungumeta jikinsa yana jim sautin ajiyar zuciyarta rufe idonsa yayi yana tunano irin dadin da yaji besan lokacin da yaji abu na zuba a bananarsa ba haka yake rungume da ita har asuba....

sautin kukan Abraham ya karad'e cikin dajin cikin tsananin azaba yake mai rad'adi ga zucuyarsa dake tafarfasa yau husnah tayi masa laifin da bazai taba kyaleta ba harabada husnah ta yarda yaseer ya kusancetw?wasu hawaye yakeyi bakin kurin na zubowa daga idanuwansa ya bude hannuwansa yayi wani huci hayaki ya fito daga bakinsa husnah ta hanasa kusantarta amma ta amince da bil'adama ya shiga jikinta yau husnah ta karya masa alkawarin data daukar masa yayi ihu zuhraliyya ce ta fito wajen hucin azabar karafinan da yake daure yasa tayi baya ta zube a kasa tana kuka Abraham cikin rad'adi yake fad'in zuhraliyya ki kwanceni daga nan wajen ina cikin matsanancin hali nasan ke kanwata ce maijin tausayina sanan inajin tsananin kishin ruwa"zuhraliyya hawaye ya zubo mata ta daga hannuwanta saiga wata kwarya ta bayyana tana kallon kwaryar saiga ruwa tana kokarin mika masa taji an daka mata tsawa ta bayanta mahaifinsu ne taja da baya ta sunkuyar da kanta kasa juraid da junaid kannen Abraham ne suka bayyana a wajen mahaifin Abraham ya shiga zagaye a wajen cikin wata irin murya Baba yace "Abraham"ya kira sunansa be amsa ba saboda tsananin fushi da tashin hankali da yake ciki zuhraliyya ta zube a gaban mahaifinsu "ina neman agajinka baba da ka kwance yaya Abraham ka duba halin da yake ciki sanan kayi masa uzuri da soyayya"gyaran murya baba yayi yana kallon wasu hawaye dake fita a idon Abraham yace "zan kwanceka amma ba yanzun ba Abraham sai zuwa wani lokaci sai kuma kayimun alkawari akan wanan bil'adamar"Abraham bece komiba hannuwansa sun kage a bankare yake ya kauda kansa gefe bayaso yayi magana saboda zugi da rad'adin dake cikin zuciyarsa a dankare"mahaifin Abraham dariya yayi ya bace ganin yadda Abraham yayi zuhraliyya ta mike tace"yaya ka kwantar da hankalinka zan daukar maka fansa akan cin amanar da husnah tayi maka "ta jinjina kai yayi ihu yayi gunji zuhraliyya tayi wani girgiza ta kara tsawo sosai ta dauki kwaryar ruwa tana shayar da Abraham yasha sanan ta koma daidai yadda take ta bace,

******
momy na parlor yaseer ya fito Baya cikin kwanciyar hankali daka kallesa zaka hango damuwa a tare dashi momy tace "ah ah ya naganka kai kadai?"

"ina kwana momy"ya gausheta a sanyaye,

"lafiya lau ina husnah?"damm gabansa ya fad'i tunawa da Artabun da yayi da ita taki koda tashi tayi wanka yacev"bacci takeyi bata tashi ba"momy ta jinjina kai "Masha Allah lafiya tasamu"yaseer yayi murmushin karfin hali yana kokarin zama momy tace "ai tafiya zakayi gidan ku dan yanzun mukai waya da hajiya zainab muneeba bata da lafiya kwana akayi akanta sanan daddynku na fushi dakai ka kwana a nan"damm gabansa ya fad'i meyasamu muneeba?tambayar da yayiwa kansa kenan kansa ya dau carji hankalinsa ya tashi d'ansa dake cikinta kawai yake tunani sam ya mance da ita ga husnah cikin wanan halin yanzun ya zaiyi? momy tace "kayi shiru naganka a burkice ko kana tsoron kaje matarka ta yankaka ka kwana a nan wajen husnah ne?"ya girhiza kai ya sauke ajiyar zucuya yana laluba aljihunsa yace"Bari in dauki makullina nabarosa daki intafi gidan"momy ta jinjina masa kai ta dauki wayarta ta shiga danne danne,

tura kofar yayi be ganta ba kukanta yakeji a toilet ya tsaya daga jikin toilet din cikin murya kasa kasa yace "husnah husnah meyasa kike kuka?kiyi shiru zanje gida indawo kinji zanzo mu fita anjima da yamma ko?"shiru tayi batare da ta amsa masa ba jin haka yasa ya kira sunanta a hankali ta amsa "naam"yace "muneeba batada lafiya ne shiyasa zan tafi banso intafi inbarki haka ba"idanuwanta jajir ta jinnina kai wato ma wajen matarsa zaije ya gama da ita ya keta mata haddi zai tafi ta rufe idonta kawai tanajin radadi jin shiru ya juya yadau makullinsa ya fice,

a hankali take watsa ruwa zucuyarta cunkushe da tunani ga zafi tanaji a kasanta haka ta fito daga wankan tana d'ingisa kafa yusrah ta turo kofar dakin ta shigo da sallama "Assalamu alaikum"husnah bata kalleta ba tana dingisa kafa tana tafiya a hankali yusrah sakin baki tayi tana kallonta juyowan da husnah zatayi taga fuskar yusrah ta koma mata ta zuhraliyya sakkk.... zuhraliyya na tsaye a gefe,

husnah wani kallo takewa yusrah itako yusrah tsoro taji tace "lafiya Anty husnah kike kallona haka?yusrah ce fa?"fuskar yusrah ta rikide ta koma tata bayan tayi magana husnah tayi zuru to ya dazun taga fuskar zhuraliyya a tare da yusrah? ajiyar zucuya ta sauke "yusrah"tace a sanyaye tana kokarin zama yusrah tace "meyasameki Anty husnah?ko kafar taki ke ciwo har yanzun?"da sauri husnah ta jinjina kai yusrah tace "momy tace ki fito kiyi breakfast kisha maganinki"ta jinjina kai idon yusrah ya sauka akan zanin gadon da yayi kaca kaca da jini cikin sauri ta jita har tanacin tuntube, husnah ta dingisa kafa ta karasa jikin madubi idonta ya sauka akan wadda kw gefenta da sauri ta waiga Baya bataga kowa ba ta kara kallon madubin tayi tozali da fuskar zhuraliyya dik dige dige jiki ta harde hannuwanta bakinta na rawa tace "zhuraliyya"a hankali ta waigo bata ganta ba kyalkyalewa da dariya zhuraliyya tayi cikin dakin sautin dariya taji bata ga kowa ba cikin sauri ta bude wardrobe ta ciro wasu kaya ta zura idanuwantq zuru zuru tana kokarin fita bata ga tahowarta ba gani tayi Tasha gabanta taja da baya da sauri tace cikin tashin hankaki "meye hakan?neyasa kikazo ki tsoratani?shi Abraham din ne ya turo ki"cikin tsawa take maganar dikda yadda zuciyarta ke tsananin bugawa shiru babu kowa kawai ta bude kofar ta fito tana dingisa kafa tin daga nesa momy ke kallon yanayin tafiyarta tana isowa taga kujerun dining dim babu waje ta tsaya momy cikin faduwar gaba take kallom husnah tace "zauna mana husnah?"nusrah ta saci kallon husnah ta kauda kai momy ta nuna mata kujera ta zauna husnah mutum tagani zaune a kujerar tace "momy akwai mutum"a sanyaye momy ta kalli kujerar ba kowa tace "ba kowa"husnah ta had'iyi miyau idonta ya cicciko ita tana ganin mutum zhuraliyya na juyowa ta razana husnah ta kwalla kara ta fadi sumammiya....
Chapter 40 · 0% Book details